GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Julaibib yashigo da sallama,yana sanye da babbar riga,’yar ciki da wando na farin voil,takalminshi sau ciki da hular dara bak’a, k’amshin arabi’an perfume d’inshi ya cika tsakar gidan kamar lokacin yake fesawa, gyaran fuskar dayayi sai yak’ara mishi kyau”har ka cire kwalliyar sallar?Ba dole ba autan Inna,zanyi aikin fid’a da farar shadda ne?Zai shiga d’akin Hajiya yace “ka daiyi sauri kagama dan ga na Inna can yana jiranka.Tabi bayan shi zuwa d’akin.

“Happy Eid-eel Fitr sarauniyar Sinan.

D’an gajeran sak’on Sinan daya shigo wayar ta kenan,tayi murmushi.Tazauna tana kiran a’isha dan Kafanchan ta tafi wajan Kaka acan tayi sallah. Tad’aga da sallama,Sudaida ta amsa sannan tad’ora”zakara ya ja kaza kinyi sallah lafiya?Ta amsa”a ah mantawa kikayi takalmi ne yaja k’afa.Sudaida taja tsaki “ai wallahi sa a ma kika ci dana kira ki,keda za kiyi zaman ki shi Hashim d’in yazo nan yayi sallar wai sai kawai kika wani bishi…a’isha ta tari numfashi” ke dakata haka malama karki d’oramin jakar tsaba kisa kaji sudinga bina,wannan sallar nafara zuwa Kafanchan?Ni ba wajen shi naje ba wajan Kaka naje.Tasake jan tsaki”ba cinya ba k’afar baya. Itama ta amsa”a ah ALLAH yasa k’afar kafad’a ce, ke kika sani,ba Khausar wayar.Yaya Khausar gida tawuce ni ina gidan Hajiya.Tam barin kirata sukayi sallama. Asama taji Hajiya tana fadin”to na samo maka matar aure.Matar aure wace iri kamar yaya? Yatambayeta cikin rashin fahimta.Takalleshi”au ka manta yadda mukayi dakai cikin azumi?Ba ka ce in samo maka bane?Yakama kai”Innalillahi,Hajiya ni fa wasa nake miki.Tawatsa hannaye “kai kajiyo, amma dai aikin gama ya gama duk dai ban fad’a ma kowa ba sai yarinyar,to amma tunda kaima na fad’a maka to zan fad’a ma Iyayan na ku kowa yaji yakuma sani.Wacece ita?Tagirgiza kai”uh uh ba yanzuba ina so ne tad’an kara girma da hankali lokacin an kawar da Yayyinta.

Shi da Sudaida suka kai juna.Yakauda kai cikin rashin sanin abun fad’a,yasauke numfashi,d’an madaidaicin kofin hannun shi ya ajiye a saman tebur.”akara maka ne?Yakalli Hajiya kamar be ji abinda tafad’a ba na’am, a ah Alhamdulillah wannan d’inma ban shanye dukaba, yad’auki murfin yarufe kofin.Yad’an karkace kad’an yaciro rafar yan naira ashirin guda d’aya ya’ajiye agabanta”Hajiya ga nawa goron sallar ba yawa. Tayi murmushi”Julaibibi me yawan kenan ALLAH yayi albarka nagode madallah.Sai ga Nasmat ta shigo da babban foodflask cike tam da tuwon sallah”godiyar me wannan tsohuwar take yi?

Idanun ta yasauka akan kud’in takama ha6a wai wai wai sai ta zauna”Hajiya lillahi warasulihi keda mutuwa tafara k’wank’wansa miki k’ofa me za kiyi da sababbin kud’i?Tamik’a mata hannu kawo su kawai,to ke me ma za ki siya ne? Hajiya ta d’auki kud’in ta”zancen ki dutse,zan kuma rasa ba ki, ki zauna jiran gawon shanu kinji ko?Takalli Julaibib”Autan Inna yau take sallah fa.Yamata wannan rikitaccen kallan na shi yayi-yayi tadaina kiranshi da wannan sunan amma tak’i “yan mata kyau da sallah idan tawuce sun zama jakai.

Tagalla mishi harara”wallahi ALLAH yasauwak’e ai kaima ka san ba ma cikin irin wad’annan kucankan ‘yan matan. Adai fad’ama wanda bai sani ba”ai kaima ka sani kana kuma gani ganin idanunka.Yad’an kalleta”uh ke dai abar tuna ba ya kawai wai gyartai ya ci sarauta,yajefa mata rafar ‘yan naira biyar guda d’aya”ga shinan gaba d’aya ‘yan matan dake zuri’ar Hajiya za ku raba,kowacce ki tabbata kin ba ta dan ba wacce zan kuma ba sisin kwabo na, yanuna Sudaida sai ki fara da ita.Tasa kud’in a jaka tabbb… Wannan shine tazo muji ta tawuce ta bayan kunni wannan nawane ni kad’ai kai dasu wallahi…bai saurare taba yama Hajiya sallama yatashi yatafi.

