
Suka kalli juna yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da bata so dan haushi yake bata,yafito daga wanka yana shafa mai.Yaya Julaibib wani irin mutum ne me tsatstsauran ra’ayi da baza ka ta6a gane inda yadosa kai tsaye ba a wasu lokutan.”kayi bak’uwa. Fuskarshi ba walwala “wacece ita da baki san sunan taba? Tajuya”oho nima a ina nasan ta,kafito ka ganta mana ganin idanun ka.Sai da yagama shiryawa sannan yafito, yana ganinta yasaki fuskar shi yana mata barka da zuwa, yazauna suna gaisawa da tambayar me jiki.”jiki Alhamdulillahi.Ni da Baban Humaima ne yana mota. Yafita yashigo dashi..
“Doctor Garga Ibrahim Manogi “babban likitane da ake ji dashi a Teaching Hospital na Zaria,k’wararre ne akan abinda yashafi k’wak’walwa(Neurology) likitan da akace sune ma idan sunje Shika lokacin da Bilkisu tayi hatsari, shine yake auren kanwar Innar Bilkisu.
Sudaida takawo musu abinci.Doctor Manogi yanaci yad’ago yana kallansu”gaskiyar magana abincin nan yayi d’an karen d’and’anon daya burgeni,kai Ustazu haka yake kiran Julaibib dole za kayi tumbi kwanan nan,yakalli Sudaida”kin gane ko idan ya6ata miki rai karki hana shi kome da yake so sai wannan Palatable girkin na ki tunda shi baya san cin abincin waje kinga ai kin horashi duk da ya iya dafawa amma dai kafin yadafa ai ya d’and’ana ko?Sukayi dariya.Doctor Manogi haka ALLAH yayi shi da sauk’in hali da raha sai yanayin shi yamata shige dana Yaya Aminu.Yakalli matar shi”Bongel Ustazu da matar shi basu burge kiba?Tayi murmushi”sun burgeni musamman ita, kaga bata sanni ba amma har tabarni nashigo mata gida duk da taji na ambaci sunan mijin ta,ka san wasu matan da kishin rashin hankali. Yad’an harareta”toh waya fad’a miki bata kishin shi? Kawai ta hak’urane dan ta san itace kad’ai a zuciyar shi, kin san jiya muna tare dashi bayan sallar magriba sai kawai yace min wai gida za shi,nayi-nayi dashi yabari yau mu bugo sammako amma yanok’e”wai ai yau d’in da sassafe zai dawo,amma kinga d’an rainin hankali gashi nan a zaune har bayan la’asar.Julaibib yasa hannu yana shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi yana murmushi.
Bongel tad’an kalli Julaibib”ina son ganin Adnan Ibrahim Me-Lambu inji abinda yahana shi dawowa makaranta yayi B.ed d’in shi. Ai Adnan ya san dad’in kud’i ya zama d’an kasuwa kwanaki na mishi magana yace wai shi bazai iyaba wanda yayi abaya ALLAH amfana.Tace kash…na mishi sha’awar karatun saboda yaron yanada k’ok’ari yana d’aya daga cikin d’alibaina yan gaban goshi. Da muna magana ta waya daga baya na daina samun shi. Eh wayar tashice tafad’i yanzu wani sabon layine dashi.Ai ko zaka bani zamu muyi magana…
Sai yanzu Sudaida ta fahimci wacece ita.Bongel Lecturer ce,yaren turanci (English) take koyarwa a FCE Zaria,lokacin da Adnan yake karatu tasha jin sunan Malama Bongel a bakinshi da irin kirkinta,da taimakonta ga d’alibai,bata san d’alibai wad’anda basu da himma,tafi matsa ma irinsu da yawan tambayoyi dan zaburar dasu, masu san karatun suna zage dantse ko dan kar susha kunya a gaban d’umbun jama’a yan uwanshi d’alibai,yan abi yarima asha kid’a,yan kyalekyale suna adawa da irin halaiyarta musamman na zuwa musu aji a bazata ta na musu jarabawar gwaji,irin su Adnan a lokacin sune yan gaba gaba,baya yadda yarasa laccanta sai da dalili me k’arfi.Malama Bongel ALLAH yabata k’warewa da juriyar koyarwa,ga kuma ilmin tsurar shi Ubangiji me kyauta da k’ari ya ba ta,babban kuma abinda yak’ara mata farin jini shine bata kada d’alibai a jarabawarta (carry over)
Sunyi sabo da Adnan,saboda wani ciwo da yayi taje gaishe shi anan take tambayar shi d’an wani gari ne?Yafad’a mata Zonkwa,tayi murmushi kace kai d’an gidane,shikenan dazarar anyi hutu zata ba shi sak’o yakaima Innar Bilkisu a garin Matsirga,kanwartace uwa d’aya uba d’aya.A wasu lokutan ma takan ai ko shi takanas da kud’in mota yakai mata sak’o yakoma Zari’a a ranar. Malama Bongel tana da sauk’in kai,ba ta d’agawa da ilmin da take dashi,sai dai tana fama da ciwon idanu,tasha wahala dan akwai lokacin data ajiye aikin koyarwa saboda kome sai da lafiya akeyi, cutar glaucoma tayi mugun kamata,sai da suka tashi tsaye sannan tasamu lafiya,suka kuma ba ta medicated glass da take amfani dashi.
