GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ango ka sha k’amshi.Yayi murmushi. To ya shirye-shirye ance aski idan yazo gaban goshi ya fi zafi ko?…Tacika shi da surutu yatare ta”Zigwai nagode da gaisuwa yakatse wayar. Tasake kira yad’aga,cikin dariya tace”haba na Sudaida ba da kan ka asare idan kaje gida kace ya fad’i,ai ban gama ba.Baki gama me ba?Kamar Yaya,me ye tsakani na dake? Babu,sai dai abu d’aya yarage a tsakanin mu,idan kuma kacika alk’awari to ba kare bin damo maganar birthday party na.Na sani ban kuma manta ba,zan cika miki wannan alk’awarin.Yauwa very good.Ita tariga shi katse kiran.

Umma tashiga d’akin tasame ta a kwance”ke Sudaida me yasa kin cika kafiya ne kamar mutanan farko?A raunane takalle ta”Umma kaina ciwo yake yi matsananci kamar zai rabe gida biyu.Umma tad’aga murya”ki shirya kutafi makaranta kin nok’e ba kya jin dad’i, kici abinci kin kafe ba kya jin yunwa,kisha magani kin bud’e taga kin watsasu waje,to me kike so a miki?Tayi shiru idanun ta sun ciko da kwalla.To ki tashi maza-maza kifita yana jiran ki a waje.Tamarairaice Umma…Umma ta tari numfashin ta,tanu na ta dayatsa”ke kul…tashi nace.Jiki a sanyaye tamik’e tana goge hawayen da suka zubo mata da gefen farin hijab d’inta.

Ba kowa a k’ofar gidan,sai kawai tayi zaman ta a d’an k’aramin dakalin dake tsakanin filawoyin wajen”Sinan gajiya yayi kenan yatafi?A hankali tsigar jikin ta yafara ta shi,sanyin yana ratsa ta, a takure tahad’a kai da gwiwa,tafara karkarwa hak’oranta suna dukan juna,tamik’e dak’yar zata koma gida.Yana tsaye ya nad’e hannayen shi a k’irji,yabi ta da kallo tana sanye da doguwar riga na atamfa me duhu da farin silifas, d’azu a gidan Hajiya riga da zani da dankwali na shadda ruwan toka ne a jikin ta,fuskar ta tayi fayau babu kwalliya,idanun ta sun kod’e dagani ba tambaya taci kuka ne fiye dana d’azu ta gode ALLAH.

Luuu tatafi kamar za ta fad’i saboda jirin daya fara d’iban ta,a hankali takoma ta zauna,tasa duka tafukan hannayenta tarufe fuskarta tana k’ank’ame jiki dan bata daina jin sanyin ba.”Sannu Sudaida jiri ko? Tagyad’a kai. Sudaida yakira ta.Tacire tafukan hannayenta a fuska sannan takalle shi,yamik’a mata Farm-pride yoghort d’in hannun shi”ki daure kisha.Tawani marairaice”Yaya Julaibib bazan iya sha ba,amai zanyi.Yazauna a gefen ta sannan yayi k’asa da murya cikin rarrashi”haba Sudaida kiyi hak’uri kisha zai miki magani,rashin cin abincin ki ya dame ni,Sagir ya fad’amin kinfi mako d’aya a haka,kullum sai Umma ta tasa ki a gaba kike cin d’an kad’an,yabud’e mata “d’an daure kisha kinji ko?

Yaya Julaibib amai zanyi zuciyata tana ta tashi fa.Yagirgiza kai”uh uh kar6i kisha baza kiyi amai ba rashin cin abincin ne yasa miki ta shin zuciyar.Tasa hannu biyu takar6a,kad’an ta kur6a tamik’a mishi, yagirgiza kai”d’an kara…da haka har sai da tasha rabi,yakar6a yarufe yamik’a mata anjima kidaure kishanye zai miki amfani,kinga yadda kika zama kuwa Sudaida?Takaryar da kai gefen dama”kai baza ka shaba? Uh kisha kawai. Tamik’a mishi hannu”d’an ban dabino… Baya rasa dabino a aljihu yasa hannu ya d’ibosu”guda uku suka rage.Tasa hannu biyu takar6a tana ci.

A mashayar”Beer Parlour”suka had’u da Zigwai.Yaja kujera ya zauna yana kallan ta tana shafama faratanta jan farce ja,tad’ago takalle shi”daga ina kake tun d’azu ka shanya ni?Daga cikin gari mana,na je samo kud’in kashewa ne tunda ke muguwa ce fiance d’inki ba shi da kud’i amma baza ki iya taimaka mishi ba.Tagalla mishi harara”in taimaka maka fa kace?Kai bakaji kunya ba kura da shan duka gardi da kar6e kud’i? Yamotsa kafad’a”a very stingy woman,ba wata kunya dana ji,kin san da ina dashi bazan tambaye kiba,tare ma zamu kashe su.

