
Suna cin dafaffiyar masara tashigo da sallama tazauna tana gaishe da Hajiya tare da fad’in “Hajiya gani ance kina kirana”Hajiya tabita da kallanta nazari, tarame tayi wata iri ba ta cikin wal-wala gidan na tama yau kwanki biyar kenan bata zo ba,shine ta aika akira ta”kwana biyu ban gan kiba ko lafiya?Lafiya lau”ta amsa a tak’aice.Hajiya ta gyad’a kai”to d’auki masaran kici mana,ni fa gaskiyar magana yarinyar nan ba ta da lafiya,Julaibibi wai ko kuna ganin yadda take k’arewa kamar kud’in guzuri? Dammm…zuciyar shi tabuga daya d’ago Yakalle ta, yacigaba da kallan ta ba tare daya ce kome ba.Hajiya tagyad’a kai”ah to kaima ka gani ko?
To tunanin auran ne yamaida ke haka kome? Shima Sinan d’in kwana biyu shiru ko dai kunyi fad’a ne? Zuciyar ta tayi rauni,ba abinda take son yi sai kuka,bata 6ata lokaci ba tafara sharar kwallah a hankali sautin kukan kefitowa hawaye sharrr…sharrr…masu d’umi suka fara sintiri a fuskarta,tacigaba da kukan ta har da sheshshek’a;ba wanda yahana ta sai da taci tak’oshi sannan dan kanta tayi shiru,tahaye gadon Hajiya ta kwanta.Julaibib yayi shiru ran shi ba dad’i”mecece matsalar Sudaida ne?Kira yashigo wayar ta tad’aga da dishashshiyar murya”ina gidan Hajiya ne,tad’anyi sauraro…kayi hak’uri Sinan bana jin dad’i ne kabari sai gobe ko kuma kaba Yaya Khausar za ta ajiyemin…Cikin shashshek’ar kuka tace”to Sinan nagode…
Hajiya tata fa hannaye cikin sallallami “Oh ni jikar mutum hud’u,amma wannan yarinya ALLAH yashirye ki,ba yanzu nagama tambayar ki ko ba ki da lafiya ne kikace ke kalan ki ba?To ai shi kenan kowa rai yama dad’i barin me shine. Tamik’e tana sa hijab.Sai ina? Julaibib ya tambayeta.Tad’auki mukulli tana kallanta Sudaida “idan kin gama kwanciyar jin dad’in za ki tafi gida ban dawo ba to dama karki kuskura kibar min k’ofa a bud’e,tamaida kallanta ga Julaibib”gidan Sahura za ni.Hajiyarmu adawo lafiya,nima dana gama cin masarar hannuna zan tafi.
D’akin yayi shiru wucewar wasu dak’ik’u har yagama cin masarar ya ajiye totuwar yamik’e yana kallanta”tabbasss duk wanda yayi ihu to taimako yake nema”Sudaida ALLAH yadafa miki akan damuwar ki.A raunane ta amsa”amin Yaya Julaibib nagode.Yaja numfashi yafitar da iskar tabaki ta hanci”ni gobe zan koma makaranta, inaga sai ranar d’aurin aure Insha-ALLAH da sassafe zan taso,na san zan samu d’aura aure,su Nasmat duk sun fad’amin abinda suke so in sai musu,ke ma me kike so in sai miki?Tamik’e zauna da sauri cikin rawar muryar data rasa dalili”sai ranar d’aurin aure?Kana nufin bazan sake ganin kaba sai ranar da ALLAH yayi?Kwallah yacika idanun ta.Cikin rashin fahimta yakalleta”kamar yaya sai ranar da ALLAH yayi? Yaya Julaibib ranar d’aura aure to a ina zan ganka? Kuma ranar za a kaimu gidan aure,washe gari za ka koma makaranta to yaushe zan ganka? Kana nufin sai ranar danazo gida idan kana gari sai mu had’u?Ko zaka dinga zuwa gida na?Yagirgiza kai”me kike so Sudaida? Yayi tambayar da wata irin murya data sa Sudaida d’ago kai da sauri tana kallan shi cikin dukan zuciya.
Yadafa k’irjinshi dai-dai saitin da zuciya take”zuciyata ayan kwanakin nan tana min wata irin bugawa da ban san abinda zan kwatanta miki ba Sudaida, na kuma rasa gane dalilin haka,ni fa tun bayan rasuwar marigayiya(Bilkisu)har yanzu ban samu kwanciyar hankali ba,bana yin ishashshen baccin da masana a harkar binciken lafiyar d’an Adam suke bada shawarar a kalla duk dare kayi baccin a wanni takwas.
