GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yanunashi da yaysa”to kadinga kiyayewa da da da yanzu bambancinsu na da yawa,bazan ji dad’i ba idan kana tafiya kana share waje kayi zaman ka iyalinka kuma ko oho ba,a zaman takewar iyali ba abinci da abun sha kad’ai ake buk’ataba a ah har da kai gundarinka,kuma kullum kadinga tunawa kai shugabane za kuma a tambaye ka game da hakkin shugabancin da aka baka kana ji ko?Cikin girmamawa ya amsa”eh Baba nagode ALLAH yak’ara girma.

Inna takalkeshi”kai Julaibib dare na dad’ayi kashiga kaci abinci.To Inna,yashigo yazauna yana cin abincin,yana kallan labaran k’asa amma rabin tunaninshi na wajen Sudaida da take bacci,daya gama ci yakai kwanon d’akin-girki sannan yazo yatashe ta suka wuce na su gidan.

Dasafe Aminu yaje gidan suka tattauna akan karatun Sudaida.Yakar6i k’ananan hotunan ta, Sudaida tashigo da sallama ta ajiye jug d’in hannunta a gaban Aminu”dama ina ta sauri dan karka tafi.Yad’ora duka hannayenshi a saman tebur d’in”ban tafi ba amma ba sha zanyi ba.Tacire murfin”kagani Yaya Aminu kunun tsamiya ne mutumin ka.Yayi murmushi”toh idan nasha na ki inyi yaya da Innarmu da yake jirana? Julaibib yace wannan za kasha tunda kullum na Inna kake sha,da rana sai kasha wancan.Yamik’e kai Malam damun manya ai yafi na yara gard’i kusha abunku,yabashi hannu sukayi musafaha “ALLAH yakiyaye hanya,sai munyi waya.Julaibib ya amsa da amin,nagode.

Sudaida Ibrahim Me-Lambu ta fara karatun lissafi da kimiyyar na’ura me k’wak’walwa (Mathematics/Computer Science)sai dai tana shan zirga-zirga,lallai ilmi ba a samun shi da sauk’i, sai anyi gwagwarmaya kamar zuma yake ga zak’i ga d’ankaran harbi.Yau tana gidan Hajiya tana shan rake suna hirar Julaibib da suka gama magana dashi ta waya,shima yana can yana fafatawa da karatun.

Gajiyace da samun waje wai kuturu da gad’a,bayan ta gama shan raken bacci yafara kawoma idanun ta ziyara.Hajiya tatashe ta,tamik’e zaune tana mitstsik’e idanu”Hajiya lafiya?Tagyad’a kai”lafiya k’alau,kishiga d’aki ki kwanta a gado mana.Takalli agogon dayake d’aure a hannunta nadama tad’an yi tsaki”lokaci ya ja sosai,sai tamik’e tanasa hijab,tad’auki jakarta tara taya “Hajiya gwamma in tafi gida yamma tayi sosai. Hajiya tace shikenan sauka lafiya,sukayi sallama tatafi.

Bayan sallar Isha’i tana zaune tana nazarin littafan data barbaza akan daddumar datayi sallah, hankalinta yayi nisa akan karatun kamar a sama taji an maida k’ofar d’akin-shak’atawa an rufe,ba tare dataji motsin shigowa ba,tamik’e dasauri kamar za ta hantsila littafin hannunta yafad’i k’asa,tarintse idanun ta tana Istirja’i zuciyarta tana bugawa da k’arfi saboda tsoro, d’akin yayi tsit ba motsin kome sai karar agogon bango tik tik tik…Tasake kasa kunne,nan ma shiru bataji kome ba,sai tabud’e idanun ta wato kawai tsorata tayi?Takad’a kai”wallahi mutum rahama ne,yanzu ma dan dare yayi ne amma da gidan Inna za ta tafi,ALLAH yakaimu gobe na daina kwana ni kad’ai.Caraf idanun su yahad’u,yana tsaye nad’e da hannayenshi a k’irji, kafad’ar shi tadama rataye da jakar matafiya ruwan toka,yayi sharrr…dashi cikin farin yadi da farar hula zita.Tanunashi da yatsa”Yaya d’ansarai kaine da gaske ko kuma gizo ne?Yak’arasa kujera yazauna “matsoraciya kawai,to da gaske ni d’inne.

Tasauke numfashi”wai ALLAH to sannu da zuwa,sai kuma tad’an turo baki gaba”amma gaskiya ka tsora tani,kuma d’azu munyi waya amma baka fad’amin yau zaka dawo ba?Nasamu sarari ne shi yasa nace yau kome dare sai nazo na ga Zaujatiii…Takawo mishi ruwa da lemu,yad’auki ruwan yanasha yana mata kallan nazari ta dad’a ramewa.Ya ajiye kofin yarik’ota”Zaujatiii…me yake damun kine? Tad’ago kai takalleshi kamar bata ji ba”na’am me kace?Sai kuma tagirgiza kai”ni ba abinda yake damuna,tamik’e barin maka abinci me sauk’i ko yar dafadukar taliyace… Yabita da kallo bawai jikin na ta yake k’arema kallo ba,a ah tunanin irin ramar datayi kawai yakeyi,kuma acewarta wai ba kome?

