GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tibishi yad’ora hannayen shi aka yana zare idanu”Holy ghost fire!…Inzayadami?(Me yafaru)Tafashe da kuka tana kad’a kai”ina katafi kabarni acikin wannan mawuyacin halin? Na neme ka a waya banji kaba.Yakoma yazauna”sha kuruminki Zigwai wayata nasiyar nayi kud’in mota zuwa Kafanchan kasuwar aladu, na kuma je da k’afar dama and’aukeni lodi mutanan k’asar China sunzo siya, lodin tirela hud’u mukayi,ba k’aramin kud’i nasamu ba,dan haka murabu da Sinan dan naga hak’armu baza ta tadda ruwaba.Me kake nufi? Yazuba mata idanu jikinta duk a farfashe yake”gaskiyar magana tunda Sinan yamiki irin wannan dukan kawo wuk’an to babu wata rana dazaki kuma mishi koda kun rage daga ke sai shi a doron duniya bazai kuma sauraran kiba.Tunda na samu abin yi kishare shi kawai,d’an iska yadaije amma ai munci gari,nima kwana biyu zan kiyayi zuwa cikin gari da duk inda nasan zai ganni,dan na san zai nemeni ruwa a jallo.

Takalleshi amma tunda bai auri Sudaida ba na san zai koma ruwa tsundum. Yamata wani kallon sauna”ke Sinan fa ba sin ki yakw yiba shishshigi da nacinki yasa kika samu kanshi,kuma koda kika samu kan shi ai ba wani d’ad’ashi da k’asa kikayiba,ak’arshe ma bazuwa yayi yaba ki hak’uri akan kuyi hannun rigaba? Yamik’e”nidai buri na ya cika,dama yarinyar ce bana so ta aure shi saboda girman kanta,kin san sannu wannan ta fatar baki bata ta6a cemin ba,duk da tasan nid’in abokin saurayin tane aibtasha ganin mu atare,idan nabari ya aureta to za ta rabamu tunda na san zaiji maganar ta dan yana son ta.

Zigwai takwanta”ai dai munyi biyu babu. Tibishi yakalle ta kisa ranki a inuwa,barinje kasuwa in miki siyayya,yana fita ta kyalkyale da dariya”haba Tibishi ai linzami ya fi k’arfin bakin kaza,kai ka had’ani da Sinan dan yazama saniyar tatsarmu,to mun tatseshi yadda yakamata, yanzu idanu na a bud’e suke ina ganin kowa garauuu ba ka da kud’in dazan aure ka,bari dai mucinye wanda kasamo,za ka nemeni ko sama ko k’asa karasa,garin zan bari dan yamin zafi saboda rashin Sinan, zan tafi wata jahar in bud’e sabuwar rayuwa da sababbin alhazan birni masu aljihu da kud’i ba irin kaba tsami ragowar burkutu giyar k’ok’o da hayakin maro da taba dayaci yacinye ka,sai na sai gida da mota,sannnan zan yi aure…toh maji magani an binne tsohuwa da ranta…

Haka ya yi an sai da gonar rago an sai mishi fura.
Farar dabara shiga rijiya da fura.

10 Jumaada Thani 1441
4 February 2020

We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na goma sha tara.

Kwanaki biyu Sinan yayi a gadon asibiti yasamu sauk’i sai dai likita bai sallame shiba sai zuwa gobe.Yakar6i wayar Hamidan dan ta shi ko ta fad’i ko kuma su Tibishi sun sace ta,yadaddanna lambobin ta sannan ya d’ora lambar a kira.Tad’aga da sallama,wani abu yatsirga ilahirin jikinshi,ta kuma yin sallama jin ba ayi magana ba sai ta katse.Yacire wayar a kunnenshi yana jujjuya ta,idanun shi sun kad’a jawur,tabbasss kukan zuci yakeyi.Yaya Sinan ba a d’aga bane ko matsalar na’urar sadarwa?Yajuya yakalli Hamidan d’in,sai ya gyad’a kai”zan cigaba da gwadawa wata k’ila tashiga.Sai da ya danna kira sannan yace”Hamidan dan ALLAH kaje gida Mama tadama min kunun tamba.Yamik’e yana murmushi”a lallai yau jikin Alhamdulillahi,a had’o da abinci ko?Yagyad’a kai”amma me d’an ruwa-ruwa.

