
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar alhamis suna cikin hutun makarantar boko na ranar yara(Children’s day)kuma yau ba makarantar allo ba Islamiyya kowa yana abinda yake so ne, dan duk sun gama ayyukan gida.Tana kwance ranta ba dad’i tunda Julaibib yatafi sau uku kawai sukayi waya yauma takira shi sama-sama suka gaisa yakatse,tasake kira yad’aga da sallama”Yaya Julaibib na maka laifine? A ah baki min kome ba.To me yasa kike min wani iri? Yad’anyi murmushi”Sudaida kenan ni ban miki wani iri ba fa zan shiga aji ya katse wayar…Tayi lamooo a gadan,tunani barkatai ya cika k’wak’walwarta ta rasa na za6a tayi.
Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu kamar yadda suka sa ba,suka kalleta suka kwashe da dariya”Sudaida uwar tafakkuri (tunani)me kuma yafaru?Khausar ta ta6e baki tabud’e wadrobe ta d’auki kayan da zata goge a d’akin-shak’atawa tafita…Bata basu amsar tambayar su ba,takalli Zainab”ya maganar bikin saukar mu?Ta zauna a gefan gadan”ai Malam yayi tafiya sai ranar asabar zai dawo.a’isha tamik’e “barinje muk’arasa kallan mu dan yau bazan dad’e ba,angona Hashim anjima yana hanya.Nasmat tad’an daki kafad’arta”to gaggawa hannu hagu a romo mutumin da ko tasowa bai yiba.suka mik’e ita da Zainab.Nasmat tabi da Sudaida da kallo “dan ALLAH me yake damun kine?Tamaida kanta saman matashi”na fad’a miki ba abinda yake damuna to ki rabu dani mana.Sudaida na damu dake shi yasa nadamu da halin dakike ciki. Tamaida idanun ta tarufe…Nasmat ki kyaleni bana san hayaniya fa.Tamik’e ALLAH yabaki hak’uri, amma ina zargin wani abu koda yake…sai tad’an motsa kafad’a shikenan can da yawarki yarinya.
Sai da aka cinye zangon karatu d’aya sannan Julaibib yazo gida.Yau alhamis ranar da ake bikin saukar Alqur’ani me girma nasu Sudaida,kome an shirya shi cikin mutunci, bangaran maza daban na mata daban Liman yabud’e taran da addu’a yama daliban addu’a Allah yasa suyi amfani da abinda aka koya musu a kowani irin hali da yanayi suka shiga na rayuwa…aka biyama d’aliban allunan su sannan aka cigaba da wa’azi da fad’akarwa akan neman ilmi dan shine yake sanya rayuwa tayi kyau tayi albarka.
Bayan angama kome sannan aka shiga yin hotuna da rabama d’alibai kyaututtuka aka rufe taro da addu’a,Sudaida tasunkwui da kai abinda yaba mak’alallun k’wallan cikin idanun ta damar zubowa k’asa sharrr… Wannan taran me tarin albarka mutane da yawa sun halacceshi amma banda Sinan,to me ya hanashi zuwa tunda ya sani?Tayi kwafa wallahi za mu had’u ne.
Tana d’ago kai,caraf idanun su yahad’u, wani sanyi dad’i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar ta. Alk’asim yak’araso wajan “gaskiya yan matan nan kun had’u,zai mik’a ma Sudaida rufaffen envelop a’isha takai hannu za ta kar6e,yajanye hannunshi da sauri”a ah ya haka? Tagyad’a kai”eh haka nake nufi,kai kaga hakan zata sa6u bindiga acikin ruwa? Wasa tare ci bamban?Khausar tace ko muma abamu ko itama tarasa. Yayi yar dariya “mata problem kunga fa ba wani abu bane a ciki,rubutune kawai akayi da biro bulu.Eh koma dai menene to abamu na mu. Nasmat ta katseshi”to wai ma yahaka?Ana zatan wuta a mak’era sai ga ta kuma a masak’a?Wallahi wanda nayi hasashen zai bata kyautar kaasatan bai yiba sai kai?Yamaida envelop d’in aljihu “shikenan karku samu damuwa za kuji a salansa, Sudaida sun hana in baki hannu da hannu zan aiko miki dashi gida,yajuya yayi tafiyarshi bai saurari hayagagar da suke mishi ba.Suka jera suna tafiya zuwa gidan Hajiya”Aisha tace wai me yahana Sinan zuwa wajan saukar mu,naga har Hashim daba d’an gari ba ya zo?Tawatsa hannu”nima ban sani ba amma ina ga kamar ba k’alau ba.
