GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tad’ora ha6arta a kafad’arshi ta dama” kayi hak’uri…Na yi Sudaida ni ai ina son ki a kowani hali da yanayi kece dai kika ce sai kina sona za kimin girki ko?Tayi shiru cikin alamar kunya.Yakalleta yanzu dan girman ALLAH babu soyayyata dank’are a taki zuciyar?Tad’an ta6e baki a zuwan furucin shi bai gamshe taba ko a kwalar rigarta.Tajanye ha6arta tana mishi wani kallo cikin turo baki gaba,da yanayin shagwa6a ta tambaye shi”me kake cewa?Shima yarama irin kallan data mishi”a ah bance kome ba.Takyalkyake da dariya. Yawatsa hannaye “magulmaciya kawai ana so ana kaiwa kasuwa;uhhh yakama ha6a”wato an hak’ura ana shan kukar k’azama…kafin yak’arasa tarufe mishi baki da tafin hannunta na dama”ai dai na ce kayi hak’uri…

Yasauke numfashi”ni dake muna san auren nan ba na dole aka mana ba,fad’uwa ce tazo dai-dai da zama,sai dai fa Sudaida bani da lafiya.Tad’ago tana kallan shi.Yalangwa6e kai “bakiga yadda na rame bane Zaujatiii… Tamishi kallan tsafff sai taga hakan har a kan fuskar shi, tabud’e idanu cikin tsoro”toh me yake damun ka!

Kayi rashin lafiya ne ban sani ba lokacin kana makaranta?Yagyad’ai”eh ai kullum a cikin ciwon nake…Cikin fargaba tasake binshi da kallo”ciwon me?Toh me yasa baza kaje asibiti ba Yaya Julaibib?Ai ciwon son kine bana ganin likita ba,nayi fama da kewarki sau shurin masak’i Zaujatiii.. So ba k’arya bane,wani mikine a zuciya ta”Sudaida ki furta min kina so na,kina k’auna ta, za ki zauna dani,muyi hak’uri da juna tunda zo mu zauna zo mu sa6ane.

Tajijjiga kai”ni na yadda na amince,ina son ka,ina k’aunar ka akowani irin hali da yanayi mun zama k’arfe da mayen k’arfe Zaujiii… Yagewayeta da hannayenshi”hankali na ya kwanta, bani da sauran shakku,ba abinda za kimin yasake bani tsoro.Tayi murmushi”uh uh fa Yaya d’ansarai karkamin kurifa?Yagirgiza kai”ai nagane logonki yarinya,ba kuri bane,duk abinda za kiyi a banza wai talaka ya girmi sarki.Tagyad’a kai”ALLAH dan dai na tuba ne…sukayi dariya zuciyoyin su fesss…Hummm…Fushin masoya hutuhhh….

Nurse a’isha Muhammad Jibril{Asdilat for real????} Ubangiji ya kiyaye min ke da kiyayewar shi,yatsare hanya,yakaiki Nursing School Mak’arfi lafiya. Ubangiji kama karatun na su albarka.Kasa su amfani kansu su amfanar da d’aukacin al’ummar Manzon ALLAH,da ita da duk wata Nurse dake fad’in KD garin gwamma da sauraran Jahohin mu na arewa,dana sauran yan’uwa musulmai na duniya kaafatan????

Bar ganin ka ta ra…kiyayi me nema.
A sara a kasuwanci jari.

15 Jumaada Thani 1441
9 February 2020

We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintikau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na ashirin.

Yaciro sakamakon jarabawarta a cikin jaka ya bata tana gani,ta samu sakomako me kyau credits shida har da lissafi da turanci”toh tunda kince kina so na,za kicigaba da karatun ki kwanan na.ALLAH da gaske Yaya Julaibib? Yagyad’a kai Insha-ALLAH.Tak’ank’ame shi tana bashi sumba da godiya…gaskiya na k’ara son ka ninkin ba ninkin,malala gashin tinkiya.Suka kalli juna suna dariya.

Safiyya ta haifi sankacecen yaron ta me girman ban mamaki.A gidan suka had’u dukan su suna ta hirar yaushe gamo ta baki da baki duk da kusan koda yaushe suna had’uwa a Whatsapp. Khausar tasake kallan yaron sannan tayi yar dariya”gaskiya Yaya Safiyya duk girman cikin nan ki ban zaci d’a d’aya za ki haifo mana ba. Tagalla mata harara”toh madallah ke idan kin ta shi sai ki haifo yan hud’u.Tagyad’a kai”za ko kisha mamaki. Zainab takama ha6a”ke Khausar yau she akayi daren da gari zai waye ne?Yi hak’uri Maman Hanifa.Safiyya tayi murmushin mugunta”ai akan tafe kan isa Khausar,ALLAH dai yabamu rai da lafiya za kiji jin jikinki,ki kuma gani ganin idanun ki…

Sai bayan sallar azahar Sudaida tawuce gidan Inna,anan ta tarar da Nasmat taje gaishe da Inna da bata ji dad’i ba kwanaki biyu da suka wuce.Tazauna tana tayata ninke kayan wankin Inna suna ta hirar su suna shan dariya, basuji shigowar shi ba sai ganin shi sukayi tsaye a bakin k’ofar yanad’e hannayen shi a k’irji”hirar me kuke yi haka ina ta sallama ba wacce tajini bare ta amsa.Nasmat tace”au yi hak’uri autan Inna bamu ji bane.Yagyad’a kai yana kallan Sudaida”d’an zo mana.