Yana fita yakai wayar kunnenshi,tad’aga da sallama.Yasauke numfash sannan ya amsa sallamar,yakira sunan ta Sudaida…Zuciyoyinsu suka buga,sukayi shiru na wucewar wasu dak’ik’u.Da rawar murya take fad’in”Sinan ya jikin?Ance kana kwance a gadon asibiti,Sinan me yasa kabiye ma son zuciya bayan ka san son zuciya 6acin ta…dama da gaske kura ce lull6e dafatar akuya?Sinan kai masoyina ne, wallahi ban ji dad’in abinda yafaru ba ko kad’an…ALLAH yashirye ka dana… Yatari numfashin ta”na rantse miki da girman ALLAH bana shan giya”ba ka shan giya to ya akayi kasha? Ba fa a wasan kwaikwayo kafito ba.Yakad’a kai, matsalar kenan ba wanda zai gasgata shi”Sudaida na san na rasa ki,to amma duk da haka bazan barki cikin duhu ba,ranar wanka ba a 6oye cibi… Yafara ba ta labarin had’uwarsu da Zigwai wanda shi kanshi yasha mamakin sauk’in halin ta,saboda irin wulak’ancin dayake mata,amma tashanye kullum bata fushi kwantar da kai take mishi na gasken-gaske da haka har taja ra’ayin shi yafad’a tark’onta.

Cikin kuka tace”ai na fad’a maka dabi’a tana na so,maganin kar ayi to tun farko kar a fara,dan shaid’an baya raina k’ofa.Sinan ina maka fatan alheri a rayuwa,dan ALLAH kacanja abokai da mutanan kirki.Nagode Sudaida,kema ina miki fatan alheri da samun natsuwa a gidan auren ki.Sudaida sarauniyar Julaibib.Yagoge lambar ta daga cikin wayar sannan ya ajiye,yana jin ranshi ba dad’i sunyi sabo na ban mamaki da Sudaida tun tana yar k’aramar yarinya…Lallai sabo turken wawa.

Julaibib daya jingina da k’ofar d’akin-shak’atawar yak’arasa shiga yazauna,ganin shi baisa ta daina kukan ba.Yakalleta cikin kulawa”kukan na menene Sudaida?Ai k’addara ta riga fata”rayuwar mu ba a hannu take ba,ALLAH ne yake tafiyar mana da ita,ta duk yadda ya so,shiyasa so ba samu bane,haka kuma samu ba so bane a wasu lokutan;yasa hannayen shi yagewayeta yana mata wani salo a hankali,yana kuma fad’a mata wasu kalamai sai ga shi tasa hannu ta share hawayen ta kuma yi shiru,tana k’ar6an sak’onnin dayake bata a ilahirin gangar jiki da sararin zuciya,wucewar wasu dak’ik’u sannan yad’ago fuskar ta suka kalli juna tayi saurin kauda kai”idan kunne na sun jiyo min dai-dai a cikin kalamanki naji kince shaid’an baya raina k’ofa ko? Ba baka sai kunne…jikin ta ya mutu murusss kai kawai tagyad’a.Yamik’a mata hannun damar shi “bani wayar ki.Tasa mishi a tafin hannun,yasa ta aljihu…

Sudaida…Yakira tatad’ago tad’an kalleshi. Kin san me yasa nakar6i wayarki?Uh uh.Yasauke numfashi”to na kar6i wayar ki saboda ba na so wata mu’amala tacigaba da kasancewa a tsakanin ku,yanzu ke matar aure ce,shi kuma wani k’ato ne daba muharraminki ba,ba dangin Iya bare na Baba;shi kuma shaid’an baya raina k’ofa.Yabata wata sabuwa galleliyar waya da layi sabo a ciki.Tasa hannu biyu ta kar6a”Yaya Julaibib nagode da da tunatarwanka.

Bayan sallar isha’i yashigo”Ina amaryar? Ta shaida muryar ko da acikin magagin bacci take, tafito sanye da hijab d’in data idar da sallah “sannun ku da zuwa…Yayi murmushi”yauwa amarya sha gud’a.Ya ba ta kunya ba kad’an ba,ta kuma ji abun banbarak’wai namiji da suna kande, wai Yaya Musaddiq da tsokanar ta,dama shi da Yaya Adnan sam ba shak’uwa a tsakanin su, wannan sauk’in halin sai Yaya Aminu.

Cikin girmamawa ta gaishe shi tare da tambayar ya Yaya Safiyya?Yagyara zama”ai itace ma ta ai ko ni,wai tana gaishe ki,kin san yanayin na ta,tafiyar wahala take mata amma dai za ta k’ok’arta tazo.

Taje takawo musu abinci Musaddiq yamik’e”a ah wallahi kuci kayan ku.Julaibib yazuba mishi idanu saboda me? Yad’an daki kafad’ar shi”ni kuma nawa da yake jirana a gida inyi Yaya dashi?Yamik’a mishi hannu sukayi musafaha.Suna tsaye a bakin k’ofa sukayi k’us-k’us d’insu sukayi dariya suka tafa.Tabisu da kallo”maza ma sun iya tsegumi?Tayi yar dariya wai itace ba su so taji kenan”Yaya Musaddiq mukwana lafiya.To Sudaida ALLAH yatashe mu lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button