GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Umma gani.Umma tamata wani kallo “ba tun d’azu nace ki d’auki dabgen Hajiya ki kai mata ba?Baki ji bane ko zuwan ne baza kiyi ba? Tad’an sosa kai Umma fa boss ce,bata d’aukar raini ko na sisin kwabo”Yi hak’uri Umma barin d’auko hijab,tasa hijab ta d’auki kwanan samiran sannan tad’an kalketa cikin shakka”Umma dan ALLAH daga nan zan biya gidan Inna.Tayi shiru kamar bata jiba sai da tagama zuba wani dabgen a wani samiran ta rufe sannan takalleta”adawo lafiya suma ki tafi musu da wannan.Wani murmushi yasu6uce mata dan ba k’aramin aikin Umma bane tahana”nagode Umma tarik’o hannun Hanifa’yar Musaddiq ta fari suka tafi.

Tana shiga sai ga Nasmat itama takawo ma Inna hadaddan kunun aya kafin a kira sallar magriba sunyi alwala,ana kiran sallah sukaci dabino da lemun 6awo da ruwa me rangwamen sanyi sannan suka tada kabbarar sallah.

Julaibib da Baba suka shigo da sallama sukama juna barka da shan ruwa sannan ya ajiye ledan hannunshi a gaban Inna.Nasmat tajawo ledan gabanta tafara shan abarban da yake ciki da kankana yankakku tana fadin”kyan rawa da makar6i.Sudaida ma tasa hannu ta d’auki kankana tana cema Hanifa sa hannu ki d’auka…Baba yayi murmushi ganin irin kallan da yake musu,yayi k’wafa yajuya zuwa d’akin shi Inna tana mishi dariya itama.Sudaida ta ka sa cigaba da sha, ranta ba dad’i har yanzu bai dawo yadda tasan shiba, ba wani kyan gani da yayi,yabar k’asumba ba wani gyara,kana mishi magana zai bika da wannan rikitaccen kallan,ya ya6a maka bak’ar maganar da ko barinje (mahauci) iya karta kenan.

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba yana nazarin wani littafin tafsirin Alqur’ani me girma Hajiya tashigo da sallama,yamik’e da sauri yataro ta”maraba da zuwa Hajiyar mu,ta ture shi”kai tafi can matsa kabani waje,ta zauna a kujera tana murza k’afafunta,ya d’auko man zafi zai shafa mata tajanye k’afafunta da sauri”bana so.Yayi murmushi”haba Hajjaju makkatu wal madinatu gwiwata a k’asa,kaina bisa wuyana.Oho ashe kaima ka san kayi laifi,saboda ALLAH Julaibibi tunda kazo garin nan sau d’aya rakkin rak kazo gidana,ba fad’a to me yakawo wannan gabar? Kiyi hak’uri Hajiya bana jin dad’i ne.Tajijjiga kai tana mishi kallan nazari”kai Julaibibi tunanin Bilkisun ce yake susuta ka haka?Yagirgiza kai “haba dai Hajiya ba wannan bane.

Yamik’e da sauri ya d’auko madara da maltina da kofi.Hajiya tabishi da kallo cikin mad’aukakin mamaki”ciwon har yakai ba ka iya yin azumi ne Julaibibi?Yadafe kai “Innalillahi.Ina yi, wai dama ke zan kawo ma na man tane.Tamik’e wa?Ni kaga tafiya ta.Yarufo gidan”barin taka miki suna tafiya suna hira”anjima da daddare zan zo miki hira sai ki tanadar min garwashi zan zo da d’anyan masara in gasa mana”To ALLAH ya kaimu har gidan Kawun shi yakaita.

A d’akin-shak’atawa Sudaida ce kawai tana kwance a doguwar kujera tana waya,tamik’e zaune saboda shigowar su,kusan dak’ik’u goma sannan tagama wayar,tad’ago tana kallan Julaibib bayan ta d’ora ha6arta a kafad’ar Hajiya”Hajiyarmu you’re welcome.Kin san abinda bature me jan kunne yake nufi da haka?Tajijjaga kai”tun kafin in haifi uban ki ya haifeki kuwa.Tad’an turo baki, Julaibib yayi murmushi yana shafa k’wantaccen bak’in gashin kanshi”Yo kya 6ata fuska ba tambaya kikayi nabaki amsa ba?

Mu turancin mu ma gangariya masu abu da abun su kura da kallabin kitse, turanwan ne fa suka koya mana baki da baki,To me yasa bakya yi?Tad’an kalleta kaji wata magana to yaran turanci yarena ne?Ni yarene hausa idan takama ayi turan cin inayi mana”do you get me? Sudaida takyalkyale da dariya saboda yadda Hajiya tayi furucin tagyad’a kai”yes grandam.Su Mama suka shigo suna gaishe da surukar ta su cikin girma da mutuntawa.

