
Tad’aga murya”eh yanzu kuwa zanyi baccin.Sai kuma tamik’e jikin ta yayi sanyi gaskiyar magana bai kamata tayi haka ba”ai bak’on ka annabinka, wanda yadamu dakai shine zai zo inda kake to bai kamata kanuna mishi halin-ko-inkula ba”bak’in karen masoyinka ai yafi farin ragon mak’iyinka.
Yayi jimmm…nawucewar wasu dak’ik’u a bak’in k’ofa,Sudaida ta k’i fitowa ta musu sannu da zuwa to me zai fad’ama Inna?Sai yajuya zuwa d’akin-girki yad’ibo musu kofuna da lemun biyar a raye da ruwa har zuwa lokacin bai samo amsar dazai ba Inna ba,yahura iskar bakin shi”lallai Sudaida zata gane da gero ake koko yacigaba da tafiya,zai fad’a mata Sudaida bata nan.
Yamurd’a k’ofar d’akin-shak’atawar da sallama yashiga,sai dai abun mamaki Baturiya da suna manga Sudaida yagani durk’ushe a gaban Inna tana gaisheta cikin girmamawa”kun zo lafiya? Yasu Malam da sauran mutan gidan?A Alhamdulillahi lafiya lau,duk suna gaishe ki,sannu mungode.Daganin yadda Inna take amsawa itama taji dad’in shimfid’ar fuskar da Sudaida tamata wacce tafi ta tabarma.Tamik’ama Bello hannu sukayi musafaha “d’an kanina kaga dana iya yaren fulatanci toh da yau duk hirarmu da fillanci za muyi shi. Bello yad’an bud’e idanu”kai dama baki iya ba?To kisa Yaya d’ansarai ya dinga koya miki mana,kinga lokacin da Adda batayi wannan tafiya me nisan nan ba to idan yazo da fillanci suke magana suyi ta dariya,ranan nan ma yace mata wai…Kai Bello Inna ta tari numfashin shi’ba na hana ka fad’an abinda ba a tambaye kaba? Sai yayi shiru.
Da sauri Sudaida tamik’e ta kar6i kayan ta zuzzuba musu lemon a kofuna sanna tashiga d’akin-girki ta d’auko musu abincin data dafa tajuye a food-flask tana mita a ranta”kai ALLAH yasuwake da halin d’ansarai yanzu da suna da yawa dole sai tayi wani sabon girkin. Inna tasha lemon amma tak’i cin abincin.Sudaida ta karyar da kai gefen dama”haba Innarmu idan baki ciba ai baza muji dad’i ba,ni ‘ya ce awajen ki,uwa kuma ai bazata k’i cin abincin ‘yar taba ko da tak’oshi za tasa albarka,Inna idan bakiciba sai inga kamar da wata a k’asa a yadda muka d’aukeki ni da Yaya d’ansarai ke ba haka kika d’auke muba…suna had’a idanu tad’an harare shi sannan ta kauda kai. Inna tace”ba haka babe Sudaida, karki kuma furta irin wad’annan kalaman,ni na d’aukeku kamar Ya’yan dana haifa,ALLAH yamuku albarka,yabaku zuri’a d’ayyiba. Dole ta d’auki cokali tayi bismillah sannan tad’an ci kad’an, Bello kuma yace shi baya shi dan bayajin yunwa yanata cin meatpie da su Inibin da Julaibib ya bashi.Da za su tafi Sudaida tabata turmin atamfa,taba da Shadda yadi goma da turare wai aba Malam tana kuma gaishe shi,tak’aro ma Bello meatpie dayawa dan jiya tayi kuma ba wanda yazo gidan shiyasa bai k’areba.Yakalleta yana ta murmushi “kince za ki Matsirga?Tagyad’a kai”eh Bello zamu zo Insha-ALLAH.Yamik’a mata hannu sukayi musafaha “Adda Sudaida sai kinzo zan tatso miki madarar saniyata da Malam yabani karsana guda biyu nawa ni kad’ai ina kaisu kiwo har rafin Matsirga nake kaisu susha ruwa sai mudawo gida,sukayi dariya.Sannan ta rakasu haraban gidan suka shiga mota.Sudaida tasunkuyo tana maimata” ALLAH yatsare Innarmu,ALLAH yakaiku gida lafiya.Amin Sudaida, Inna tadinga shi mata albarka,tasa gefen hijab d’inta tana share ruwan hawaye,yau mutuwar Bilkisu ta dawo mata sabuwa.Suka d’aga hannu suna ma juna adabo.Julaibib yaja motar cikin karsashi,yana murmushi jin dad’i abinda tama Innar Bilkisu ya kankare duk wani bak’in laifi data mishi dayake jin haushi…wata irin k’auna da kewar ta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar shi.
