GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

A yangance ta amsa”ga kai ga k’afa ai ba tambayar me aka yanka. Yakai loma bakin shi yana gyad’a kai”gaskiya na gani ganin idanu na, yagama cin abincin yamatsar da sauran gefe, wayar shi da aka kira ta katse musu hanzari, yad’aga cikin ladabi”a ah bana kusa amma dai yanzu zan zo,yakatse wayar yana kallanta “Babana ne yake son gani na yanzu.Tamotsa kafad’a”ba matsala,amma ai za ka dawo ko?Yamik’e”wannan dole ne bani mukulli idan nadawo ba sai nazo inata k’wank’wasawa ba koda kinyi bacci.tad’an taka mishi zuwa bakin k’ofa”kasiyo min balangu. Yagyad’a “kin samu balangu kin gama.

Tibishi yak’araso yana dariya”akwai ranar kin dillanci…a ranar za ka gane da gero ake koko.Zigwai ta 6ata fuska”gaskiya ka daina zagin saurayi na.Yashige d’akin yana zagin ta”kaji yar duniya,saurayin ki ko dadironki? Tawatsa hannaye “what ever,idan ba haka ba zan fad’a mishi.Yaja tsaki”idan kin fad’a mishi sai me?A saran wa? Kafin me riga yarufa,me bargo yayi gumi. Yak’arasa cinye abincin da Sinan yarage,yana ta janta da hira tace”a ah zo kawai kayi tafiyar ka dan yace zai dawo.Yamik’e”to sai da safe,yakamota yana k’ok’arin ba ta sumba,ta ture shi”katafi mana indai ba kwa6armuce kake so tayi ruwa ba.

Yak’ara matsawa kusa da ita”haba ‘yan mata,dan dai d’an alakoran daza ki bani ai bazai sa ba bazai rage ba,tamu dake ba ta 6aci, yazuba mata idanu”anya banyi ihu da kirari na da6ama kaina wuk’a ba? Tagirgiza kai”bakayi haka ba Tibishi”marakiyi ai ba abokin tafiya bane” tamishi rad’a a kunni,ya bud’e idanu yana kallanta “ta jijjiga kai”na rantse da ALLAH da gaske nake yi,suka kyalkyale da dariya suka tafa”shegiyar duniya to mukwana lafiya,amma kirage min kayan dad’in daya kawo miki, tagalla mishi harara”ba zan ajiye ba d’an rainin hankali,kura da shan duka gardi da k’wace kud’i?

Tibishi yana hango Zigwai ta sauka a kan mashin yatareta”me za kiyi a cikin gari?Tamishi wani kallo”ji wata banziyar tambaya kai me kazo yi?Ni cikin gari wajan zuwana ne.To nima haka zani wajan Sinan ne kwanaki hud’u kenan baya amsa wayata na tura mishi sak’onni sun fi guda goma nan ma ba amsa dan haka zani ingani ganin idanu na ko lafiya?Yad’aure fuska”ke Zigwai ina fata kina sane ke ba wata tsiya bace a wajan Sinan? Tayi shiru, yakalleta”to rashin jinshi a waya kuma ya samo asaline da irin zirga-zirgan bikin shi daya gaba to,kin san suna gama WAEC za ayi auran to saura kwanaki sugama zana jarabawar. Dammm…zuciyarcta buga.

“Sinan zai auri Sudaida???!!!

Tayi d’as da yan yatsun ta”incredible! Haka mukayi da kai Tibishi?To ko ba haka mukayi ba to ke kina ganin kai tsaye za kice Sinan yabar auran tane bai d’auki ke wacce taci kai ba? (hauka)Tarik’e k’ugu tana kallanta d’ai-d’ai kun mutanan da suke kai-kawo a cikin hantsin saboda sanyin da akeyi, suna tsaye sai ga su Sudaida sun zo sun wuce a mota,tabi motar da kallo har ta harba saman kwalta.Sudaida ma tagansu”wai a wannan mugun sanyin amma tayi irin wannan shigar me kama da tsirara,takada kai”ALLAH yasauwake.Tibishi yasauke numfashi”muzauna musan na kwatanci fa,kar k’aramar magana tazama babba, tagirgiza kai”ni fa yau sai na ga Sinan.Yad’aga murya dan tafara bashi haushi”wai ba na ce miki Sinan ba ya gari ba?To indai haka ne gwamma in koma gida dan ba saboda kai nafito a wannan sanyin Jauran ba.Yad’aga mata hannu “sauka lafiya.

Sudaida tabishi da kallan tuhuma saboda karo na bakwai kenan ana kiran shi a waya yak’i yad’auko ta daga aljihu ma,bare yaga me kiran.Yad’an motsa kafad’a “share kawai.A share kamar yaya?Bai yi magana ba yaciro wayar a aljihu yana nu na mata kingani sunan Zigwai yafito 6aro-6aro a fuskar wayar sai yamayar aljihu yana mata bayani”wajan aikin mu d’aya dashi,to wasu takaddu yabani in cike,na kuma san tambaya ta zaiyi idan na cike su in kai office,ni kuma gaskiyar magana zuwa wajan ki yafi kai takaddun mahimmanci…ba zato sai ga Tibishi “jaba Sinan irin wannan abun da kakeyi ba kyau,ya kama ta aba duk me hakki hakkin shi.