Tagama shafe faratan ta sannan tasa nailpolish d’in a jaka,tabi wajan da kallo ya cika dank’am da mutane maza da mata ga hasken disco light kore,ruwan bula da ja,wasu na shaye-shaye,wasu suna bin wakar da aka kunna a k’atuwar rediyon,tamaida kallan ta ga Tibishi “birthday party na bazai yiwu a ranar lahadi ba,na maida shi ranar juma’a.To saboda me?Tad’ora duka hannayen ta a saman tebur d’in”dole ranar juma’a zan yi shi saboda ranar juma’ace d’aurin auran Sinan ka gane manufa ta?Yajijjiga kai”na ga ne,kinyi tunani me kyau,amma fa a tsorace nake kar kwa6armu tayi ruwa.Yaba ta k’warin gwiwa “hey just chill up”kwa6armu baza tayi ruwa ba,duk abinda zai faru indai munci gari ba damuwa,ai ranar biyan buk’ata rai ba a bakin kome yake ba inji k’uda.

Da yammacin ranar laraba,rana tayi sanyi Hajiya takira layin Julaibib yad’aga da sallama yana yar dariya”Oh Hajiyar mu na yi kewar kifa”taja tsaki”kai tafi can kaba ni waje,ka yi kewa ta amma tunda kasa k’afa kabar garin nan kaka sa kirana?Ayya Hajiya ta ke kad’ai,kin san d’an makaranta yana fama da geron Sunday(garin kwaki\rogo)ba ta siyan katin waya nake yi ba.Yadda yayi maganar cikin jimami da tausayin kai yasa Hajiya tayi dariya”Julaibibi kana dani amma katsaya fatarar katin waya?To bari yanzu za kaji alert..Yauwa Hajiya ta nagode miki ba kad’an ba Ubangiji yak’ara girma.Amin Julaibibi. Hajiya ina cikin damuwa,na ka sa samun natsuwa.Ashsha me yake damun ka Julaibibi?Tun ranar dakika fad’amin kin samo min matar aure,Dan ALLAH Hajiya ba wai butulci zan yi da za6in ki ba,dan na san baza kimin za6en tumun dare ba,to amma alfarma d’aya nake nema kifad’amin wacece ita?Taja tsaki”na d’auka wata lalura ce ke damun ka?To yar gidan Kawun kace.Wane Kawun nawa?A ah to kuma nan d’aya ni dai nafad’a maka sai ta k’ara girma,yo data isa aure tare za a had’a dana su Sudaida ta k’arasa karatun a gidan ka.Yar karama ce kenan,ajin ta nawa?A ji d’aya take a ka’aramar Secondary idan kuma kana so ayi bikin ta girma a d’akinta to,kayi rainon ta yadda kake so.Yayi shiru kamar baiji abinda tafad’a.Hajiya tayi dariya”Julaibibi na to sai anjima ta katse wayar.Yahura iskar bakin shi bayan ya maida wayar shi aljihu,yayi tsai…cikin tunani Kawun nan na shi ai suna da yawa,kuma kowanne yana da tarin ya’ya mata,yayi iya tunanin shi amma bai canko ko wacece ba, yarik’e kugu yana bin d’akin na shi da kallo…

Sinan yana tsaye da mahaifin shi yana ba shi sak’on wasu kayayyaki da zai siyo mishi a Kaduna,Zigwai tak’araso wajan,tana sanye da matsatstsun riga da buje na material ruwan d’orawa an mishi d’inkin rashin mutunci da rashin sanin kimar kai,tantirancinta ya bayyana, tana rataye da bakar jaka,takalmanta masu rufi da tsinin diddige bak’ak’e”Sannu Alhaji tad’an rusuna tana gaishe da mahaifin shi,wani abu yadaki zuciyar Sinan, yad’auke kai daga kallan k’urullan da take mishi.Alhaji yakalle shi sai ya sunkwui da kai.Zigwai tayi wata yar dariya irin ta yan duniya”Malam Sinan angon Sudaida.Yad’ago yana murmushin yak’e,sai ta mik’a mishi envelop “sak’o nakawo maka.Yak’ar6a yana mata kallan tuhuma.

Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi”za ka gane da gero ake koko, Sinan ai sai dai muyi biyu babu. Suka kalli juna shi da mahaifinshi “yadafa kafad’arshi,Sinan ba girma a ganka kana mu’amala da irin wad’annan k’adangarun barikin, ka san shaid’an baya raina k’ofa.Yagyad’a kai “Baba baka yadda dani bane?Sinan ba rashin yadda ce tasa na fad’a maka haka ba,illah gyara kayan ka…ai kai ba k’aramin yaro bane,sai dai tunatarwa tana amfanar da mumini,ai mun ba ka tarbiyya gwargwadon iyawarmu,idan kaje kayi wani abu sa6anin wanda muka d’oraka a kai,to ai ALLAH yana ji yana kuma gani wannan tsakanin ka dashi ne,bazai kama mu da sakaci ba,ni dai idan za kayi sara to kadinga duba bakin gatarin ka, kasan da irin mutanan da za ka dinga mu’amala, ina jiye maka kaidin irin wad’annan da suke ji kamar su juwo mutum ta k’arfin tsiya ya dilmiya. Jikin shi yayi sanyi,yayi nadamar abinda yafara “nagode Baba.Alhaji Kamal yashige motar shi yatafi. Yazauna a wajan cikin damuwa”to wai ma me yakai shi k’ulla mu’amala da Zigwai?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button