GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun shigowar shi d’akin sai yanzu tacire tagumin datayi tad’an saci kallan shi,Bai cire kome nadaga shigar shi ba sai takalmi,k’afafun shi cikin safa.

Sudaida…

Yasake kiran ta”tashi muyi sallah…Tasunkwui da kai tafara shashshekan kuka. Tagirgiza kai”uh uh Sudaida yau fa ba ranar kuka bace,rana ce da za ki k’ara godema Ubangiji dan kin shigo gidan aure, auran nan kuma hanyace da zata sadaki da Darul-karamah..

Yad’auko Kofi yazuba madara yamik’a mata”kar6i kisha.Itafa ya dame ta,kad’aici take buk’ata wallahi,dan haka tace bata sha. Sudaida..Ta tari numfashin shi”Yaya Julaibib nifa gaskiya bazan iya zaman auren nan ba…tacigaba da kuka.

Yayi tsaiii…na wucewar wasu dak’ik’u yana kallanta”idan rai ya 6aci toh hankali yanemo shi,abinda yatuna kenan yamata uzuri dan shima yaji rad’ad’in rabuwa da Bilkisu fuj’atan. Yagyad’a kai”To naji, amma d’an daure muyi salla ko?Dak’yar tamik’e ita fa wani irin hali da yanayi ta tsinci kanta a ciki kamar almara. Bayan sun idar da sallar yayi wannan addu’ar ga wanda yayi sabon aure..

“Allahumma inni as’aluka khairaha wakhaira ma jabaltaha alaihi,wa’a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi”

Duk sukayi shiru na wucewar wasu dak’ik’u, a hankali yad’ago yana kallanta,sai yaciro wayar shi yasaita ta yana d’aukarta hotuna,tana d’ago kai caraf idanun shi yahad’u,tasunkwui da kai da sauri tana dad’a rufe fuskar ta da mayafin, bazato taji ya cire mayafin yarik’o ta yana d’aukarsu tare”Yaya d’an… Sauran kalaman suka mak’ale saboda wannan rikitaccen kallannan na shi daya mata,ta turo baki gaba idanun ta sun cika da kwallah. Sai da yagaji dan kanshi yabari.

Hucin numfashin shi taji a gefen damanta,yayi k’asa da murya”ALLAH yabaki hak’urin zama dani…Yagewaye hannayen shi a jikinta”Kin gaji da yawa ya kamata kiyi wanka da ruwa me d’umi sai ki kwanta kiyi ishashshen bacci ko?Dak’yar tayi furucin”ni ba sai nayi wanka ba. Yagirgiza kai”uh uh sai kinyi wanka za ki kwanta… Yasake ta”kije kiyi wanka,yajuya yafita.

Har tayi wanka takwanta sannan ya shigo tana kwance irin kwanciyar mage.Har kin kwanta”uhhh tace.Yaja stool yazauna yana kallanta”gobe fa sammako zanyi in koma makaranta kilama baki tashi daga bacci ba.Sai taji ranta ba dad’i.Tayi shiru kawai…ko za ki bini mutafi tare?Tad’an dago suka kalli juna”yad’age gira yana mata wani kallo”in shirya miki kayanki yanzu?Tawani marairaice tana zancen zuci”sai kawai aji tabi shi makaranta?Yayi yar dariya yana mik’ewa”kiyi baccin ki kinji,ni akwai nazarin da zanyi”Lailatun sa’ida…fi amanil-lah.Ya tafi d’akin- shak’atawa yana had’a wasu littafai da zai tafi dasu.

Sinan bai farka daga nannauyan baccin daya d’auke shi bayan ya gama aman giyar daya shaba sai cikin sulusin dare.Yafarka da wasu miyagun mafarkai daba su da tushe bare makama, yabi d’akin da kallo zuwa kayan jikinshi,yashiga rarraba idanu”me yakawo shi d’akin Hamidan kuma?K’wak’walwar shi tafara aika sak’onni zuwa bangaren tunanin shi”me yafaru dashi? Yaufa ranar d’aurin auren shine,rana ce ta musamman a gare su shi da sarauniyar ta shi,a kuma daren su nafarko cikin angwanci, yakad’a kai ai sam-sam baza ta sa6uba bindiga cikin ruwa, ruwa baya tsami banza,tar-tar yafara tuno abinda yafaru kafin gushewar hankalin shi.Dammm…Yaji rikitowar wani abu a k’ahon zuciyar shi,kafin kiftawar idanu yajik’e sharkaf da zufa kamar wanda yayi wanka da kayan jikin shi, da sauri ya sakko a gadon kamar zai hantsila yawuce d’akin-shak’atawa anan yaga Hamidan yana bacci a doguwar kujera,kuma d’akin wayammm ba kowa,ba kamar jiya da yan’uwa da abokan arziki suka cika ko ina ba.A rikice ya sunkuya dai-dai fuskar Hamidan yana kiran sunan shi,yasa hannu ya yarfe zufan dayake ta tsatstsafo mishi a goshi a karo na barkatai,yahadiye wani abu mezafi.