Yaya Julaibib tabishi zaure.Yajuyo “na’am.Dan ALLAH rake za ka siyo min idan za ka dawo anjima.Yakalleta cikin natsuwa”Sudaida a ina zan samu rake yau sallah fa ai basa fitowa. Tad’an marairaice “ALLAH bayan sallar la’asar za a samu wanda yafito.Yad’an motsa kafad’a”idan an samu to.Nasmat da Sudaida su suka gyara naman suka soya ma Hajiya,dan dama sun iya kome an horasu da aiki.

Yadda yake juyi a kan gadon cikin sulusin dare dan ba ya jin bacci,haka yake juya kalaman Hajiya”to na samo maka matar aure…amma dai aikin gama ya gama…yagyara rufa yana dad’a d’ora kanshi a saman matashin “hummm…wacece matar?Wacece ita? Yakad’a kai cikin sauke numfashi”ALLAH yajik’anki Megado… Wani tunani yad’arsu a zuciyar shi game da Sudaida,sai kuma yagirgiza kai”abun dakamar wuya…toh yanzu da Hajiya take wannan maganar “idan yarinyar bata mishi ba fa?Yana jinjina irin zaman da za ayi na har k’arshen numfashi ne fa, yagyad’a kai”abu mafi sauk’i suyi magana da Hajiya tafad’a mishi ko wacece,idan bata mishi ba toh a canja mishi da wata tun kafin Iyaye suji maganar.

Daga masallaci sallar asubahi yaje yasa mu Hajiya da maganar amma fau-fau tak’i yadda suyi ta”wai ai yarinyar da d’an sauran ta,za ta fad’a mishi a lokacin daya da ce,kuma ba ta dawani makusa dole ma ya so ta tunda itama macece.Dole ya hak’ura yatattara yakoma inda yafi wayau…Ko hutunan da suka d’auka dasu Hajiya bai tsaya ya kar6a ba,dan Hajiya tace bata san wani hoto a waya,dole suka kira Misbahu me hoto ya d’auke su na kati,bai ma yi sallama da yan’uwa kamar yadda yasa ba ba.

Tana wanke kayan makaranta Asma’u takawo mata waya”ga shi ya damemu da kira.Waye?Bata yi magana ba ta ajiye wayar a gefen ta,tajuya tayi tafiyarta. Aka sake kira tad’aga tana d’an turo baki kamar yana ganin ta”ni dai ALLAH na yi fushi.Shi yasa nake ta kira kika k’i d’agawa?A ah wayar tana d’aki na sa ta a caji,ni kuma ina tsakar gida ina wanki,ALLAH da gaske Yaya d’ansarai naji haushi dana je gida neman ka Inna tace wai asubanci kayi.To kiyi hak’uri. Nayi. Yauwa nagode ALLAH yamiki albarka. Amin. Sudaida…yakira ta. “Na’am.Baki fad’amin hotunan da mukayi a masallacin Idi sunyi kyau ko basu yi ba?Tayi yar dariya”sunyi kyau musamman wanda muka yi da Hajiya.To d’an turo min ta whatsapp”tabbb…ai kawai kayi hak’uri idan kadawo ka gani ganin idanun ka.Yayi murmushi “wato kin rama ko?To shikenan ki ajiye min,nima a makon nan zan shigo,kin ko ajiye min dambun naman ko duka kika ba wannan yaron?Ta gane wanda yake nufi amma sai tace”Yaya Julaibib wani yaro zan ba dambun nama har da na ka? Saurayin ki…yafad’a a dak’ile.Kai dan ALLAH Sinan d’in ne yaro?To dame kwad’o yafi gaya?Zak’i. Yabata amsa a tak’aice kafin tace wani abu ya katse wayar.

Julaibib Abdullahi d’ansarai…Yana gama degree d’in shi na farko ya d’ora degree na biyu(masters) a dai Islamic Studies baya wani samun zama kullum cikin zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Zari’a har ya kammala kome sai karatu da za a fara ba kama hannun yaro yazo gida yayi mako d’aya sannan ya tattara yakoma dan cigaba daka inda aka tsaya,shi dai Musaddiq bai cigaba ba sai harkar kasuwancin su ya keyi,yana kuma yin kome tsakani da ALLAH,kome a rubuce yake sai Julaibib ya zo ya nuna mishi.

Sudaida tana zaune a tsakar gidan su Swachet wata yar ajin su ce ta je kar6o takaddun WAEC na shekara uku da suka wuce wanda Yayan ita Swachet d’in ya rubuta,tana so tad’anyi nazarin su,tana zaune zaman jiran Swachet takwaso matasu a d’aki.Tayi tsai…na wucewar wasu dak’ik’u da tunanin waye to da wannan aikin?Karo na uku kenan ana lek’owa ana komawa,to mutanan da suke shiga gida kai tsaye ko macece ko namijine indai ba mara gaskiya ba wazai yi haka?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button