Tamatsa wajen shi suna k’us k’us k’us d’in su,Sudaida tana kyalkyala dariyar kalaman daya fad’a mata.Nasmat taja tsaki”ke tunda maganar taku ba tak’are bace,to nifa tafiya zan yi kina 6ata min lokaci sai kace ba gida d’aya kuka kwana ba.Yajuya jeki Zaujatiii wannan yar sa’idanu ce.Tad’an d’aga murya”Yaya d’ansarai karfa kamanta. Idan na manta ki tuna min tawaya kafin in dawo.To adawo lafiya.

Nasmat tabita da kallo”wato ke da d’ansarai abun nema ne yasamu matar falke ta haifi jaki. Kamar yaya?Tayi mumushi”ke dashi d’in duk kuna matuk’ar k’aunar junan ku,sai yanzu k’wak’walwata take hasko min wasu yanayi da nake gani a tattare daku na tsananin kishin juna a kowani hali da yanayi,kishi kuma baya k’ayatarwa matuk’ar ba soyayya,toh ALLAH ya dauwamar da k’auna har Darul-karamah(Aljannah) Sudaida tayi lallausan murmushi”ai ba ja kare ya mutu a juji.Ina son Yaya Julaibib amma halin miskilancin shi wasu lokutan yana bani haushi.Nasmat ta kyalkyale da dariya”miskili ka fi mahaukaci ban haushi.Abdul yashigo da rake ferarre,atile,yalon Bello da d’anbagalaje yakaima Inna a d’akin-girki wai inji Kawu,tana dubawa tamik’a mishi ledar “wannan dai Sudaida zaka kaima,maza tana d’akin-shak’atawa.

Nasmat ta tafi,amma ita har dare tana gidan.Bayan sallar Isha’i Alhaji Abdullahi yashigo. Tamik’e da sauri takar6i kayan hannunshi tana mishi sannu da zuwa,yasa6a babbar rigarshi fuskar shi cike da fara’a”a ah Sudaidan Malam d’ansarai ce?Ta sunkwui da kai.To sannu da zuwa,yashiga d’akin-shak’atawa ita kuma takai kayan d’akin-girki sannan taje ta gaisheshi cikin ladabi.”Lafiya lau,kunanan lafiya ko?Tad’anyi murmushi tana murza zoben hannunta,itafa har yanzu nauyin Baba take ji tunda akayi auren nan. Yacigaba,

“ALLAH yamuku albarka,ayita hak’uri rayuwar duniyar ma gaba d’ayan ta hak’uri ce,idan akayi hak’uri da yawa aka jajirce, agaba sai kiga anyi nasara a koma menene.Yasa hannu a aljihun rigarshi yar ciki yad’ibo kud’i yan d’ari biyar dabai san ko nawa bane yabata.Tasake sunkwui da kai “Baba kabarshi nagode.Yakad’a kai”Sudaida kinga…tad’an d’ago takalleshi”ai ba wanda yake k’in alheri sai shaid’an, ke ai ya tace,a kowani lokaci naga dama zan iya miki kyauta ko da baki zo ba,to zan iya aika miki dashi har gidanki.Tasa hannu biyu takar6a”nagode Baba ALLAH yak’ara girma.Amin Sudaida. Yamik’e yatafi d’akinshi.

Har tafara bacci a gadon Inna yashigo gidan.Baba yarufe shi da fad’a”kai Malam d’ansarai ban sanka da yawo kamar wanda yaci k’afar kare ba ko da daba ka da Iyali bare yanzu, ina katafi ina ta kiran layinka bata shiga?Ya amsa da ladabi”amin afuwa Baba,wallahi Gidan-Waya natafi game da karatun Sudaida,sai kuma nayi rashin sa a sai mako me zuwa,ni kuma ba na nan, kuma na tsaya ganin Provost d’in makarantar ne. Wayata kuma mutuwa tayi saboda rashin caji. Yagyad’a kai”to ALLAH yataimaka,amma maganar karatunta ai ba damuwa ko da baka nan,zan sa Aminu yayi kome.Yakalle shi kwanaki nawa za kayi kadawo?Baba nima ban sani ba sai dai kawai anganni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button