Hamidan yayi juyi sannan yabud’e idanu, dan a sama yaji kiran”tashi Hamidan ka zauna.Hamida yatashi yazauna yana kallan shi cikin 6acin rai,wallahi da shine babba sai ya zabga mishi barin makauniya dama da hagu,yakad’a kai”labarin zuciya a tambayi fuska sai kawai yajuya mishi keya.Cikin tashin hankali Sinan yace”dan ALLAH an d’aura aure na da Sudaida?

Yajuyo yamishi wani kallo”tabbasss an d’aura auren Sudaida amma da dan’uwanta d’ansarai dan Baba ma bai goyi bayan a d’aura mata aure da d’an giya ba,yanzu haka tana d’akin mijin ta…yatare shi cikin k’araji da tafasar zuciya”ya ishe ka! Yafad’a kujera yana Istirja’i k’urunk’usss…ta faru ta k’are an yima me dami d’aya sata. Idanun shi sun kad’a jawur Tibishi da Zigwai sun kai shi sun baro.

Yau bak’ar rana ce a gare shi me bak’in muni…yafara tuno abinda yafaru wayewar garin juma’a, a sanda hantsi yadubi ludayi yadawo daga ciro kud’i a ATM dazaiyi hidimar abun sha na walimar dare da za ayi bayan an kai amarya,yasa mukulli zai bud’e d’akin shi kenan sai ganin Zigwai yayi ta shigo gidan na su tak’aramar k’ofa, me gadi yana d’akin shi yana sallar walha,lallai idan ya barta Baba zai iya fitowa kowani lokaci,ga kuma bak’in yan biki,da sauri yazare mukullin daga jikin kofar yamayar aljihu,yaja hannunta da sauri suka bar gidan,suna fita yasaki hannun ta ya wanka mata mari san ya angijeta tayi baya tafad’i,yafara yarfa mata ruwan bala’i”dan abu kazan uban ki meye darin gamata da ke dahar za ki biyo ni gida? Ba mun gama ba,ba kare bin damo?Tawani marairaice”dan ALLAH angon Sudaida kayi hak’uri,ban san ranka zai 6aci irin haka ba, amma nima ai daga yau ba k’ari wankan wuta,na kira lambar ka sau shurin masak’i kaj’i d’agawa, kaga ai dole tasa, dan wajen Party yayi cikar farin d’ango amma ba special quest of honour,tacigaba da marairaita har tasamu fushin daya taso mishi yafara lafawa”dan ALLAH kazo muje ana gama yanka cake sai kadawo. Yagalla mata harara”baza niba ko dole ne?

Dasauri takai gwuiwoyinta k’asa tana mishi wani irin murmushi na yan duniya da jan hankali” haba Sinan dan darajar k’auna da soyayyar daka kema sarauniyar ta ka,yau d’aya dai karka watsa min k’asa a cikin idanu bayan na gama sakankan cewa,ai ka gani ko a jikin katin gayyata an buga kaine bak’o na musamman me girma.kuma na fad’a maka tuntuni ka kuma amince da haka,haba Sinan ai alkawari bai ce haka ba,da tun farko ka fad’amin baza kaje ba ai da na canja ka da wani,tamik’e cikin hawaye tana kallan shi”shine nan nagode…nagode tajuya tayi tafiyarta.

Yabita da kallo,sai yaji ran shi ba dad’i yasake kallan agogon dake d’aure a hannun shi,har yanzu k’arfe goman safiya bata k’arasa ba, bari kawai yaje tunda alk’awari yamata,zuwa goma da rabi sai yamata sallama yazo yak’arasa abinda zai yi kafin lokacin masallaci yayi. Da wannan tunanin yabita,yasha gabanta da mota yabud’e mota gidan gaba tashigo ta zauna”kiyi hakuri Zigwai.Tagirgiza kai”na hakura angon Sudaida,ALLAH zan so ganin ka anjima dan na aan wankan da za kayi zai bambanta da duk wani wanka da kata6a yi,yayi murmushi kawai.

Wajan party ya had’u da had’ad’d’un yan duniya hayak’in taba,dashi aka yanka cake,sai dai agurguje yake yin kome yana kuma yawan duba agogon dake d’aure a hannun shi dan kar lokaci ya shammace shi. Tabishi da kallo”wai wannan duba agogon na meye?Duba agogon me kuma?Sai ta share zancen”me zan kawo maka ne kad’an jik’a mak’oshi?Yaharareta.Tayi yar dariya “ka d’auka ba abinda zaka iya shane?Dan dai kak’i yadda ne amma bommi ba giya bane, ko a zuba maka d’an kad’an?Yagirgiza kai”a ah kusha abun ku,ni dai na san giya ne bommi,tunda idan mutum yasha yana gusar mishi da hankali.Tata6e baki “idan kai baka sha ba ai hausawa dayawa yan uwanka sun sha.Toh Ubangiji ya shirye su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button