
Tana kwance bayan ta idar da sallar Isha’i,zuwa wannan lokacin zuciyar ta ta gama tafarfasa ruwan ciki ya k’one k’urmus har ya kama da wuta,zuciyarta tayi gobara saboda takaicin d’ansarai autan Inna;tayi kwafa taja dogon tsaki tun wajejen k’arfe goma sha d’aya da rabi na safiya Hanifa tazo tafad’a mata”Baba d’ansarai ya dawo,har ya bata Inibi da dabino me yawa, tashigo ma da Inibi tana ci,wani sanyin dad’i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyarta,duk da bawani d’asawa suke yiba,ta tambayeta to yana ina? Hanifa tace yana gidan su”Kawu Adnan shi da Babana(Musaddiq)
Nan da nan ta dad’a gyara ko ina tayi wanka tayi kwalliya tafeshe jiki da turare,ta turara d’akunanan gidan da turarukan d’aki ko ina yad’auki k’amshi da kyalli;to amma saboda tsiya d’inkin ludayi wai sai gab da magriba yaga damar shigowa gidan,kuma ko dak’ik’a goma cikakku bai yiba yasake ficewa,bai kuma sake shigowa ba sai yanzu awa biyu da idar da sallar Isha’i. Tamaida idanun ta tarufe kamar me bacci.
Yatsuguna yana tashin ta,dak’yar ta tashi tazauna tana turo baki gaba,yakoma kujera yazauna”zan samu abinci?Takauda kai”banyi girki ba,dan wanda tadafa mishi da rana,bayan la’asar tajuye ma almajiri.To ko shayi ne had’a min yunwa nake ji.Batayi magana ba dan dai ba yadda za tayine da baza ta had’a ba,tad’an ja tsaki”aikin banza harara a duhu,shi baya gajiya da shan shayi, shayin ma daba a sa madara sai kace jikan buzaye,tahad’a takawo mishi lokacin ya shiga wanka,yafito cikin fararen kaya na shan iska, botiran gaban rigar a bud’e suke gargasar shi akwance lufff…bak’ink’irin da shek’i.
Yad’auki shayin da bismillah yad’an kur6a sai yakalleta”me yasa kika samin siga bayan ga zuma?Tad’an harare shi”ni siga nake sawa a shayi,ai ba mutuwa za kayi ba.Yayi murmushi yana kad’a kai”k’uruci dangin hauka ga abinda aka tambaya ga amsar da take bayarwa “Sudaida mutan Matsirga suna gaishe ki,suna nan zuwa.Shiru ma amsa ce.Yabita da kallo”ke wai lafiyar ki kuwa? Ko dawowar tawace baki so?Ni fa shi yasa bana san zuwa,tunda raina ne yake 6aci.Tamishi wani kallo me kama da harara”na rantse da girman ALLAH ni…sauran kalaman suka mak’ale saboda haushin daya mamaye ta,takaicin ta ace yazo garin tun farar safiya,bai shigo yaganta ba,amma ya tafi Matsirga ba dangin Iya bare na Baba,dangin-dangirere wata tsohuwar budurwar shi data dad’e a kushewa,itace ‘yar gwal har yanzu itace a sararin zuciyarta shi.Cikin fushi ta kwashi littafai da daddumar data yi sallah fuuu… Tawuce d’akin baccin ta.
Ya ajiye kofin shayin a saman tebur yayi shiru da yanayin damuwa”me yasa Sudaida take mishi haka?Ai itace k’arfin dawowar shi a yau,amma ta watsa mishi k’asa a cikin idanu;duk yadda ya d’okantu da ita a yau d’in amma da ta shi mazantakar tamotsa sai ya danne zuciyar shi bai bi ta d’aki kamar yadda zuciyar take raya mishi ba,ya kwaso wasu littafi yana nazarin su.
Tacire wayar ta a caji tahaye gado sannan ta kunna data,sak’onni suka dinga shigowa bata ta6a wayar ba har sai da suka gama shigowa sannan ta fara duba Status d’in su Khausar,haushi yadad’a kamata,ganin kowacce tana cikin shauk’in k’auna ita da masoyin ta…A status d’in a’isha ne taga Hashim ya zage yana daka shakwara a turmi tana ce mishi baiyi laushi ba sai ya k’ara dakawa,shi kuma yana fad’in nagaji fa gaskiya..ga wanda suke cin sakwaran da miyar Ogu suna dariya.
Ga na Khausar nan ita da Huzaifa sunyi wani irin kyau na ban mamaki gaba d’ayan su sun canja,ta d’ora ha6arta a kafad’arshi suna dariya, d’ayan kuma wasu irin kalamai ne na tsananin k’auna ta rubuta shi ga hoton zuciya an gewaye ta da adon filawar Damask rose-flower.
