GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tamik’e cikin sand’a dan san ganin ko waye.Caraf idanun su yahad’u,tabud’e idanu cikin mad’aukakin mamaki da tsoro, tanuna shi da yatsa”Sinan kaine kake lek’e?Me kazo yi anan unguwar? Ya sosa kai yana mata d’an murmushi” wai dama kece?Me kika zo yi anan?Tayi jimmm… Tana mishi kallan nazari kamar ba shi da gaskiya sai waige-waige yake yi”kar mu maimaita tambaya ba amsa mana. Yasake sosa kai yana murmushi “Sudaida sarauniya ta… Wallahi na fito shan iskane kawai, sai kuma naga wata kamar ke shine nake lek’awa,yakalli agogon dake d:aure a hannunshi “kai jama’a lokaci fa ba wuya,kin san yau akwai wa’azin maza a gidan bak’i, muje mana,yad’ago yana kallanta har yanzu itama shi take kallo “lafiya kuwa Sudaida?Tagirgiza kai”ni mamaki kake bani wai duk girman cikin gari karasa inda za kaje kasha iska har sai ka shigo nan daba bahaushe ko musulmi me sallah ko d’aya? Ni fa wallahi Sinan ba na ga ne ma wasu al’amuran na kafa gaskiya.Anya Sinan…?Yatare da sauri cikin dad’in baki da rantsuwar ba abinda yakawo shi,har sukayi sallama yajuya da sauri yabar unguwar. Takama ha6a “Sinan fa kamar ba shi da gaskiya tajijjiga kai akwai lauje cikin nad’i.

“Hey Ibrahim…

Swachet ta dafa ta,me kika fito yi a waje? Sudaida tajuyo cikin sauke numfashi,sannan tasa hannu tazame hannun Swachet daga kafad’arta”na sha fad’a miki mu addinin mu na musulunci yaba Iyaye girma na alk’adari akan Ya’yan su, mu kome sunan mahaifin kane ba ka kiran sunan shi kai tsaye ba dan ya haife kaba sai dai dan yaci darajar sunan mahaifin ka ko mahaifiyar ka,ni sunana Sudaida to banga dalilin da zai sa ke kuma kidinga kirana da sunan mahaifi na ba,wannan al’adar turawar ba da Sudaida ba gad’a da fatalwa.

Swachet tawatsa hannaye cikin halin-ko-inkula”ni banga wani abu ba fa.Takar6i takaddun tana gyad’a kai “tunda baki gane me nace miki ba ko?Tad’an ta6e baki tana yar dariya”Sudaida kin cika shagwaba tun muna JSS Class idan an miki abu sometimes sai kin turo d’an k’aramin bakin nan naki kamar gidan tsutsa gashi har yanzu as a matual baki bari ba haka zaki haifi Ya’ya idan sun baki haushi kidinga musu? Takai mata duka. Sukayi dariya.Muje in taka miki amma ba da yawa ba, dan akwai wanda nake jira.Sudaida takalleta da sauri”waye shi?Ko kema kin fara zuwa kwanan gidan ne.Tayi d’as da yan yatsunta”God forbid bad things ni da zan zama sister,ni bani da saurayi ma, sak’o kawai zai kawo min in kaima budurwar ta shi.

Tibishi yatare shi”wai har ka dawo sai kace akan k’aya kake?Yafad’a kujera tare da lumshe idanun shi na wucewar wasu yan dak’ik’u sannan ya bud’e su”ai ban ma k’arasaba na had’u da Sudaida.Yacire kofin bommi(ruwan kwakwa) dayake shirin kaiwa bakin shi,yana mishi kallan uku ahu”to me kake nufi?Ya ajiye kofin a saman tebur yahad’a hannayan shi waje d’aya yad’ora ha6arshi akai”wai tsoron yarinyar nan kakeji?Har yanzu baice kome ba,ya daiyi tagumi yana zancen zuci”zan bar abinda nafara kawai tun kafin wankin hula yakaini ga dare,kwata-kwata bani da kwanciyar hankali.Tibishi yaja dogon tsaki sannnan yamik’e yabar d’akin yana zagin Sudaida, Sinan,hausawa dama duk wani wanda yake sallah harda Katafawa yan’uwanshi a jinsi da d’aukacin masu sallah na doron duniya gaba d’aya.

Yatsaya a k’ofar d’akin-girkin yana kallanta tana kwasan tuwon dare,tayi kyau cikin riga da zani da d’ankwali na atamfa ruwan hoda da ratsin k’ananan filawoyi ruwan makuba,d’an k’aramin bakinta yanata kyalkyallin man le6e ruwan hoda”miyar me kikayi?Ta yamutsa fuska tana turo baki”labarin zuciya a tambayi fuska “miyar shuwaka.Yayi yar dariya”da kan ki? To Yaya Julaibib ya zanyi?Sarkin yawa ai ya fi sarkin k’arfi shi sukace suna so,na ce bazan yiba,Umma ta ce wai dole shi zanyi duk da itama fa ba wani so take yiba,ai wallahi gidan Hajiya zani bazan rasa abin sawa abakin salati ba.To yi sauri ki gama sai mutafi tare nima can zani barinje mu gaisa dasu Mama.

