
Taje tad’auko katan d’in lemun bakwai a raye(seven alive)ta6arke ledan a gaban shi tazaro d’aya, tabud’e murfin sannan ta d’auko kofi ta tsiyaya kusan rabin kofin sannan takalle shi”ko a cika maka kofin? Yamik’a hannu yakar6a “wannan d’in ma ya isa nagode, yana kai kofin tsakanin la66an shi tayi murmushin mugunta,ta dunk’ule hannu ta naushi iska”k’aramin arne ka had’u da gawurtacciyar arniya.Sinan sai dai muyi biyu babu,baza ka auri Sudaida ba nima ban aure kaba kowa yaji idan da dad’i.Tayi wata irin dariya irin ta yan duniya ganin ya shanye lemun duka “ALLAH yakai damo ga harawa…
Wucewar wasu yan dak’ik’u sai yafara gani garara-garara yanayin shi yana canjawa,d’aukacin jama’ar wajan yafara ganin su suna kasuwa kashi-kashi yana ganin Zigwai da Tibishi suna magana a gaban shi cikin dariya da tafa hannu amma bazaice ga abinda suke fad’a daga haka bai san abinda yakuma faruwa ba.Ashe maganin bacci da gusar da tunani,kuma wanda yawuce ka’ida(over dose) suka zuba acikin wannan lemun guda d’aya,sun kuma yi ma kwalin alamar dasu kad’ai za su gane.
A gida kuma Alhaji Kamal da Hamidan sun tun sha biyun rana suke neman Sinan amma ko sama ko k’asa basu ganshiba, hakama lambar wayar shi sun kira sau shurin masak’i na’ura me k’wak’kwalwa tana fad’a musu a kashe take,haka suka gaji sukayi shirin masallaci suka tafi.
Sinan sai da yayi bacin awanni biyu sannan suka tasheshi,har lokacin bai gama dawowa dai-dai ba,sai suka dura mishi giya nan fa yadad’a rikicewa.Wani abokin Tibishi yakalli Sinan”wannan ba yau za a d’aura mishi aure ba amma yazo nan yashare waje ko auran dole za a mishi? Dammm…zuciyar shi tabuga duk da yana cikin maye.Yata shi yana tangad’i da tam6ele yashiga mota.Yana tafe jama’a na kaucewa da ababan hawansu, yana kuma shan zagi da tsinuwa daga bakin wasu,saboda k’iris yarage yahad’a hatsari mummuna,a haka har ya isa masallacin juma’a wajan d’aurin auren…wasu zafafan hawaye suka zubo mishi”Zigwai tasa ya zubar da mutuncin shi dana gidan su abainan-nasi, kalaman Sudaida suka dawo mishi duk da k’anka’ntar shekarun ta amma tayi hagen nesan da san zuciya yahana shi hangowa…
Zama da madaukin kanwa…wai kai ba ka da wajan zamane sai acikin yan maro(wiwi)?…yatuno da maganar mahaifin shi na wancan makon”Sinan ba girma aganka kana mu’amala da wad’annan k’adangarun barikin… Mun baka tarbiya gwargwadon iyawarmu… Tunatarwa ce kawai…Yamik’e cikin tafasar zuciya “lallai yau za ayi ta tak’are me raba shi da Tibishi da Zigwai sai ALLAH Hamidan yakalle shi ganin yana bud’e kofa”Ina za ka a wannan daren Yaya? Ko kallan shi baiyiba yasa kai yafita.
Tana kwance hankali kwance iskar fanka tana kad’ata.Yadamk’o gashin dokin daya cika kanta tozon rak’umi guda.Zafi yaratsa ta tabud’e idanu cikin gigita,suka kalli juna,sai ta dad’a rikicewa.Yanemi abun duka bai samu ba dan haka yad’auki belt d’in daya gani a gefen gadon, yafara dukan ta ba ji ba gani sai da belt d’in yatsitstsinke amma duk da haka bai hak’ura ba,yafara tattaka sai da yaga ta daina motsi sannan yatsallaketa cikin jini yafita, amma har lokacin bai huce abinda suka mishi ba,wasu jijiyoyi sun fito a gefen kanshi kamar shatin bulala,ran maza ya 6aci iya 6aci.