Na maryam kuma hummm sallah ba a magana,ta yi mugun mamakin abinda ta d’ora a irin yanayin zaman da tayi da kuma kayan jikin ta,a k’asa ta rubuta”My Snuggle…I miss you deadly… Tabbb…ai bata gama kallo ba tabari tana zagin ta “abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tayita kira layin ta a kashe, duk da ta san taza6i wad’anda za su ga Status d’in na tane,amma ita sai hakan bai gamshe taba gaskiya.
“Nasmat tamata magana”
Hummm…Amaryar autan Inna kuna shan sharafin ku fa..
Sudaida ta6ata fuska”a ah abinda yafi sharafi muke sha.
Nasmat takyalkyale da dariya…nima naga alama shi yasa sai jefi-jefi a ke ganin ki online…har yanzu kanwa bata kar tsamin bane k’wannafin yakwanta?
Sudaida taja dogon tsaki”ke dai kika sani da neman magana ni sai da safe…kawai ta kashe data ta kwanta;bata duba sak’o ko guda d’aya ba,tunani barkatai ya cika k’wak’walwarta “hummm yunwar ya tashi”taja dogon tsaki wallahi ai ba lallai ba tilas.
Washe gari ma da sassafe yabar gidan wai suna da taro a Zango Urban kamar tace yasiyo mata d’anbagalaje amma ta shareshi,ta d’auki wayar ta takira Yaya Aminu tana tambayar shi”kaima kana Zangon ne?Eh Sudaida.Dan ALLAH Yaya Aminu d’anbagalaje nake so amma me taushi.Kai kai kai Sudaida ai gwamma me k’arfin kinga za ki motsa muk’amuk’inki da dasashi ko kuwa? Tad’an marairaice”Yaya Aminu ni dai me taushi.To zan siyo miki Insha-ALLAH. Yauwa Yaya Aminu wallahi, shi yasa nake son ka ALLAH yabarka da Sidddiqa tazama sarauniyar ka.Amin Sudaida. Sukayi dariya.
Abubuwa suke ta maimaituwa na rashin fahimtar juna a tsakanin su,musamman Sudaida da take d’aukar fushi a abinda bai kamata ayi fushin ba,abun ya k’i ci ya k’i cinyewa kamar cin k’wan makauniya.Yauma tunda yatafi masallaci sallar asubahi bai dawo gidan ba.A hankali taji ana k’wank’wansa k’ofar gidan ta san shine, dan taji tsayuwar motar shi.Tatashi tabud’e takoma tayi kwanciyar ta.Yatsaya a tsakiyar d’akin hannayen shi nad’e a k’irji.
“Sudaida bak’in Matsirga sun zo.
Dammm…zuciyar ta tabuga da k’arfin gaske.Tafara zancen zuci”Kutumelesi wato zuwa yayi dakan shi yad’auko su?Su suna da mutunci da kima a idanun shi,ya kuma damu dasu amma ita ko oho ko?
Tajijjiga kai wani…kumallon mata yata so mata har wuya,amma ba tayi ko kawa da zuciyar ta bata amayo shiba.Tad’ago takalleshi”Oh sun zo?Tagyad’a kai”toh sannun su da zuwa. Yabita da kallan nazari ganin tana dad’a gyara kwanciya har da jan bargo ta lullu6a”ke wai menene haka?Kitashi kije ku gaisa mana. Tayamutsa fuska sannan tajuya mishi k’eya “gaskiya ni har yanzu bacci ne a cikin idanu na kum…Yatari numfashin ta “Innar su Bilkisu ce fa?
Furucin shi yamata sukar wuk’a a k’ahon zuciya wallahi ta kasa daurewa,idanun ta suka kawo ruwa”shikenan kuma dan kayi bak’i bazan yi bacci ba,bayan idanu na har wani zafi da yaji-yaji suke min saboda rashin baccin?Ni fa na rantse da girman ALLAH bazan iya wannan zaman ba,tunda baka d’auke ni wata tsiya ba,toh ba dani ba wannan takuran,ko dan kaga gidan kane? Tagalla mishi harara”an hak’ura ana shan kukar k’azama kuma dole sai tayi tsada?Wallahi sai a hak’ura tunda ba mutuwa za ayi ba ehemmm.
Suka zubama juna idanu cikin kallan-kallo nawucewar wasu dak’ik’u kowa zuciyar shi ba dad’i. Sudaida tana jiran martani ne tayi abinda idan ta tafasa za ta k’one,sai shi kuma yamata shiru,dan yadda ta6ata mishi rai idan yatsaya toh aika-aika za ayi,sai kawai yagyad’a kai”ki cigaba da abinda kike yi,amma fa kowa yaci ladan kuturu sai ya mishi aski,wanda ya girmama iyayen wani to bana kowa ya girmama ba sai na shi.Yakai hannu yak’ara mata gudun fankar “shikenan kiyi baccin ki.Yajuya yafita fuskar shi ba walwala,labarin zuciya a tambayi fuska.