GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Bakomai…Tayi murmushi yau wace rana ya mata wata magana ta daban ba amsar daya saba fad’aba na “Bazan iyaba”saita kalleshi “to za ka aureni?Yayi shiru kanshi ak’asa.Tad’an motsa kafad’a. Tana zuwa kusa da k’ofar ya matsa da sauri kamar zai hantsila.Tayi yar dariya”Matsoraci kawai “ni ba abinda zan maka yanzu amma duk ranar daka shigo nan tanuna tsakiyar tafin hannunta na maka kattt…kisan mummuk’e,sai tayi d’as d’as d’as da yan yatsunta wani murmushi ya su6uce mata. Tamishi wani kallan k’auna me cike da shauk’i…Tabud’e k’ofar tayi tafiyarta.Yasauke gwauran numfashi “wallahi da basu da lecture gobe da sassafe da yau yayi tafiyar shi gida kamar yadda Musaddiq yatafi.Yamaida k’ofar yarufe da sak’ata yasa mukulli sannan ya kwanta cikin wani irin yanayi.

Tana zuwa d’aki tafasa ihu tafad’a gado.Lidiya da suke yan’uwa kuma d’akinsu d’aya sai dai kowa da abinda yake karanta kamar dai Julaibib da Musaddiq tabita da kallo sai juyi take cikin wani irin yanayi,tabar yanka ganyen Ogu da take yi na abincin darensu,tazauna agefen gadan.

“Inzayadami Kasham?(Meyafaru Kasham)

Kasham tacigaba da juye-juyenta cikin wani irin yanayi,zuwa can kuma tamik’e zaune, tajingina kanta ajikin gadan cikin sanyin murya tace ” Julaibib ne”

“Jesus Christ! Holy ghost fire!!!

Lidiya tafad’a tare da dafe kirji da duka hannayenta,tabita da kallan takaici taja dogon tsaki, wallahi kinji kunya,wai dan ALLAH me kika ganine ajikinshi daya tafi da hankalinki haka? Dogone k’akk’arfa,kar kuma kimanta Baranzan wanda kukayi alkawarin aure dashi,shima haka yake,ke ya mafi Julaibib tunda shi Sojane training d’in da yakeyi shi ko rabin-rabinshi ba ya yi, sunansu kuma d’aya”Maza”ko akwai wani abu bayan haka?Tayi lallausan murmushi”taja dogon numfashi a hankali take fitar da iskar tabaki ta hanci.Sannan tace”Hummm…Lidiya kenan ai maza kama suka tara amma halinsu ya bambanta. Tagalla mata harara”kin gama asara,ni dai banga abin so a wajen me shegen girman kai ba,shi ba kowan kowa ba dillalin kashi.Sannu wannan dazai amsa miki da yauwa sai yaga dama amma ke kina neman haukacewa saboda shi…kai tirrr…wallahi tayi d’as da yan yantsunta takoma kan girkinta tana mita Rubbish girl…

Kasham tazame takwanta”duk abinda zaki fad’a indai akan san d’ansarai ne bazai ta6a tasiri a zuciyata ba har abadan duniya, ina san shi koda shi aka tarama munanan halayen jama’ar duniya,ni na san ko waye Julaibib,ba shi da wani girman kai”so hana ganin laifi…

Suna zaune a shago jadawalin bikin Musaddiq d’in suke dad’a dubawa,dan saura kwanaki goma sha biyu.Tayi sallama daga waje tana sanye da riga da zani da dankwali na atamfa ruwan goro da ratsin k’ananan filawoyi ruwan madara da Bak’i,tayafa bak’in mayafi takalmanta bak’ak’e abinci takawo musu.

Wa alaikumussalam shigo.Tana shiga idanunsu yahad’u,yad’an saki fuska”yau Baba yayi tafiya sai zuwa yammaci zai dawo, ni kuma ban san irin garar da yake had’a muku ba idan kun kawo abinci”rake zan sha”sai Maths text book da Graph-book da za a sai mana ni da Yaya Khausar.

Banza yar k’auye,tafi kibamu waje, ba dama a tambayeta me take so sai tace”rake”to ba za a sai rakenba.Julaibib yad’aga mishi hannu “a ah malam shan koko fa kwanciyar rai,to me yamaka zafi?Yamaida kallanshi wajanta”koda yakema idan fitsari abin banzane kaza ma tayi mana.Ta sunkwui da kai”kowa yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yakeyi,shine ko nama a wasu lokutan baya iyaci duk san shi da nama kamar kura sai gani sai hange idan ciwon hak’orinshi ya motsa.