Sudaida tasake kallanta cikin zancen zuci”kowani d’an Adam tara yake bai cika goma ba,kowa da irin tashi matsalar.Wato wannan zuwan kuma Innarsu Bilkisu ce ba ta da lafiya kenan,dan dasafe taji Julaibib yana tambayar mai jiki tawaya lokacin datake shiryawa,sai dai bata tambayeshi waye ba lafiya ba,shima bai fad’a mata ba,dan idan bai ga damaba ko ta tambaye shi,shiru zai mata kamar baiji ba.
Shi kuma Julaibib sun had’u da Doctor Manogi ne a wani taran MSSN da akayi a jahar Taraba,sun fito sallah dan Julaibib shi yamusu limanci,suna yar hira yake tambayar shi shi d’an wani gari ne?Yafad’a mishi Zonkwa amma a Zari’a yake zama a halin yanzu dan shi d’alibine a jami’ar Ahmadu Bello.Doctor Manogi yanuna shi da yatsa”kar dai kai ne d’ansarai sarauyin wata Bilkisu data rasu?Yajijjiga kai”eh ni ne.Yace ALLAHU-AKBAR yamishi ta’aziyya sannan shima yamishi bayanin ko shi waye…daga nan hira ta 6alle har suka dawo Zari’a suka cigaba da mutunci da zumunci.
Sunyi hira sosai sannan suka shirin tafiya, Bongel tadafa kafad’ar Sudaida”naji kin fara karatu me tsada na masu k’wak’walwa,toh ina tayaki murna.Ki zage dantse kiyi ilmi kema kiba al’umma gudummawa da d’an abinda ALLAH yabaki,musulmin kwarai shine wanda zai amfanar da yan uwan shi da alherin shi.Sudaida kinyi sa ar kama zuciyar d’ansarai dan ba shi da wata magana sai taki,dan ALLAH kiyi hak’uri da shi, shima dole yayi hak’uri dake,zo mu zauna zo musa6ane,ALLAH yabaku zuri’a masu albarka. Sudaida tasunkwui da kai bata amsa ba tana d’an murmushi,ta bata wasu biscuit da alewa”gashi aba su Humaima”Bongel takar6a tana godiya”su Humaima sun gode.Doctor Manogi yamik’e yana kallan Julaibib”zaka d’auko jakar taka mutafine? Yayi yar dariya yana sosa k’asumbar shi”sai ranar jumma’a Insha-ALLAH. Yagyad’a kai’allah ya kaimu,toh madam mu zamu wuce.Yaciro rafar kud’i yan ashirin guda d’aya ya ajiye mata a saman tebur,tamishi godiya.Sukayi sallama Julaibib yatafi rakasu.
Bayan sallar Isha’i yashigo ta mishi sannu da zuwa.Ya amsa da yauwa fuskar shi ba walwala takalleshi na wasu dak’ik’u”Yaya Julaibib za muyi bak’i amma shine baka fad’a min ba?Yayi kamar ba dashi take magana ba.Haushi yakamata. Yaciro wayar shi a aljihu sai ta fizge. Yad’ago yana mata wannan kallan da yake bata haushi,bai yi magana ba sai hannunshi daya mik’a mata alamar tabashi wayar,itama tayi kamar bataga abinda yayi ba”me yafaru ne ina maka magana kayi shiru?Oh baki ma san abinda yafaru ba ko?Tagyad’a kai”ALLAH ban sani ba.Yayi shiru kamar bazai yi magana ba zuwa can kuma yace”Da safe bana ce miki asibiti zamu tafi ba amma ki kayi tafiyarki makaranta saboda kin raina ni ko?
Tawani marairai”dan ALLAH kayi hak’uri, to amma Yaya Julaibib ni fa lafiya ta k’alau.To ramar me kike yine?Tashafa wuyanta”oh ni Sudaida kowa haka yake fad’a ni kuma ban gani ba.Yad’an harare ta”ni ai nagani bakya san abinci ne ai da safen ma bakici abincin ba kika tafi, yanuna mata ledar da yashigo da ita,tamik’e tad’auko faranti a d’akin-girki tajuye mishi balangun me koren tattasai,albasa,kabeji da cucumber ga yajin tafarnuwa,ta tura mishi gaban shi”ai na kine zauna ki cinye shi.Yaba kyauta tukwuici”sai ta mishi godiya dafatar k’arin bud’i amma har ga ALLAH ita ba ta wani jin balangu, yanka biyu taci,ta d’auki rakenta tafara sha.Shi kuma yana dad’a fad’a mata lallai ta dinga cin abinci kar cutar gyanbon ciki(ulcer)takama ta. Yaya d’ansarai ba fa rashin cin abinci yake kawo cutar gyambon ciki ba.Yabar rubutun da zai yi yakalleta”to me yake kawo shi? Ta6alli rake ta taune ta zuke ruwan tazubar da 6awon sannnan tace”rashin cin abinci akan ka’ida shi yake haifar da cutar gyambon ciki.Kamar yaya bangane ba.