GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana sanye da farar shadda,kanshi da farar hula zita,sai bak’in takalmi sau ciki,kafad’arshi ta dama rataye da dudduma,dawo warshi kenan daga sallar juma’a.A tsaye yake a k’ofar gidan yana tunanin kawun nashi jarumin mutum ne me kamanta adalci a komai nashi,ga shi yanaji da mahaifiyarshi da gasken-gaske,yana mata wata irin k’auna ta ban mamaki,kafin asamu me halinshi sai an tona,dan yafifitata sama da mata da ya’ayanshi,yar gatan tsohuwa kenan data kerema duk tsofaffin k’arninta, kai ita Hajiya ALLAH yamata gyad’ar dogo sama ya’ya,k’asa ya’ya tsakiya ma ya’ya,gaba d’aya ya’yanta takwas babu k’ashin yarwa.

Kai Julaibib ka tsaya awaje kamar wani bak’o me jiran abashi izinin shiga?Hajiyace, yakalleta da murmushi”to ai dama ke nake jira “bismillah muje…Suna tafiya suna hira har suka shiga cikin gidan.Musaddiq yafito daga d’akinshi, kaga ban tsaya jiran kaba, wallahi a sahun makararru natsaya,idan su Baba suka fito suka hangoni a haraban masallaci kasan zan sha fadane.Kamar ba dashi yake magana ba yashige d’akin yad’ebi wasu takaddu zai fita,Musaddiq yakalleshi bari akawo mana abinci mana dama kai nake jira. “Bazanciba” Ah bazaka ciba kamar yaya? “Azumi nakeyi” yabashi amsa atakaice. Azumi yau juma’a? Yagyad’a kai “Eh azumin tsakiyan wata sha uku,sha hud’u,sha biyar,to yau sha uku ga wata.Yagyad’a kai”ALLAH yabada lada”yafara kiran Sudaida,Sudaida,shiru Khausar nan ma shiru sai yamik’e to ina jin basanan barin d’auko da kaina,suka fito tare shi yawuce wajan Hajiya, Musaddiq kuma yatafi d’akin-girki d’auko abincinshi.

Sha d’aya da rabi a sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar asabar aka taso su daga makarantar allo, tana sanye da bak’ar abaya da farin hijab,da wasu littafan addini a jakar data rataya a kafad’a,allanta kuma ta rik’e a hannu.Suna zaune a dogon dakalin tazo tawuce kamar bata ganshi ba. Yamik’e da sauri yabita”haba ranki yadad’e Sudaida Sarauniyar Sinan,me yayi zafi haka idanu suke cin wuta?Takalleshi da 6acin rai”wai dan ALLAH kai baka da wajan zamane sai a cikin yan maro (Wiwi)? Zama da mad’aukin kanwa fa yana kawo farin kai. Yagirgiza kai cikin damuwa “Sudaida ba yadda zanyi da sune,ina zaune zaman jiranki suma sukazo suka zauna,wajene na kowa to ya zan musu?Khausar tazo tawucesu da takaicin Sudaida,ta rasa abinda yaja hankalinta wajan soyayyar Sinan.

Bakice kome ba.Sinan yakatse shirun. Tad’an harareshi”ALLAH yaso ka na na huce.Yayi dariya tare da shafa k’irjinshi bangaren da zuciya take.Yauwa ko kefa,kinga yanzu hankalin masoyi ya kwanta.Sukayi hirarsu sannan yataka mata kad’an sukayi sallama,yaso yarakata har k’ofar gida amma tace nan ya isa, dan tasan su Yaya Musaddiq suna wajan da autan Inna,kuma ba tasan wannan rikitaccen kallannashi me ban haushi dan ba magana zai yiba..Taja tsaki”ALLAH yasauwak’e mishi wannan halin…

Nagari ake so ba d’an gariba.

13 Rabi’a Thani 1441
10 December 2019

We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD… 2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in.

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin ????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na uku.

Kasham tabaro k’auyansu Madauci da yammacin ranar talata,bayan taji sauk’i daga jinyar da tayi na tsawon awanni ashirin da hud’u.Tashiga cikin makaranta da d’okin ganin Julaibib ta kuma hango shi a inda suke zama.Tak’arasa da saurinta “Barkanku da yammaci”Maimun abokin karatunshi ya amsa”Yauwa barka dai.Tatsare Julaibib da manyan idanunta masu maik’o cikin kallan k’auna me cike da shauk’i “kai bazaka amsaba kenan?Iskar data d’ibo tama bata isheshi kalloba.Tayi jimmm…na wucewar wasu dak’ik’u tana kissima wani abu a zuciyar ta,sai tad’an motsa kafad’a any way…sai anjima. Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi.