Yadawo yatar da jarkokin kindirmo dana manshanu da sauran tsarabar da Inna takawo a inda yatafi yabar su.Yatsaya a gabanta hannayen shi suna cikin aljihun doguwar farar rigar shi,yakalleta cikin natsuwa”Sudaida ya baki adana suba?Saboda bani da buk’atar sune. Tagama wanke-wanken da take yi tamik’e tana yarfar da ruwan hannayen ta,tawani tsuke baki kamar me shirin yin fito.Yagyad’a kai”toh bani abinci sauri nake yi zan tafi Samaru.Cikin fushi tace”na rantse da girman ALLAH tun kafin wankin hula yakaika ga dare kasan inda za kaje kaci abincin ka,danni ba baiwa bace. Yazuba mata idanu”ji wasu soki burutsu da yarinyar nan take fad’a,yakalleta cikin natsuwa”nine bawan ki kenan, tunda duk rintse zan fita in nemo in kawo miki ki ci ko? Taturo baki gaba”ko bani dolen-dole kafita ka nemo,to ni guda nawa nake cin abincin?
Kinga ba wannan ba d’auko min abinci na fad’a miki sauri nake yi”na daina girki a gidan nan, tunda ko a tsarin shari’a ai cewa akayi miji yaciyar da matar shi bawai mace tayi girki ba.Yagyad’a kai”to amma dai yin girki a wajen mace dole ne,tunda kyautatawace idan miji yafita ya nemo muku,ke kuma sai ki dafa muku, a kuma al’adar duk mutanen dana sani galibi matane suke yin girki haka aka taso anayi Iyaye da kakanni tun tale-tale.Ba sai da so da k’auna za ayi hakan ba?Tafara k’unk’uni.Shima sai yanzu ya harbo jirginta…kumallon mata ke d’awainiya da ita,to amma me san d’an tsuntsu shi yake binshi da jifa.
Yarik’o ta tana k’ok’arin fizgewa sai yamata rik’on kura ta samu nama,sai ta koma tayi lamooo “Sudaida a duniyar ALLAH me namiki da bakya so na?Yad’ago fuskar ta suka kalli juna”haba Zaujatiii…Dan girman ALLAH fad’amin abinda zan miki dan in samu k’auna da soyayyarki.. Yagewaye hannayeshi a jikinta yana mata wani salo…yayi k’asa da murya yana mata wasu irin kalamai na rarrashi da bambaki me k’aryar da damuwar data mamaye sararin zuciya.
Sak’onnin na shi yana shiga ilahirin gangar jiki da zuciyarta duk da bata so hakan ba amma zuciyar ta tak’i bujirema hakan,k’aunar shi da haushin shi yamamaye ta,sai kawai ta fashe da kuka ta k’wace tashige d’akin bacci tafad’a gado takifa fuskar ta a jikin matashi tana jin wani irin abu dabata san ko menene ba.
A tsakiyar d’akin yaja yatsaya yana kallanta”to meye abun kuka?Kai sha’anin mata a wasu lukutan sai su wallahi,banda dabi’arsu ta rauni da kuma dai shagwa6a wai tarwad’a da kukan k’ishin ruwa.Agefen gadon yazauna,yarik’o hannunta”kinga kukan ya isa haka share hawayen ki dan yana ta6a min zuciya,zai hadda sa min rud’ani fa…ta tureshi”Kalaman ka baza suyi tasiri a zuciya ta.Yagyad’a kai”toh na nawa kuma?
Yaya d’ansarai ba ka so na dan tunda aka kawo ni gidan nan nayi adabo da farin ciki,kazo garin nan tun farar safiya amma sai gab da magriba za ka shigo gidan, sannan sai kadinga nuna min wasu can sun fini mutunci tunda za kaje wajen su kasahare waje kuyi hira,ni kuma ko oho,idan nakira ka a waya sai kadinga min fad’a… Kaza da kaza haka tadinga fad’in duk abinda yazo bakinta”ni gaskiyar magana na gaji da matsalolin ka,idan cuta tak’i ci tak’i cinyewa ai rai take nema.
Yayi yar dariya”wato laifi tudune…ba nine sama da ke ba?Ko ba aure tsakaninmu ai bai kamata zan fita kice min”ALLAH raka taki gona ba.Kin San wannan kalmar ta min ciwo ta kuma bani mamaki wai daga bakin ki tafito?Dan na miki fad’a akan abinda yake dai-dai?Dama gyara kayanka yana zama sauke muraba Sudaida? Tasunkwui da kai,itama ta gane tayi kuskure”Yaya d’ansarai…ta kira shi,sai kuma taja tayi shiru. Yakalle ta”na’am ya aka yine?Da rawar murya tayi furucin kayi hak’uri na gane kuskure na…Idanun ta yaciko da kwallah.