Yasake kallan ta cikin natsuwa “Sudaida kome da kika ga ina yi dauriya ce kawai; amma ciwon yana nan a zuciya ta kamar yan awannin da suka shud’ene,yad’an yi yake”koda yake baza ki fahimci radad’in rabuwa da masoyi ba!!!Toh ina miki fatan alheri a gidan auran ki dafatan zama na har abada,mutu ka raba takalmin kaza,ina miki fatan samun babban rabo a alk’iyama Darul-karamah dake da zuri’arki…Yaya d’ansarai…yakauda da kai,yakuma riga ta magana”tunda baki fad’i abinda kike so ba,toh zan ba Asma’u gudummawa ta, zata kawo miki har gida.Bai jira amsawar taba yajuya da sauri yatafi.Tabi bayan shi da kallo dan ya mata susa a inda yake mata k’aik’ayi.
“Rad’ad’in rabuwa da masoyi!…
Tafad’a tasake maimaitawa,rad’ad’in rabuwa da masoyi!!! Sai tasa kuka wasu zafafan hawaye suka zubo mata sharrr…sharrr…wallahi Yaya d’ansarai nima ina jin rad’ad’in… Wai…! Wayyoh…! ALLAH na!!!!
Nasmat data shigo tayi tsai…tana kallan ta cikin nazari,tarik’e ha6a”ikon ALLAH nazaune ya fad’i,a zaure sukayi kaci6is da Julaibib yana cikin damuwa tana mishi godiyar gudummawar daya ba yar a ba ta,sai yamata wannan rikitaccen kallan na shi yayi kamar baiji abinda take fad’a ba yayi tafiyar shi,tana tunanin me yasa meshi tashigo, toh ga Sudaida itama a wani irin yanayi. Tazauna a gefen gadon sannan tadafa kafad’ar ta”jimamin rabuwa da Yaya d’ansarai ne yasa kike wannan kukan ko me? Tarungumo ta”ni fa na shiga rud’ani, Nasmat ban san abinda yake damun zuciyata ba wallahi,amma ko a yanayin bugawarta ta canja,tsoro nake ji… Tasaki Nasmat tana tsaida kukan”Nasmat bana san auran nan…Dama kawai a kyale ni.
Takad’a kai”lallai ma Sudaida na ki wasa ne;kema kin san baza ta sa6uba… Idanun ta suka cika da kwallah”to ni wai ya zanyi ne? Ya za kiyi dame? Har ta bud’e baki za tayi magana sai kuma tayi shiru.Nasmat tayi yar dariya”Sudaida sarauniyar Sinan,kin san me? Kuka bai ta6a zama mafita a cikin matsala ba”ALLAH mahaliccin me kowa da kome za ki kaima kukan ki,zai taimake ki ta inda ba kya zato,nima na yadda ciki ba dan aci tuwo kawai akayi shiba,tabbasss a kwai abubuwan daya kamata yazama sirrin kane,sirri ne kawai tsakanin ka da zuciya.Tamik’e tana rik’o hannayan Sudaida”kin san a kwai makarantar Islamiyya lokaci kuma ya kusa,gwamma muje mu shirya dan ina tsoron ALLAH ina kuma tsoron dukan makaran Malam Jama’are da wannan shar6e6iyar dorinar,tamik’e suka kulle ma Hajiya k’ofa…
Ana dara ga dare ya yi…
Da sauran kuka anci gumba an hana maye.
2 Jumaada Thani 1441
27 January 2020
We Ibrahim’s Daughters ????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi nagoma sha takwas.
Julaibib yana gidan Yaya Karima yana mata sallama Baban Abdul yashigo,yamik’a mishi hannu sukayi musafaha”Malam d’ansarai ya karatu? Yayar ka ta fad’amin wai gobe za ka koma nace haba-haba dai ba shekaran jiya kazo garin ba?Yad’an sosa k’asumbar shi”ai yanayin karatun ne sai a hankali.Baban Abdul yagyad’a kai “maganar iyali kuma shiru mak’atau bulaguro a k’iyama tun bayan rasuwar marigayiya,ga shinan kana kallo k’annin ka mata shida za a aurar.Yayi murmushi”ALLAH yaba su zaman lafiya,amma gaskiya ni yanzu ba aure agaba na.Baban Abdul yanu na shi da yatsa”kai Malam d’an Sarai kar kayi butulci fa…yatare shi da sauri”ba haka bane Baban Abdul,shi aure d’an lokaci ne idan lokaci yayi mutum ko bai shirya ba dole sai yayi.Haka ne kuma”To Ubangiji yaba ka macen albarka,amma idan a kasa himma abun zaifi tafiya yadda yakama ta,a kawo k’arshen zaman tuzuran cin nan.Yayi yar dariya kawai sukayi sallama.