
Tagama aikinta tazo za ta wuce yatare hanyar yana kallanta cikin natsuwa kamar wani abu bai faruba,ko da yake shi tsakani da ALLAH yamata nasiha irin haka bai dace ba dan kayan sun kamata kome na ta ya bayyana,itace dai ta maida cibi yazama k’ari.Na yi sallama baki amsaba,na tambayeki abinci na nan ma kinyi shiru lafiya kuwa?Taturo baki gaba”shiruma amsace. Sudaida ba magana nake miki ba? Nan ma tayi shiru.Me yasa kike jamin zarene kin san halina fa. Tamishi wani kallo me kama da harara,cikin fushi tace”to sai me?Me tsoron ta mutu ai shi yake maho.Yayi jimmm…Yana cigaba da kallanta cikin nazari,wucewar wasu dak’ik’u sai yajuya…tabi bayan shi da harara”ALLAH raka ta ki gona…Yaja yatsaya zai juyo sai kuma yafasa yayi tafiyar shi kamar baiji abinda fafad’a ba.
Tana azkar d’in yammaci bayan ta idar da sallar la’asar tana tunanin a ina Yaya d’ansarai yatsaya bai dawo gida yaci abincin rana kamar yadda yasaba ba,duk da ba wani d’asawa suke yi ba,…shiru-shiru har bayan sallar isha’i haushin shi yakamata ita kuma ta k’i kiran shi a waya taji me yatsaya yi taje tayi kwanciyarta tana zencen zuci”wato ko da, da take son shi take kukan rabuwa dashi,to shi dai ba ta ita yake yiba tunda gashi suna zaman aure yana mata yadda yaga dama, tadad’a gyara rufa tana k’wafa aikin banza kawai tura agwagwa cikin ruwa,jikinta yayi sanyi “lallai san maso wani k’oshin wahala, har bacci yayi awon gaba da ita bataji shigowar shiba.
Da safe tana tsaye a jikin taga ta zubama motar Julaibib idanu,tun jiya bai fita da ita ba,sanda yadawo gidan tariga tayi bacci kuma bai tashe taba, anyama ya dawo gidan? Dan yadda ta ajiye mishi abincin dare haka taba almajiri dasafe, bai ta6a ba,har d’akin shi taleka yanzu kuma ba ya nan,to ina yatafine?Wata kila tun daga sallar asubahi yawuce gidan Inna ko gidan Hajiya,ta lumshe idanun ta tana mamakin canjin halin Yaya d’an Sarai.
A hankali ake k’wank’wasa k’ofar. Tasauke numfashi,ranta ya mata dad’i Julaibib ne dan haka yake buga k’ofa na natsuwa.Tabud’e cikin d’okin san ganin shi ta ma manta da rashin jituwar su.Suka kalli juna yamata murmushi, murna ta koma ciki,zuciyarta tayi rauni,kwallah yacika idanun ta,ta rasa hujjar hakan wallahi, yarage fara’ar fuskar shi,yagyad’a kai labarin zuciya a tambayi fuska”ba kya maraba dani ko?Sai kawai yajuya, dasauri taruk’o gefen rigarshi tabaya”wallahi ba haka bane,yajuyo fuskar shi ba walwala”toh yayane?Taja da baya tabashi hanya dan yashiga,yakad’a kai”bazan shiga ba.
Tamarairaice”Yaya Aminu dan girman ALLAH kayi hak’uri kashigo,wallahi na yi kewarka ne,tunda aka kawo ni Lillahi warasulihi sai yau d’in nan kazo duk yadda muke da kai..tayi furucin da yanayin shagwa6a.Yashiga d’akin-shak’awar yazauna a kujera”to banda abinki Sudaida yaushe zan ta zirga-zirga a gidanki? Tashige d’akin-girki dasauri takawo mishi kunun tamba yasha madara “Yaya Aminu ga mutumin.Yabud’e kofin yagani”to nagode Sudaida,kad’an yasha saboda ya riga ya k’oshi,a gida ma yana da wanda bai shaba na wajan Innan d’ansarai.
Sun d’an ta6a hira sannan yace mata kishiga d’akin mijinki ki d’auko min mukullin motarshi zan kai ta gyara, ba yadda banyi dashi akan yad’auki tawa yayi tafiyar ba amma yak’i,sai tasha naraka shi yashiga motar haya,kuma a ranar yanada jarabawa…har tabashi mukullin yatafi hankalinta yayi mugun tashi”yanzu d’ansarai zaiyi tafiya yabar garin amma ko sallama bazai mata ba? Itako wace irin kiyayya yake mata haka? Ai ko kafin suyi aure yana mata sallama bare yanzu da take cikin gidan shi a k’ark’ashin igiyar aure.Tayi k’wafa”ai ba lallai ba tilas,yaje yadawo tana sauraren shi da duk ma wacce zai zo.