Adaren yakoma neman Tibishi sai dai duk inda yasan zai ganshi yaje amma cikin rashin sa a bai ganshiba…tabbasss da aun had’u sai wani ya rasa ranshi ko kuma suyi mutuwar kasko.Yakama hanyar gida zuciyar shi a cunkushe, kaci6is sukayi da mahaifin shi da Hamidan za su tafi masallaci sallar asubahi. Sinan yasunkwui da kai ya ga 6acin ran da bai ta6a gani a fuskar mahaifin na suba”yanzu duk abin kunyar dakayi jiya hakan baisa ka kwana a gidaba? Yanuna shi dayatsa” anya Sinan,anya rayuwar gaba za tayi kyauvda albarka idan ba a tsaya an inganta rayuwar da ake ciki a yanzu ba? Anya Sinan kana tuna tsohon banza daga yaron banza yafara? Sinan yayi shiru a ranshi yana nadamar sanin Tibishi da Zigwai a rayuwarshi..Alhaji Kamal yakad’a kai”shikenan sai kaje ka shirya kafito masallaci, yakalleshi “kama rama sallolin jiya daka kwanta wannan baccin asaran?Tsoro yakama shi” shi Sinan yashiga ukun shi wallahi sai yanzu yatuna.Asanyaye yagirgiza kai”yanzu zan rama. Yakalli Hamidan”kaji,Ubangiji yashirye shi. Hamidan ya amsa da sauri amin Baba. Suka tafi masallaci kowanne ranshi ba dad’i.
Yana durk’ushe agaban mahaifiyar shi yana bata hak’urin abinda yafaru amma fau-fau tak’i sauraran shi, tanuna mishi k’ofa”ta shi kabani waje ganin ka yana k’ona min rai,Sinan ka bani kunya…tirrr da wannan halin na ka, albasa batayi halin ruwa ba wallahi. Yayi k’asa da murya “Mama bana shan giya,makirci kawai a ka kulla min…ta tare shi a zafafe” kai karka maidani sakarya,wa zai kulla maka makirci?Makirci da munafurci har yawuce wanda kadad’e kana aikatawa,ko kawai dan dubunka ta cika? Alhaji Kamal yashigo”haba Mamansu idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba,d’an yau ne ka haifeshi baka haifi halin shiba.Takalleshi a rikice “yanzu kana goyon bayan shine,har kana ba shi lasisi?Tad’ora hannayenta aka”oh ni yar mutum biyu” na rantse da ALLAH Alhaji idan yaron nan bai tashi yafitaba to zan d’aga mishi nono…Tabud’e baki da niyar sake magana sai kalaman suka mak’ale saboda 6acin rai.Tasa hannu tashare hawayen daya zubo mata.
Sinan yasake shiga wani tashin hankalin gobarar gemu fiye dana d’azu”lallai ka shiga uku, rayuwarka tana cikin garari tunda har za kasa mahaifiyar ka zubar hawaye saboda mummunan laifin ka. Yanzu wa zai yadda dashi akan baya shan giya? Abu d’aya yasan yana sha a 6oye shine taba sigari,itama ba koda yaushe ba,wazai yadda dashi?Yadafa goshi”ko Alqur’ani d’ungurungum zai had’iye bashi da mafita. Nadama,haushi da bak’in ciki suka baibayeshi, kome yaji yafice mishi a rai.
Alhaji Kamal yadafa shi”tashi katafi d’akin ka.Gwiwa a sage yamik’e.Alhaji Kamal yakalli matar shi “abinda Sinan yayi tabbasss bai kyauta ba,kuma bana goyon bayan shi,to amma wani hanzari ba gudu ba, idan fa yatuba bai kuma aikata hakan ba har abadan duniya,to ALLAH me gafara ne,zai kar6i tuban shi ya yafe mishi tunda bamu yama laifi ba face mahaliccinmu gaba d’aya, dan haka karki tsananta,ke uwa ce addu’arki har kullum ita ake buk’ata, kullum addu’armu da fatanmu ace Ya’yanmu sunyi zarra fiye da duk wasu Ya’ya wajan natsuwa,sanin ya kamata, mutunci da tsantseni,to inga yanzu kin mishi baki? Bazai amfani kan shiba,bazai amfane muba,bazai amfanar da sauran al’umar manzon ALLAH ba,kin 6ata goma biyar bata samuba,baya ba zani kenan…
Yana rik’e da marik’in k’ofar d’akin shi kafin yamurd’a tabud’e jiri yayi awon gaba gaba dashi yifff…yasha k’asa.K:arar fad’uwar tashi megadi yaji.Yayi cikin gidan da sauri yana kiran Alhaji da Hamidan,sun yayyafa mishi ruwa amma shiru kamar an shuka dusa,dan haka suka wuce dashi asibiti.
Tsakanin d’a da uwa sai ALLAH, hankalin mahaifiyar tashi a tashe,takira Hamidan tana tambaya”ya jikin na shi?Yakalli roban k’arin ruwan da aka sa mishi a hankali yake d’iga a cikin siririyar robar yana shiga jijiyarshi zuwa cikin jikinshi”Mama ya samu bacci saboda allurar baccin da aka mishi,likita yace jininshi yayi mugun hawa.To Alhaji fa?Tasake tambayar shi cikin damuwa. Sun fita shi da likita.To Ubangiji yasa kaffarace nima anjima zan shigo. Yagyad’a kai”To Mama sai kin shigo a iso lafiya.Yauwa Hamidan ALLAH yamaka albarka.Amin Mama.