GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana kwance cikin damuwa saboda fad’an da Julaibib yarufe ta dashi kamar zai ba ta na jaki,sannan ya hanata tofa albarkacin bakin ta, na ganin da yama k’anwar Sinan a gidan; kila zaton shi Sinan ne ya aiko ta tunda zai kira lambarta yajita a kashe,ita kuma Maman suce tabata turaran wuta da su humra kala-kala takawo mata,dama ta siya ta ajiye idan tazo gidan saita ba ta toh kuma ga yadda al’mura suka kasance.

Yanuna ta da yatsa idanun shi sun kad’a jawur”idan na kuma ganin wata ko wani a cikin gidan nan daya danganci Sinan na rantse miki da ALLAH abinda zan miki har ki mutu baza ki manta shi ba…Idanun ta suka ciko da kwallah Yaya d’ans…ke! Nace ki rufe min baki ko?Yayi d’as d’as d’as da yan yatsun shi”baki sanni bane,yaja dogon tsaki yawuce d’akin shi.

Tasauke numfashi da ajiyar zuciya,tasa hannu tana share hawaye,tabi k’ofar da ake k’wank’wasawa da wani malalacin kallo,ta maida kanta jikin matashi tana dad’a gyara kwanciya.Aka cigaba da k’wank’wasa k’ofar,dole tamik’e cikin fushi tana jan tsaki a ranta tana mita”na ci dambun kuturu.Tasa hannu tabud’e k’ofar caraf idanun su yahad’u,ta gallama Sudaida harara. Sudaida tayi kamar ba ta gani ba,tayi d’an tsallen murna fuskar ta cike da d’okin ganin ta tafad’a jikinta”oyoyo Hajiyarmu sannu da zuwa…suka shige d’akin-shak’atawar,Hajiya ta ture ta”ke gafara can karki 6alla ni,tazauna a k’asa tana dafe k’afafu da alama ciwon k’afar yana son motsawa.

Da sauri Sudaida tad’auko man zafi ta d’urk’usa a gabanta tana murza mata a k’afafun tana maimaita”sannu da zuwa Hajiyar mu gaskiyar magana naji dad’in ganinki ba kad’an ba. Hajiya tasake galla mata harara”amma shine kika barni a waje ina ta k’wank’wasa k’ofa?Tayi yar dariya”kai Hajiya gidan amarya fa kikazo ni k’wank’wasa k’ofar kine ma yatashe ni daga bacci.Hajiya takalli agogon bangon dake d’akin sha d’aya saura minti goma na safiya”Toh ALLAH ko yasauwak’e da wannan baccin asaran. Tagirgiza kai”ba amin ba,ai lokacin abu ayi shi, amarci ai ba k’arya bane,ba kuma abinda ba ya sawa.Hajiya tazuba mata idanu cikin kallan nazari”amarcin ne yadad’a k’arar dake kamar bushashshen takand’a?Ke ko cikar d’akin bakiyi ba.Takai hannu tashafa wuyanta”sharri dai ba kyau Hajiya ni ba bushewar danayi wallahi,toh so kike kiga na zama ta shi da nishi?Tamata dak’uwa”kar6i nan aiko Iyayan ki na fi k’arfin in musu sharri bare ke karankad’a miya.Tad’an turo baki gaba”ai baza ki musu sharri ba tunda Ya’yan kine kina son su,nice dai ba kyau so.Hajiya takad’a kai kawai.

Ina Julaibibi ne rabona dashi tun shekaran jiya da daddare.Haushin shi yamamayi zuciyarta,to amma Hajiya babbace ko yaya tanuna wani yanayi za ta iya gano ta bare kuma yadda ta tsare ta da idanu.Tamik’e tana rufe man zafin”ke Hajiya ai yanzu ba da bane dazai dinga zuwa gidan ki yana share waje,ni kuma dawa zai barni? Hajiya ta tafa hannaye tana sallallami”ba shakka rasa kunya 6aren tanka…lallai wuyan ki ya isa yanka.

Sudaida tawuce tana dariya,ta kwana biyu bata shiga d’akin ba,k’amshin arabi’an perfume da k’amshin turaren d’aki ya gauraye sai yaba da wani irin nau’in k’amshi me sanyin dad’i wajen shak’a,carpet d’in d’akin kore da ratsin ruwan madara dawasu kyalli-kyalli masu d’aukar idanu,hakama labulayen d’akin ruwan madara da ratsin filawar rose yan shara-shara,sassayar iskar da take shigowa d’akin ta tagogin da suke a bud’e suna kad’a labulayen suna rangaji saboda rashin nauyin su,ya canja gadon daga inda tasani zuwa d’aya bangaren, wardrobe ma yacanja daga zuwa bangaren yamma,shoe-rack(ma’ajiyar takalma) cike tam da takalma mafi yawansu farare ne,kuma masu rufi(sau ciki)

Yad’ago yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da yake ba ta haushi,yamaida kanshi ga tarin littafan daya barbaza a saman tebur,yana kuma yin rubutu a na’ura me k’wak’walwa da alama wasu abubuwan yake shigarwa”lafiya za kizo ki tsaya min akai bayan kingani ganin idanun ki aiki nakeyi.Wulak’ancin d’an Sarai har yakai haka?Ta tambayi kanta,zuciyar ta tayi rauni idanun ta suka kawo ruwa amma bata bari hawayen sun zubo ba,ta kad’a kai”ba kome dama saboda ka ma ake cin k’asa,tasaki marik’in k’ofar”Hajiya ce take magana.Suna had’a idanu yagalla mata harara “dama ai duk wanda kika ga ya ci kaza to shine da ita.Tayi kamar bataji abinda yafad’a ba.