Cikin fushi Sinan yatare shi da hayagaga har abun yaba Sudaida tsoro da mamaki saboda irin zagin daya mishi”dan abu kazan uban ubanka baza a bayar ba ayi wacce za ayi dan dan iska kawai…idanun Sinan sun kad’a jawur saboda 6acin rai yanuna Tibishi da yatsa “ka6ace min da gani kafin in 6alle ka.Au haka kace? Yajijjiga kai”eh haka nace dan abu kazan ubunka.Yajuya yana kwafa”na rantse da ALLAH Sinan za ka gane da gero ake koko,za ayi walkiya kuma kowa zai gani ganin idanun shi;kura ce lullu6e da fatar akuya.Sudaida takalleshi”me kalaman Tibishi suke nufi ne?Yawatsa hannaye “Oho mishi ba mamaki yaje ya shata ne bata fad’a mishi gaskiya ba,zanbi shawararki kawai gwamma muyi hannu riga dan nagaji da rashin mutuncin shi.Tayi tsai tana kallanshi “rashin mutunci,to me yahad’aku da yake maka rashin mutunci?Bai bata amsa ba yasauke numfashi, yabata tsaraban Kaduna sukayi sallama.

Tunda yakwanta yakasa bacci sai juyi yakeyi,zuwa can yamik’e yad’auki mukullin mashin yafita, gidan au Zigwai yatafi,tana tsaka da bacci yata sheta, tamik’e zaune akan gadan tana mitstsike idanu kamar gaske”na gaji da jiranka,tafara mishi abinda tasa ba, yarik’o hannayen ta,yakalle ta cikin natsuwa”Zigwai kiyi hak’uri da duk al’amuran da suka faru a tsakanin mu,kin sani aure zanyi,dan haka ba zan dinga barin matata ina zuwa wajan kiba,yaciro rafar d’ari biyar guda d’aya yad’ora mata a cinya “ga shinan ba yawa,amma a hakan idan kikayi maleji zai isheki kija jari, basai kin cigaba da sai da mutuncin ki a wajan sauran maza ba.Tafizge hannayen ta”me make nufi? Kana nufin mun rabu kenan? Incredible!Rabuwa da kai ba abu me sauk’i bane,sai ta fashe da kuka,kuka me ta6a zuciyar duk wanda yaji bare kuma shi da ake kukan saboda ana son shi,ba a son rabuwa dashi.Idan yacigaba da zama za tasamu lagonshi dan haka yamik’e,dasauri tasha gaban shi”idan kamin haka kaci amanar kauna,wai duk irin sadaukarwar dana ba ka a soyayya?Yakalleta cikin tausayi da tafasar zuciya”ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru,tagyad’a kai cikin hawaye”fad’i duk abinda za ka fad’a dan wanka da gari ba maganin yunwa yake yi ba”to kiyi hak’uri kawai ai ni da ke ba alk’awarin zama na har bada mukayi ba, bare kice na ci amana.Yajuya zai tafi.

Tafara mishi wani salo daya sa shi tsayawa”Sinan na yadda za mu rabu amma ina fata baza ka sani a kwandon sharaba,idan mun had’u zamu dinga gaisawa.Yagyad’a kai”dan wannan karki damu.Takashe shi da murmushi “saura abu d’aya tsakani na da kai,kuma alk’awari kayi ranar birthday d’ina za kazo”you’re the special quest of honour” idan ka halacci wajan to ka gama biya ta,kuma ka fita ko ba sabulu.Karki damu. Tasake shi yatafi.

Tabishi yafito daga bayan labulen daya zagaye d’akin,nan yashige lokacin dayaji tsayuwar mashin yalek’a ta taga yaga Sinan ne, sukayi dariya suka tafa,yakai hannu zai d’auki kud’in a saman tebur tariga shi.Yakalleta “banga ne ba.Tagyad’a kai”ai nima zan fiso kaita zama cikin rashin ganewan,wallahi idan na ba ka dayawa dubu biyar.Yakarkace kai yana kallanta da mamaki”dubu biyar zan samu?Tazuba mishi idanu”to ina laifi dubu biyar a wannan marran,karanka ne yakama?Yakad’a kai”lallai kin cika yar duniya hayak’in taba.Takwanta tana dad’a jan bargo”maraina kad’an dai 6arawone,malam idan za ka kwanta kazo ka kwanta,idan ba ka jin bacci to ta shi kasan nakwatanci karka hanani bacci gobe sammako zan buga zuwa Zuturung. Yagalla mata harara”zuwa wajan wani dadiron na ki?Takyalkyale da dariya”ina da wani dadiro ne daya wuce kai?Hummm…bari dai mugama da wancan shegen bahaushen sai muzo mufara shirin aure.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button