Me kace? Musaddiq yatambaye shi fuska a yamutse.Abinda kaji na fad’a”ke Sudaida jeki ki…sai kuma yamik’e ina zuwa.Dakanshi yasiyo musu Maths da graph d’in yakuma kar6o musu gasassun kaji guda biyar,d’aya ki kaima Inna,biyu nasu Mama,ku kuma dukkanku kuyi hak’uri ku raba biyun.Tasa hannu biyu takar6i ledojin”mungode Yaya Julaibib”.Yakauda kai daga kallan da take mishi.Jeki kinji karki daka ta wannan da hidimar aure tasa kanshi yake shirin yin gobara… Mutum bai kar zomo ba sai kiga yana shirin ba shi rataya.Tawaiwaya inda Musaddiq d’in yake,shima su yake kallo.Sai ta toshe bakinta da sauri kar dariyar da take 6oyewa ta su6uce mata tashiga uku,idan yakoma gida da daddare zai iya bata na jaki…tajuya dasauri tabar shagon.Julaibib yabita da kallo fuskarshi da murmushi.

Yauma Musaddiq ya rigashi komawa gida tun ranar laraba yatafi,Maimun ma an aiko mahaifiyarshi bata da lafiya shima yatafi.Yana fitowa daga masallaci yanufi d’akinsu dan yanajin yunwa shi kuma yafi gane yadafa abinda zaici fiye da yaje capteria,yana da miya dan haka yadora farar shinkafa yazauna yana yayyanka kabeji, tumatir albasa da gurji.Tana jingine da bishiyar barankaci tana hangoshi dan abaranda ya zauna saboda cikin akwai zafi kuma ba wuta,tana mishi kallan k’auna me cike da shauk’i,shi ko baima san tanayi ba kunu a mak’ota.Tasauke numfashi tana kiran sunan shi a saman la66anta wani murmushi yasu6uce mata ranar da duk ALLAH yabani sa a akanka?….Hummm tagyad’a kai”d’aurin gwarmai za kasha amma na k’auna… Tajuya tafiyarta.

Hajiya tashigo da sallama.Ya amsa cikin murmushi”Sannu da zuwa Hajiyarmu, yashimfid’a mata tabarma.Tace a ah mutanan Gidan-Waya saukar yaushe?Ai tun safe ina garin nan,wajejen k’arfe sha d’aya naje gida ba kyanan.Tagyada kai”Tabbas anyi haka,naje asibiti gaishe da Liman na masallacin juma’a ne.Yace “ALLAHU-AKBAR”ashe har yanzu ba a sallameshi ba?Ubangiji yabashi lafiya,zaman jinyar kuma yasa kaffarace. Ta amsa da amin,amin.Anjima ya kamata kuje kugaishe shi Yagyada kai “Insha-ALLAH.

Kai kadaine agidan?A ah Inna tana wankane”Tamishi kallan nazari”ni wannan zuwan sam baka min kyan ganiba,duk kayi wani firgai-firgai sai kace angon da hidima tasha kanshi kud’ad’en aljihu sun k’are,ko dai bakaji dad’i kwana biyu bane?Cikin yar dariya yace “to da Musaddiq kike wannan gugar zanan.Kai tafi can Musaddiq d’in wa?Shi da za a mishi auran gata,dakai nake yi.Yagirgiza kai”Hajiya ni dai lafiya ta k’alau.Cikin kad’a kai tace”amma dai sanin hali ai yafi sanin kama,idan ta kumbura tafashe tayi wari zamuji.

Bismillahi tamik’e”ni bazan zauna zaman jiran uwarka ba wannan halin nata tun na k’uruciya ashe bata barshi ba,taja tsaki haka takeyi idan tashiga bayi kamar tasamu gadon bacci da daddare,wani lokacin sai na bita da bulala take fitowa,shiga bayi ai lalurace da kake sauri ka kawar da ita kafito.Julaibib yad’an yamutsa fuska”Kai Hajiya”takalleshi saboda uwarkace sai ink’i fad’an halinta?Yagirgiza kai. Tace”to wooo ashe dai kowa yana san wawa haihuwarshi ce ba a so,dama wajanta nazo kwana biyu bangan taba”To kijirata mana.Wa?Ai tunda na mik’e sai dai kuma tabiyoni nawa gidan,tunda na ganka ai shi kenan ko baka gode bane? Aiko nagode miki ba kad’anba Hajiyarmu.Barin taka miki. Suna tafiya a hankali suna hirarsu,har gida yarakata sannan yawuce gidan Yaya Karima.Yaya Karima tadabance wallahi saboda halin dattakonta.

Rana bata k’arya saidai uwar d’iya taji kunya,ranar juma’a aka d’aura auran Musaddiq da Safiyyah,abokan karatunsu sunzo d’aurin auran nan Motoci har hud’u cike tam da jama’a.Maimun yace gaskiya garin Zonkwa yamin ba zata yadda nake tunanin garin ashe yawuce haka.Aminu yagyad’a kai”k’warai kuwa muna yin addininmu da komai namu kamar yadda hausawa,musulmai sukeyi a k’asar Hausa tunda akwai malamai masana addini a fannoni mabambanta,ga makarantu sai wanda kaza6a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button