Yasauke numfashi zuciyar shi ba dad’i ganin damuwar data shiga,ko kukan d’azu datasha kuka har tak’oshi yaji ba dad’i,to amma dole yayima tufkar hanci,kar garin kallon ruwa k’wad’o yamishi k’afa,ita da Sinan ai sun so juna, yau da gobe kuma bata bar kome ba,shaid’an baya raina k’ofa, dama ba abinda yake so sama da 6ata tsakanin ma’aurata,toh dole sai ya toshe duk wata kafa da yasan alak’a zata had’ata da Sinan dan yatserar dasu da auransu daga fad’awa halaka.Wani lallausan murmushi yasu6uce mishi “humm Sudaida za tafahimce shi,shi masoyin tane da babu kamar shi a doron duniya,shi da ita mutu karaba takalmin kaza,har lokacin da gangar jiki zai daina numfashi, rai yatafiii…

Yazauna suka gaisa da Hajiya.Tanuna shi da yatsa”kai Julaibibi kazama jarumi dan a haka nasan ka, karka biye ma wannan malalaciyar matar taka tamaida kai rago, ace kazauna kana sharar bacci har hantsi yadubi ludayi?Yashafa kwantaccen bak’in gashin kanshi yana d’an murmushi”Hajiya wane ni da wannan aikin;ai sai manya gatan wasa,amarya sha gud’a suka kalli juna shi da Sudaida tad’an harareshi tana turo ba ki gaba.

Wasu muhimman bayanai nake ta shigarwa ashafin mu na yanar gizo.Tagyad’a kai “Toh Ubangiji yayi jagora.Sunata hira da Hajiya cikin jin dad’i a wanta d’aya a gidan sannan takalle su”to ai na gaishe ku,barin tashi inje gidan Musaddiq jiya Safiyya bataji dad’i ba,wannan girman ciki ko yan hud’une a ciki iya ka kenan, ALLAH dai yaraba lafiya,suka amsa da amin. Julaibib yafita k’ofar gida inda ake sallama dashi.

Hajiya takalleta cikin natsuwa”wato kink’i tsayawa ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddarar Ubangiji ko?Tasunkwui da kai.Hajiya tacigaba shi aure dakike ganin shi ai ALLAH ne yake had’a shi ba mutum d’an Adam ba;ko shi Sinan ai ya dangana dan yazo har gida ya fed’emin biri har bindi, ban kuma kullace shi ba,na san shi mutumin kirkine,sharrin shaid’an dana zuciya ne suka rud’e shi,tanuna ta da yatsa”tun wuri ki saki ranki ki rungumi auren ki dan shine gatan ki na d’iya mace,ga sauran yan’uwanki can kowacce tayi sharrr gwanin ban sha’awa da kyan gani,ke kuma kinanan jiya i yau,ke da Julaibibi ai kun zama k’arfe da mayen k’arfe.Tayi shiru kawai a ranta tana mita”ai Yaya d’ansarai yakamata ajama kunne tunda shine baya son ta,auren dole aka mishi a tunanin ta”rashin sani karen gwauro yakori bazawara.Sukayi sallama tad’an ta ka mata zuwa harabar gidan.Tare suka koma ciki da Julaibib..Ke Sudaida zo nan…tayi kunnen uwar shegu tashige wanka.Yakad’a kai yana yar dariya”Sudaida k’uruci dangin hauka…

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar talata,tana had’a lemun abarba da kashu ta toshe kunnuwanta da earphone,tana sanye da riga da zani na atamfa ruwan makuba da ratsin filawoyi manya da k’anana masu ruwan hoda da baki tayi wani irin d’auri na burgewa gashin kanta ta tubke shi da k’aton ribbon ruwan makuba,ta juya za ta d’auki siga caraf idanun su yahad’u, yana tsaye a k’ofa yanad’e hannayen shi a kirji,tad’auke kai cikin basarwa kamar bata ganshi ba,dan har yanzu a wuya take dashi, ba Yaya Julaibib d’in da tasani a da to yanzu ba shi bane,gaba d’aya ya canja Hali,d’azu-d’azu yagama yarfa mata ruwan bala’i wai yaran Kawun su yazo,ita kuma ta manta bata sa hijab ba tazauna suna shan hira da dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button