Dayammacin ranar sai ga shi da kaya nik’i-nik’i lemukan gwangawani dana kwali, yana zaune a dakalin k’ofar gidan tafito cikin fushi Sagir na biye da ita da kayan,takar6a ta ajiye mishi “Sinan ba wad’annan nafi buk’ata ba,zuwanka wajan ya fi duk abinda za ka bani. Tajuya…Yasha gabanta da sauri yahad’a tafukan hannayen shi da sigar rarrashi”Sarauniyar Sinan kiyi hak’uri “Tagirgiza kai”ban hak’ura ba sai ka fad’a min abinda yahana ka zuwa.Yad’anyi jimmm… Na wucewar wasu dak’ik’u”za ki yadda dani?Tayi shiru sai yacigaba”to ni dai na san na miki laifin da ban ta6a miki irin shi ba,Sudaida baccine yayi awan gaba dani,to ya zanyi?To wayar ka amfanin me takeyi na kira ka sau shurin masak’i baka d’aga ba,sai kace me baccin mutuwa? Yakad’a kai cikin damuwa”lallai na cancanci abani horo,itama fa wayar a yanayin shiru nasa ta,kiyi hak’uri Sudaida “ALLAH yana san masu hak’uri,masu had’iye fushi, suna da dama su rama abinda aka musu amma sai suke hak’ura su yafe,su maida kome ba kome ba saboda ganin girman ALLAH…yacika da dad’ad’an kalamai har sai da yashawo kanta. ALLAH da gaske ke nake so Sudaida alk’awari ba karyawa ni da ke sai mun zama abin kwatance mutu ka raba takalmin kaza. Da haka yaba Sagir kayan yamayar dasu cikin gida..
Kwana biyu da fara azumin watan ramadan yashirya shi da Musaddiq sai Matsirga. Inna tana zaune a d’aki taga ana shigo da kayayyaki tasa hijab tafito tsakar gida tana tambayarsu daga ina wad’annnan kayan? Sai ga Bello yashigo da murnar shi yana fad’a mata su Yaya Julaibib ne.Jikinta yayi sanyi tabi kayayyakin da kallo cikin zancen zuci”wato k’auna ta gaskiya tana d’orewa koda ba wanda ake k’aunar a doron duniya. Bello yarik’o hannunta “Inna na shigo dasu. Tayi murmushi”lale maraba,sannunku da zuwa bismillah tajuya zuwa cikin d’aki suka bita,cikin girmamawa suka gaisheta”Iyayan na ku k’alau ko? A lafiya k’alau Inna suna gaishe ku.To madalla ALLAH yamuku albarka,ku bakwa gajiya da hadima?Musaddiq yace”haba Inna ai bakome… Yiwa kaine.To Ubangiji yasa ka muku da mafificin sakamakon shi;ALLAH yasa hakan amizaninku na kyawawan aiyuka. Amin,amin Inna.
Inna su Malam basa nan ne?Eh d’azu shi da Maude suka tafi Zango wajan k’annin mahaifanshi,Tukur kuma jiya yakoma makaranta. Suka d’an ta6a hira sannan suka mata sallama taciko musu jarkoki da kindirmo da manshanu, Bello yasa kuka shi dole sai sun tafi dashi Inna tayi-tayi ya zauna amma ya kafe ya nata ihu shi dai zai bi su,duk yamak’alk’ale Julaibib ya 6ata mishi farar shaddar da yasa da majina da ruwan hawaye,yarik’o hannun shi.
Inna bari muje waje muyi magana tabisu da kallo,a mota suka dinga rarrashin shi “kaga idan muka tafi dakai Malam bai sani ba idan ya dawo zaima Inna fad’a muma zai mana fad’a, yamak’ale kafad’a”uh uh ai idan tace kaine bazai yi fad’an ba,kuma kana da waya kafad’a mishi na san zai yadda,ni dai kawai ALLAH mutafi”to naji na kuma maka alk’awari idan aka samu hutu Insha-ALLAH zan zo in tafi dakai Zonkwa.Yad’ibo dabinon ajwa da yawa a aljihunshi idan ka yadda sai in bar maka wannan dabinon,yakalleshi sannan yakalli dabinon” to duka zaka barmin?Yayi murmushi”eh mana sa hannunka ka kwashe ma, yana ta d’auka da d’ai-d’ai da d’ai-d’ai yana sawa a aljihunshi har ya kwashe duka sannan yayi dariya aina kwashe, to sai ka zo d’in barinje in nuna ma Inna,yauwa Bello mutumin kirki barin rakaka,har ciki ya kaishi ya kuma fad’a mata yadda sukayi tayi murmushi kawai sannan suka sake yin sallama sunama juna asha ruwa lafiya.
Rana ta tafi zata fad’i magriba na shirin kunno kai,an kusa shan ruwa takashe rediyon da take sauraran tafsirin Alqur’ani me girma a gidan rediyon jahar Kaduna(FRCN)farin gida kafin Sardauna.Tayi doguwar hamma tasa tafin hannun dama tarufe bakin ta, tana Isti’aza yau ba laifi tana jin azumin nan ajika dan ma yau Khausar ce da aiki da wallahi bata san yadda za tayi ba kanta har barazanar ciwo yake yi,daga can d’akin-girki tajiyo kiran Umma tamik’e da sauri tafita.