Da daddare yana gidan Hajiya suna hirarsu takalleshi”tunda katafi Azare kayi zaman ka shiru ba amo ba labari ko wata bafulatanarce takuma rik’e mana kai?Ya jujjjuya masarar sannan yad’ago yakalleta”ko d’aya Hajiya.To in dai haka ne ya kamata ka nemi wata,ga yan mata nan burjik a cikin dangi sai ka za6a ka darje,kana gani ganin idanun ka Musaddiq Ya’yan shi biyu ga cikin na uku nan.Cikin wasa yace”Hajiya banga wacce nake so ba ko za ki tayani nema?Tagyada kai”anyi an gama maye ya auri makauniya.Bai wani dad’e ba yamata sai da safe, saboda akwai tashi cikin dare domin yin munajaati ga ALLAH buwayi gagara koyo ga kuma tashi yin sahur.

K’arfe-k’arfene sai dai a cikin k’arafan akwai zinare da azurfa.

Idan baka san gari ba…saurari daka.

Abdullahi Lawal Abdullahi (d’ansarai)
Saudat Ibrahim Yahya (Takwara ta)
Mungode da tunatarwan ku bisa wani kuskure da mukayi a shafi na goma sha biyar..

Falmata Maiduguri mungode da kulawa.

28 Jumaada Awwal 1441
23 January 2020

We Ibrahim’s Daughters ????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASAOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’iba)

Shafi nagoma sha bakwai.

Bayan sallar asham Julaibib yawuce gidan Hajiya anan yatarar dawasu daga cikin jikokinta maza anata hira da ciye-ciye.Yajawo kaskon data cika da garwashi gaban shi, Musadduq yaja tsaki”Lillahi warasulihi yauma karasa abinda za ka kawo mana sai bushashshen masara?Kai ALLAH yasauwake.Ya amsa da amin “dan ka kawo mata bushasshen nama wai shi kilishi ba shi zai hanata cin gashashshiyar masara ba.Musaddiq yagirgiza kai”kai Malam ai yanzu ba lokacin cin kilishi bane,watan ramadan muke gasassun yan shila nakawo mata me ruwa-ruwa da yajin tafarnuwa ya ji kayan lambu.Yaturama Julaibib k’unshin duba kagani.Yayi kamar ba dashi yake magana ba yafara gasa masararshi yana tambayar Hajiya ta saurari tafsir na karfe uku da yammacin yau?

Kwanci tashi har anyi azumi takwas, agida tasame shi yana shirin komawa Azare “tazauna tana kallan shi”Yaya d’an Sarai tafiya ba sallama?Yacigaba da shirya kayan shi a jaka ba tare daya d’ago ya kalle taba”ai naje gidan akace kin tafi Hayin-Dogo”haka ne to yaushe za ka dawo? Yarufe jakar yad’auki agogo yana d’aurawa a hannun damar shi”sai ALLAH ya kaimu sallah idan muna raye,ta taya shi kwashe kaya zuwa mota yayi sallama da Inna suka fito,tajingina da motar tana kallan shi cikin kissima wani abu a zuci yana zuba ruwa a lagireto har yagama yashiga mota yazauna yana d’aura belt.

Yad’anyi murmushi”duk kinyi wata iri ko za ki bini ne?Ta turo baki gaba”da inada wannan damar ai da ba haka ba wallahi.Baiyi magana ba,yabata wasu kud’i”bayawa.Tasa hannu biyu takar6a”nagode Yaya d’ansarai ALLAH yak’ara bud’i,suka d’aga hannu suna ma juna adabo.

Sun dawo makaranta suka tarar da Asma’u kanwar Sudaida ta ci kuka ta gode ALLAH idanun ta sun kumbura sun kad’a jawur”lafiya Asma’u? A tare suka tambaye ta,sai tasake jin wani sabon kukan ya kufce mata tafi minti goma sannan tafara rage sauti tana ta jera ajiyar zuciya”ke wai kukan me kike yi ana tambayar ki kin ma mutane shiru wacece sa’ar ki anan? Khausar ta tambaye ta.Taja majina tana hura iskar bakin ta”labarin zuciya a tamabayi fuska ranta in yayi dubu ya 6aci,cikin hawaye tafara magana”wai arasa wanda za a bani a matsayin mijin aure sai Yaya d’ansarai…wasu hawaye masu d’umi suka sake zubowa sharrr…sharrr…Sudaida tamik’e zaune da sauri kamar za ta hantsila,duk suka bita da kallo ganin yadda tayi sai kuma ta koma ta kwanta batayi magana ba dan ta ma rasa abinda za ta fad’a wallahi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button