Yatashi yabita”ni fa bazanci wata taliya da daddaren nan ba gaskiya.To me zaka ci? Yakar6i albasar da take 6arewa ya mayar ma’ajiyarta”dafamin shayi kawai.Tayamutsa fuska “shayi dai shayi dai?Taturo baki gaba”nima gaskiya baza ka sha wani bak’in ruwa da daddaren nan ba,kai baka gajiya da shayi kamar wani d’an Niger?Yayi yar dariya”bari sujiki ba ruwa na,ke dan baki san sirrin da yake cikin wannan shayin nasu bane da neman shi zaki dingayi ruwa a jallo.

Takyalkyale da dariya”ALLAH yasauwake in nemi shayin da ba madara.Hum yarinya baki san amfanin wad’annan ganyayyakin bane. Takalleshi”toh meye amfanin su?Yagirgiza kai”zan fad’a miki amma ba yanzu ba.Sai yaushe?Sai lokacin dana koya miki sha,idan nafad’a miki amfanin nasu zaki yadda dani d’ari bisa d’ari dan kinji a jikinki,amma yanzu idan nafad’a miki,ba lallai ne kiyadda ba”gani ya kori ji.Tashagwa6e ni dai tunda baza kaci taliya ba to kaima baka shan shayin sai dai muje kaci donut da yoghort.Yarik’o hannunta”na yadda muje.

Dasafe tafito tsab cikin shigar kamala da mutunta kai”Tazauna a hannun kujerar da yake”Yaya d’ansarai taso ka kaini na kusa makara.Batare daya d’ago yakalle taba yanuna mata abinci”zauna ki karya kafin in gama abinda nake yi asibiti zamuje a miki General-check up. Tabishi da kallo cikin mad’aukakin mamaki”asibiti kuma? Tagirgiza kai ni dai gaskiya lafiya ta k’alau ba abinda yake damuna.Yad’ago yakalleta a gajerce yacigaba da danna na’ura me k’wak’walwa”kizauna kici abinci nace ko?

Ni fa banajin yunwa kuma ai…sai yad’aga mata hannu ya isa.Duk sukayi shiru nawucewar wasu dak’ik’u,tasake kallanshi”Yaya d’ansarai zan makara fa.Yayi kamar baiji abinda take fad’a ba.Haushi yakamata tamik’e tsaye”ni na tafi.Nan ma shiru yayi.Tajuya tayi tafiyarta tana surutai”da baka sa min rai ba da tuntuni banyi tafiya taba?Dama ai na saba tafiya ni kad’ai, ALLAH yasauwak’e maka wannan halin.

Da yamma tadawo daga makaranta a gajiye,ba abinda take buk’atar yi sai bacci danko jiya ba wani baccin kirki tayi ba Julaibib ya hanata sakattt…Tana shawo kwanar gidan su tahango wata mota me d’aukar hankali fara karrr…sai d’aukar idanu takeyi a cikin hasken rana,wata kyakkyawar macece me garin jiki wankan tarwad’a tabud’e motar tafito tanama Sudaida sallama. Sudaida ta amsa sannan suka gaisa a takaice… Tacigaba da tafiyarta,matar tace”Dan ALLAH jimana “tajuyo tad’an kalleta sai ta matsa kusa da ita,matar tagyara farin medicated glass d’in data rufe idanun ta. Takalleta sama da k’asa wani murmushi yasu6uce mata,tanunata da yatsa “Sudaida ko?Sudaida tad’ago suka kalli juna,sai ta gyad’a kai kawai dan bata san a ina matar tasanta har tasan sunan taba.

Toh kiyi hak’uri na tsayar dake ba tare da kin san koni wacece ba,ina fata mijinki d’ansarai yafad’a miki zuwa na?Tak’ara kallan matar”wallahi ba k’arya hutu ya gama ratsata,ido ba muduba amma ai yasan kima,kayan jikinta na alfarma,a inda Sudaida taji dama-dama wai kibiya a cikin idanu shine shigar sanin darajar kai tayi harda hijab d’inta tsawonshi yawuce gwiwa da kad’an,tarasa amsar da zata bata tunda Julaibib bai mata maganar wata za tazoba gaskiya,sai tayi murmushi tana gyad’a kai”sannu da zuwa,toh bismillah “suka jera suna tafiya har tabud’e d’akin-shak’awa tanuna mata wajen zama taje takawo mata abin motsa baki suka sake gaisawa sannan tamik’e”bari a mishi magana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button