Julaibib my enigma man…Salonka yana k’ayatar dani wallahi”…

Maimun yakalleshi”Kai nifa bangane ma wannan bita da kulli”dukan kabarin kishiyan ba”Meye had’inka da itane duk inda taganka sai tazo wajan?… Julaibib yafad’a mishi kome.Maimun Yagyad’a kai “to ka yadda mana tunda har ta amince za tayi sallah ba kuma wanine ya tilasta mataba,ai inaga ba wata matsala,kuma kayi jihadi ne,gata kuma Masha-ALLAH kyakkyawace.Yamik’e yana mishi wannan rikitaccen kallan nashi”bazan iyaba.Maimun zai sake magana yad’aga mishi hannu”dakata haka malam, taso mu tafi.Maimun yagirgiza kai “ba d’akin da zan tafi yanzu gwamma in d’anyi shawagina.Yajuya yayi tafiyarshi to shikenan.

Yana shiga d’aki ya ajiye Hand-out, yasa hannu yana 6alle botiren gaban rigarshi tare da lumshe idanunshi a kasalance,yacireta rigar yajefa a saman kujera,ya gaji lik’is ga rashin bacci,dan baiyi wani baccin kirki a daren jiya ba saboda karatu da binciken wasu littafai da yake yi na tafsirin Alqur’ani me girma,idanunshi har wani yaji-yaji sukeyi,a a hankali yafurta”yau da wuri zan kwanta…

“Zanzo tayaka kwana…

Bazato yaji an mishi wata irin runguma ta baya,zuciyarshi tabuga dammm…dan wallahi yaji tsoro…

“Zanzo tayaka kwana tunda Musaddiq baya nan.Tafad’a cikin rad’a

Kasham…zuciyarshi taraya mishi, tabbasss ita d’ince danga k’amshin turaranta nan… Yayi k’ok’arin raba ta da jikinshi amma ya kasa,dan ruk’on kura taga nama ta mishi…

Kanshi yayi wani irin sarawa.

Tafara mishi wani salo da hannayen ta a cikin gargasarshi dake kwance lufff bak’ink’irin da sheki…kar…kar…kar…Jikinshi yad’auki rawa”baah…ba… Bahh..banasooo!…dak’yar yafuzgo furucin.Tayi lallausan murmushi tad’ago kanta tana kallan kwantaccen bak’in gashin kanshi…

Meye baka so din…???

Yayi shiru.Tagyad’a kai”tayaka kwannanne baka so ko wannan din?Tacigaba da mishi wani salo da hannayenta a dai-dai saitin zuciya… Jikinshi ya mutu murusss…

My enigma say something hun”

Tasake fad’a cikin rad’a da wani irin salo na ta nayanga.Yadaddage ya hankad’eta…tafad’i tabaya akan katifarsu.Hanyar fita yayi sai dai abin mamaki “talaka da mata hud’u har da k’wark’wara me gari gwauro”ta kulle k’ofar dan dama baiji shigowarta ba.

Daga kwancen take kallanshi, yasunkwui da kai,gaba d’aya ya jike sharkaf da zufa kamar wanda yad’auki awanni yana matso jiki.Wata jijiya tafito asaman goshin shi rad’am kamar shatin bulala ranshi in yayi dubu ya 6aci…Amma jikinshi ba k’arfi kona sisin kwabo kamar wanda aka zarema laka.

Sai kuma jikinta yayi sanyi, tasan itace tasashi a damuwa tamik’e tsaye”Kayi hak’uri Julaibib “tahad’a tafukan hannayenta”Dan ALLAH kayi hak’uri ba naso ace ta dalilina kashiga damuwa,danni me k’aunar kace,farincikin ka shi nake so ba damuwa ba.k’walla yacika idanunta… Muryarta tafara rawa

Bazaka hak’ura bane d’ansarai?

Yadda tayi furucin a hankali da wani irin salo,yasa yad’ago zai kalleta,itama shi take kallo caraf idanunsu yahad’u,yakauda kai dasauri yanajin wani irin abu yana zagaye ilahirin jiki da zuciyarshi,shi yasa baya san kallan wannan manyan idanun na ta masu maik’o.Kawai sai ta fashe da kuka,tsoro da mamaki suka baibayeshi to me aka mata wai???

“Kasham…

Yafurta sunan dak’yar.Tad’ago da sauri tana kallanshi.Sai kuma yayi shiru kamar me koyan had’a kalmomi da yadda ake furtasu.Idanunshi sun kad’a jawur.

Julaibib kayi hak’uri dan ALLAH”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button