Kwanakinshi biyu da tafiya,shi bai kira ba, itama bata kira ba,a kwana na uku ne dai takasa daurewa dan abin tsoro yafara bata…sai taga bata kyau taba itace a k’asa dan haka tasauke …rawanin tsiyar tanemeshi.
“Lafiya?
Tamabayar daya mata kenan daya d’aga wayar,bai kuma jira amsar taba yakashetacire wayar daga kunnenta cike da mad’aukakin mamaki” wai me wannan mutumin yake nufi ne? Haushi da damuwa suka kamata.. Tajafa wayar a kujera ko tunanin taci screen bata yiba, tawuce d’akin-girki tasauke dafadukan taliyan data dafa, tazuba a faranti takoma d’akin-shak’ata dan taci, sai dai tanata kallan taliyar har yayi sanyi baza ta iya ciba,ai ko almajiri yana kwala barar”allazi wahidin”tabud’e k’ofa tajuye mishi duka a robar shi.Yakar6a da rawar hannu data murya.
“Iya ALLAH yabi yaki,ya yaye miki matsalar rayuwa.Tabishi da kallo tana fad’in”amin d’an Malam.Sauri yakeyi kamar zai ta shi sama dan kada sauran almajirai su farga da abinci a kwanon shi su rufar mishi, gashi kuma wasu gardawa ne guda biyu suka sashi ya barato musu abinci,idan bai kai musu ba ba k’aramin na jaki zai shaba,kuma ba shi da mataimaki sai ALLAH.
Abu kamar wasa k’aramar magana ta zama babba,yau makon Jukaibib d’aya kuma koda wasa bai kira taba…Abun yak’ara jefata a kokwanto da fargaba”to lafiya kuwa?Gashi ba wanda za ta tambaya,haba ai da kunya sai a mata tirrr…wasu kuma su mata dariya su d’auketa sakarya ita da mijin ta amma bata san a halin da yake ba?Taja tsaki”to shi d’in ya kira tane?Ko ko dai idan akak’i jininka ko ruwa kafad’a sai ace ka tada k’ura?Wucewar wasu dak’ik’u tana zaune tunani barkatai ya cika k’wak’walwarta ta rasa na za6a tayi shi da gasken-gaske,ta tsuke baki kamar za ta rufe shi tana fitar da iska,gaskiyar magana kawai ta kasa samun natsuwar zuciya dan haka tak’arya 6illenta tad’auki waya takira shi.
Bugu d’aya yad’aga kamar dama jiran ta yakeyi.Yayi sallama muryar shi a dake.Ta amsa sallamar tana gaishe shi.Asik’e ya amsa”lafiya…Gwiwoyinta suka sage,sharrr… Sharrr…hawaye yafara sintiri a fuskarta shashshek’ar kukan na ta na fitowa a hankali. Yatare ta muryar shi ba sassauci”ke! Dakata, dakata haka malama! Ni na ta6a fad’a miki ina sha’awar jin sautin kukan ki,bare yanzu da kike jinyi ki kirani?Yaya Jul…Kittt…Yakatse wayar. Haushi da mamaki suka rufe ta,ranta in yayi dubu ya6aci “Lallai ma d’ansarai…To ko da aka ba ka ni, idan ban maka ba sai ka sallame ni…tacigaba da kuka.
Julaibib yacire wayar a kunnen shi yana murmushi”kulawa yabawa ce,ya kamata yakoma gida haka dama kullum idan sunyi waya da Hajiya sai ta mishi ciwon bakin yaje ya share waje kamar mara Iyali.Baba ma jiya sai da yace”Malam d’ansarai ka k’ok’arta duk lokacin daka samu dama kazo gida wajan Iyalin ka kaji ko?Ya amsa da ladabi”eh Baba Insha-ALLAH. Yakulle k’ofar d’akin shi dan tafiya masallaci, masallatai mabambanta sunata kiraye-kirayen sallar azahar.
Da yammacin ranar talata rana ta tafi tana shirin fad’uwa,magriba na kunno kai tana zaune a tana nazarin littafan Islamiyyarta,motsin shigowar Julaibib taji yana shiga da kayayyaji d’akin-girki,sai da yagama yashiga d’akin-shak’tawar da wata babbar leda,a gajiye ya zauna yana kallanta yasa hannayen shi yana 6alle botirin gaban rigar shi,bata wani nuna d’okin ganin shi ba,fuskar ta ba yabo ba fallasa tace mishi”sannu da zuwa.Yagyad’a kai”yauwa yana cigaba da nazarin ta.
Sudaida…Yakira ta.
Bata d’ago ta kalle shi ba ta amsa “na’am.Duk sukayi shiru,ta sunkwui da kai amma ta kasa cigaba da nazarin kallan littafin kawai takeyi amma baza tace ga abinda aka rubuta ba. Ana fara kiran sallar magriba yafita.