A gidan Hajiya tana cin sinasir da miyar taushe,Julaibib da Hajiya suna hirar data shafe su,saiga Sinan yashigo da sallama.Hajiya ta amsa sallamar”wa alaikumussalam lale maraba da Sinan,bismillah.Yashiga yazauna cikin girmama yana gaisheta.d’ansarai yad’aure fuska ko kallan shi bai yiba yacigaba da duba wayar shi.Sinan yakalli sarauniyar ta shi kamar itama batayi maraba da zuwan shiba,yad’an sosa k’eya bayan ya ajiye ma Hajiya ledar d’aya shigo da ita,Maltina da madara ta ruwane a ciki “Hajiya ba yawa ni zan wuce.”Hajiya tamishi godiya da sa albarka.Har yasa takalman shi Sudaida ba ta da niyyar ta shi.Hajiya takama ha6a tana kallanta ta”Oh ni ‘yasu, Sudaida kar6i nan tamata dak’uwa.Tamik’e tana k’unk’uni.

Shima Julaibib yamik’e”Hajiya magriba ta gabato.Tabishi da kallo “gaskiya ne gwamma ai harama dan a samu jam’i.Yazo yawuce su a k’ofar gidan kamar bai gansuba.Sinan yasauke numfashi “d’ansarai ALLAH yayi miskili,magana ta fatar baki bayan sallama rabon da muyi ta har na manta shekarar.Tad’an harareshi”ai dai ba ga ba yake yi dakai ba tunda zai maka sallama, rashin maganar ma ai kamawa takeyi a d’aure me d’aurewa.Yayi murmushi kawai”ba ta so ayi maganar Julaibib yanzu sai taji haushi,kad’an sukayi hira sukayi sallama dan anfara kiraye-kirayen sallah daga mabambantan masallatai.

Tibishi yatari numfashin ta ta hanyar kyalkyalewa da dariya”mahak’urci mawadaci ne Zigwai, yabud’e hannunshi na dama, ya fa riga ya shigo tsakiyar tafin hannunki kin riga kin mishi kattt…kisan mummuk’e, bashi da wani kata6us sai yadda mukaja da akalar shi musamma ma ke; yad’auki kofi yazuba mata bommi”sha kijik’a mak’oshinki “tanasha suna dad’a tattauna yadda za su 6ulloma al’amarin,yanzu abinda za ayi ki kirashi a waya yazo yad’auke ki,idan kuma bazai samu zuwa ba to da yamma yazo Fajumali-Hotel.

Tagalla mishi harara”kaima fa wasu lokutan shawarar ka ba ta d’auka bace.Kamar yaya ba ta d’auka bace?Tamik’e tana sa6a jakarta a kafad’a”to tayaya zan kama d’aki a Hotel d’in dake cikin gari tsakiyar hausawa?Sannan shi kuma kana ganin zai yadda ko hanyar yabiyo bare har aganmu tare?Yabata hannu suka tafa “shegiya yan mata wannan k’wak’walwar ta ki ba laifi tana ja,amma kafin ki wuce ya kamata kid’an bani na kashewa.Ta6alle jaka tawatsa mishi dubu biyu”kai kudin ka ba sa k’arewa a kome sai a burkutu(giyar k’ok’o) yanzu na san D’One zaka tafi.Suka fito yakulle d’akin yana bata amsa”kamar kin sani dan Alhamdu ma yana bina bashi.

Cikin fushi yashiga d’akin tana zaune a kujera tana chatting,sai ta ajiye wayar tana mishi wani murmushi tare da gewaye hannayen ta ajikin shi tana mishi wani irin salon jan hankali”hey dude just chill up” abinda take mishi ya ka sa daurewa,dan haka yabiye ma yarima aka sha kid’a,wucewar wasu dak’ik’u sai ga shi yana kwasar dariya,yad’an shafa cikin shi”wallahi yunwa nake ji rabo na da abinci tun na safe.Tajawo abincin gaban shi “kaci ka k’oshi dakai na nadafa maka,dan ka fara zama na musamman a cikin zuciya ta,tasake kashe murya da wani irin salon na yan duniya”Sinan ALLAH ban had’a soyayyarka dana kowani namiji ba,saboda samun irin ka a cikin maza sai anyi da gaske,ina sanka Sinan.Yayi murmushin jin dad’i “ALLAH dagaske Zigwai?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button