
Sun gama jarabawa anyi speech and prize giving day anyi angama lafiya,kowa ya koma gida zaman jiran sakamakon girbe abinda aka shuka.Maganar biki ya dad’a kankama anata shirye-shirye,amare ana shan gyara Umma ce a wannan harkar dan kunsan ita bata d’aukar raini kona sisin kwabo ko ba dan ALLAH ba kowa sai ya bi.
Jajibarin auren su Sinan kai ya d’auki zafi baya samun zama,yana sa takalmi Tibishi yashigo yana kallan shi”maganar birthday party na Zigwai zan tuna maka fa.Yakalle shi rai a 6ace”Tibishi karabu dani,dan ba wannan ne a gabana ba.Yajijjiga kai”nima na sani to amma karka manta alk’awari kad’auka.Yagama sa takalmi yamik’e “Tibishi ta shi katafi akwai inda za ni,suka fito Sinan yakulle d’aki kowa yayi hanyar shi.
Bai dawo ba sai kwanciyar bacci a na ta dad’a gyara gidan amarya,sai da ya tabbatar kome ya kammala sannan hankalin shi ya kwanta, sai lokacin yasamu damar kiran Sudaida.Tana ganin kiran shi tad’an harari wayar tana k’unk’uni, sai da yakira sau uku sannan tad’aga”Sudaida sarauniyata…tatari numfashin shi”ni ba wata sarauniyar ka tunda tun safe baka nemi ni ba,na kira ka na jita a kashe,ni fa kana 6ata min rai. Wayyo ni Sinan to kiyi hak’uri ina can ina hidimta ma muhalllin kine,amma ko ina naje to tabbaci hak’ik’a kina cikin zuciya ta, ina son ki Sudaida… Tace hum…yacigaba’irin soyayyar da baza ta fad’uba,yayi yar dariya ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baici ba yayi burgima,gobe war haka kin zama sarauniyar Sinan ta hak’ik’a,farin cikina zai fara daga gobe ne…yayita maganganun shi batace kome,basu wani dad’e yamata sallama dan zai kwanta ya gaji lik’is.
Farar rana me kyakkyawar suna, wato juma’a.Yan’uwa da abokan arziki cike da gidajan biki an karkasa ayyukan shi yasa nan da nan akayi aka gama.k’arfe sha biyu da rabi Julaibib yasamu isowa garin.Yashiga d’akin-shak’atawar Inna ana gaisawa.Yaya Karima takalle shi”ai na d’auka baza kazo ba.Yad’an shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi”Yaya Karima yanayin karatun ne sai a hankali.
To ALLAH yataimaka.Amin.Yawuce d’akin shi dan shirin masallaci.Yana sanye da babbar riga,’yar ciki da wando na farar shadda getzner,hular shi k’ube da aikin babbar rigar shi ruwan toka da ratsin fari da bak’i, takalmishi sau ciki fari,agogo da zoben shi na farin azurfa sai d’aukar idanu sukeyi saboda hasken su, k’amshin arabian perfume d’inshi me dad’in shaka,ya cika wajan.Duk suka bishi da kallo.Yaya Karima tace “gaskiya autan Inna kayi sharrr…dakai kamar wani ango,Yayi murmushi kawai”kice ma Inna na tafi masallaci.
Yau gaba d’aya hud’ubar akan aure da ma’aurata akayi,bayan an idar da sallah anyi addu’o’i an shafa,auran Hashim da Aisha aka fara daurawa,sai Muhammad da Zainab,Abdullahi da Maryam,Abdulkarim da Nasmat,Huzaifa da Khausar…sai na Sinan da Sudaida da ake shirin d’aurawa,to amma wani wawan burki da aka taka sai da yatshi hankali jama’a,wasu suka fito daga masallacin dan ganin abinda yake faruwa.
Sinan ne yafito daga cikin motar yana sambatu da tam6elen mashayar…Su…Sud… Sudai…damata…ta..taceba…wanda…zai…raba ni da ita… Alk’…wari…ba karyawa mutu ka raba takal…min kaza. Ciki da wajan masallaci kowa yayi d’ifff…ya cika da mad’aukakin mamaki na ganin Sinan a wannan yanayin, a hankali k’ananan surutai yafara ta shi.
Alhaji Kamal sai da numfashin shi yad’auke na wucin gadi yayi mutuwar zaune,dan abun ya kad’a shi”Innalillahi Wa’inna Ilaihi raji’un yake maimaitawa, Liman yakalle shi”dama ka san d’an ka yana shan giya? Yakad’a kai cikin damuwa “Liman bazan maka k’arya ba wallahil-azim ban sani ba,ban san kome game da Sinan ba sai halaye masu kyau.
Sinan d’in aka fitar daga masallacin dan yafara kakarin amai.Liman yakalli mahaifin Sudaida meye abin yi? Kafin yayi magana Alhaji Kamal ya amsa”ba za a d’aura ma Sudaida d’an giya ba,irin wannnan hukuncin zan zartar ko ‘ya tace wallahi,dan haka ina rok’on alfarma a d’aura auran nan da k’anin Sinan,yanuna Hamidan dake zaune a gefen shi cikin 6acin ran abinda Sinan yayi.Liman yabi sauran jama’ar da kallo,yasauke numfashi”k’warai zan so haka,to amma wani hanzari ba gudu ba idan aka had’asu aure Sinan bazai barsu suyi zaman lafiya ba, zumuncin dake tsakanin su na shak’ik’an juna zai samu tasgaro, indai ba tsananin sa a a kaci Sinan d’in me hange nesa da maida al’amura ga ALLAH bane.Alhaji Kamalu kayi hak’uri,ni na san da wanda zan had’a auran nan yanzu da izinin ALLAH gida bai k’oshi ba ai baza a ba dawaba. Yaciro dubu ashirin d’in da kaba bashi zakkarsu dazai taho masallaci “yanzun nan zan d’aura auran Julaibib da Sudaida akan sadaki naira dubu ashirin lak’anan(lakadan) Masallaci yad’auki kabbara.
Alhaji Kamalu mutumin kirki me karamci shi yakar6ama Julaibib auran Sudaida, dubban nin jama’a sun shaida wannan aure. Hamidan yasauke numfashi,sai yanzu yashak’i iskar yanci dayaji ba dashi aka d’aura ba, yama Julaibib da Sudaida fatan alheri da sauran angwaye da amaren,yamik’e yayi tafiyar shi yana rok’ama Sinan shiriya…ALLAH kenan buwayi gagara misali,namiji baya auran macen da ba ta shiba,hakama mace bata auran mijin da bana ta ba…al’amarin aure,al’amarine daga Indallahi,shi yake had’awa sai dai wani yazama silar faruwar shi.
Baban Abdul dake gefen shi yayi murmushi”ango ka sha k’amshi,aure d’an lokaci ne,idan lokaci yayi ko ba a shirya ba haka dole za ayi…ka tuno hirar mu ta kwanaki?Wannan gaskiya ne shirye-shiryen a yi daga baya,yamik’a mishi hannu sukayi musafaha suna murmushi, wallahi shima haka yake ganin abun kamar almara,har suka fito yan’uwa da abokan arziki sun baibaye shi suna taya shi murna da fatan alheri”Dare ga mai rabo…hantsi.Sunan wani littafi na gwanarmu (Halima Abdullahi Amma)Ubangiji ya kyautata makwanci????
D’ansarai…yaji an kira shi.Yad’ago kai bakin shi d’auke da addu’ar”Alhamdulillahil-lazi bi ni’ima tihi ta tummussalihat”jin an daki kafad’arshi.Aminu ne yazare mishi idanu”toh daga yau sai yau na zama surukin ka,dan haka ba sauran raini,idan ba haka ba in k’wace k’anwata ka gane ko?Kome girma-girma kamar tusar jaki. Julaibib yamishi wani kallo “ai aikin gama ya gama,wuk’a da nama yanzu a hannu na suke da dai kafin a d’aura ne to danaji kurarin ka,nagaba yayi gaba Alhaji…Su Musaddiq suka yi dariya.
Yara kowa yafara noman kare(gudu) dan yaje kai rahoto kuma kowa so yakeyi ace shine na farko, tun daga zaure Abdul yake k’walama Inna kira iya k’arfin shi har yashiga tsakar gidan,duk suna tsaye cirko-cirko cikin tararrabin abinda Abdul din zai shigo dashi na tashin hankali”lafiya kuwa Abdul?Sai numfarfashin gudun dayasha yake yi,yana haki da dariya yace”Inna Kawu d’ansarai aka d’aura ma aure. Asma’u dake tsaye kusa dashi batayi k’asa a gwuiwaba ta d’auke shi da wani bahagon mari,ji da ganin shi sai da ya d’auke na wucin gadi”wato wasan da takeyi da kai har yakai haka? Ka dinga mata kiran yan farauta tun daga waje duk ka tashi hankalin mu sannan kashigo mana da maganar banza”wa d’ansarai ya aura?K’anwar ubanka? Yadafe wajen dan ya maru idanun shi suka kawo ruwa,ya kasa magana sai kawai yajuya zai fita. Inna tarik’o rigar shi “Zo mana Abdul d’ina mai gida ran gida,me gida takobi…tayi furucin da sigar rarrashi,tasa hannu tashare mishi hawayen da suke zubo sharrr…”fad’amin gaskiya Abdul,me yafaru a masallaci… Bata gama rufe baki ba sai ga Adnan yashigo da sallama,suka bishi da kallo, yaja kujera yazauna.Cikin jimami yafad’a musu kome. Masu murna na yi masu komawa gefe suna k’unk’uni na yi.Asma’u tajuya zata ba Abdul hak’uri taga ya fita.