
Yanzu misali ka saba cin abincin safe k”arfe takwas kullum haka kake yi sai kuma kazo ka daina ci a dai-dai lokacin…toh shi ruwan matsarmama da yake d’iga ya narkar da abincin shima ya saba saukowa ya d’iga karfe takwas to kullum haka zai dinga d’iga ko kaci abinci ko bakaci abinci ba,idan akai rashin sa a bakaci a dai-dai lokacin ba to sai yad’iga a cikin cikinka shikenan wajen ya zama ciwo…ciwon da mutum zai zo yashiga wani mawuyacin hali na ni ya su.. Yakalle ta cikin natsuwa”ahab ba cinyaba k’afar baya…
Ni dai na fada’a miki ki dinga cin abinci”toh Yaya d’ansarai nahhh…tayi furucin da wani salo na yanga da shagwa6a.Suka kalli juna sukayi murmushi,bata gama shan raken ba ta ajiye dan yau tayi d’amarar hana karatun daren nan,shi dai kullum cikin bincike da nazari,a makaranta karatu a gida karatu?Rai ai dangin goro ne yana buk’atar ban iska…batayi magana ba kawai zama tayi a gefenshi ta gewayeshi,a hankali tafara mishi wani salo…salon daya tilas tashi ajiye littafin nazarin yafara bin yarima dan su sha kid’a.
Hantsi yadubi ludayi na alhamis bataje makaranta dan basu da lacca,tana kwance a doguwar kujera Hajiya tashigo da sallama, tamik’e zaune”lale marhabun Hajiyar mu,sannu da zuwa.Tasa hannu tad’auki ledar da Hajiya tad’ora a saman tebur”me nasamu haka? Tabud’e talek’a sai tasa hannu tad’auki guda d’aya awarar madarar shanu ce,tagutsira sannan takalli Hajiya “nagode ALLAH amfana.
Tanaci suna hira,Hajiya kuma tana ta kallanta cikin nazari dan yar shimice ruwan madara ajikinta,ta yi kyau sosai amma ta rame”ni wai ramar nan dakike dad’ayi to ko dai ciki ne dake?Sudaida takama ha6a”wuuu..ciki?Tad’an ta6e baki”uhun rufani ki saya.Hajiya takad’a kai”eh lallai ba shakka k’uruci dangin hauka,cikin ne kike neman tsari dashi?Ke ba a haihuwar aka haifoki? Ya’ya da kike ganin su ai rahamane jin dad’in rayuwa ne,su Khausar ba gashi har sun fara zuwa asibiti awon cikin ba.Tamaida bayanta jikin kujerar tana cin awararta”hu’un to ni dai Hajiya bani da wani ciki.Ai ban musaba”ALLAH na tuba shi ciki ai d’an dumane a hankali yake yad’o.
Julaibib yashigo da sallama yazauna a d’aya kujerar suna fuskantar juna da Hajiya”Hajiyarmu kin shigo?Ta amsa da eh Julaibibi.Yakalli Sudaida”lallai yarinyar nan,wasa tare ci bamban ko?Zanga me siyo miki rake anjima.Tad’auki ledar ta zauna a k’asa kusa da k’afafunshi”duba kagani,kaifa kake fad’in awarar madara bata dameka ba.Yad’auki guda d’aya”ai ba cewa nayi kwata-kwata bana ci ba.Tamishi wani kallo a marairaice”to afwan Zaujiii…yayi murmushi koma dai toshiyar baki kika bani yau dai baza ki sha rake ba,kema muk’amuk’inki su huta.Haba Zaujiii…kaima kasan”I can’t do without sugarcane” tayi furucin da salon shagwa6a.Yamata wani kallo “au bama ni ba?Tasake wani narkewa”na rantse da girman ALLAH har da kai Yaya d’ansarai nahhh…Hajiya tagalla musu harara”oh Ya’yan zamani.Sudaida takalleta”da mukayi me kuma? Hajiya wai kin manta gidan amare kika zone?Hala kin manta hud’ubar dakika dinga manane a gidanki?
Takalleshi”Yaya d’ansarai kome tace mu muku indai bai sha6ama shari’a ba,ko menene shi bata togance ko abu d’aya ba.Hajiya tayunk’ura tamik’e”toh barin barku kuci karen ku ba babbaka.Shima yamik’e”Hajiya kiyi zaman ki,ni dama wayata dana sa a caji nashigo d’auka. Yacireta dan ta cika.Tagyara zaman hijab d’in ta”ai ba ganin ka yasani tafiya ba dama nayi niyya ne. Yasa wayar a aljihu”ALLAH huta gajiya Hajiyarmu sai nazo.Inji Sudaida.Tagyad’a kai”sai na ganki. Suka fita da Julaibib.
Bai dawo gidan ba sai da yamma tana d’akin-girki yamik’a mata raken”karki isheni da mita anjima.Tasa hannu biyu takar6a”shukran jazilan Ustazu. Yakalleta da sauri”au har dake? Yagyad’a kai tana yar dariya”har dani.Toh bar d’aura girkin nan kizo muje unguwa.Yaya Julaibib da wannan yammacin?Yad’aure fuska”ko da sulusin dare ne bazaki bane?Ta tsame hannunta daga cikin kayan miyar da take gyarawa”ALLAH yabaka hak’uri”ya amsa da amin.Kiyi sauri ki shirya ina jiranki a waje.Tabi bayanshi da kallo “zuciyar ta na raya mata wasu al’amura game dashi, takad’a kai”ALLAH yakyauta maka wannan halin wallahi.
Yana kallanta tafito amma sai da wasu dak’ik’u suka wuce sannan yabud’e mata motar tashiga tazauna tana d’aura belt.Ganin sun bar cikin gari yasa ta tambayeshi inda za su,amma yayi kamar bai ji taba.Itama sai taja bakin ta ta d’inke,tamaida bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanun ta,tana sauraran wa’azin daya kunna na Ahmad Ibrahim(Bamba)sai da yatsai da motar sannan tabud’e idanun ta tana kallan wajen,nan kuma ina ne?Ta tambayi kanta”fito muje mana..taji maganar shi a sama,tafito suka jera zuwa gidan.
Inna tayi murna da ganin su kwarai, irin kambamawar data musu yasa jikin Sudaida yayi sanyi, wato su wasu irin mutane ne masu karamci da girmama d’an Adam,suna da shiga ran da ciresu a sararin zuciya bazai zama abu me sauk’i ba wai cire wando taka,shi yasa Julaibib yakasa mantawa dasu duk da babu wacce tazama sanadin had’uwar ta su a doron duniya.Inna tad’an kalli Julaibib”ai munyi waya da Bongel take fad’amin gobe zaka koma lallai abaka madara katafi musu da ita wai wanda suka tafi da ita sun tsaya a Gama-gira wajen wata k’awarta shine tabata duka,dama Maude nake sauraron shigowar shi in bashi yakawo maka ikon ALLAH kuma sai ga Ku.Ya amsa da ladabi”eh Inna nima ta kirani ta fad’a min,sammako zanyi a goben shi yasa nace barin zo in k’ar6a daga nan kuma Sudaida ta gaishe ki.Ai kuwa naji dad’i ALLAH yamuku albarka.Suka sake sabuwar gaisuwa da Sudaida tamata sannu da jiki.Jiki ai Alhamdulillahi naji sauk’i sosai.
Da zasu tafi Sudaida tace gashi ni dai nazo banga Bello ba.Inna tad’anyi murmushi”ai da ya san da zuwanki da bazai raka Malam Zango ba.To agaishe shi. Zai ji.Julaibib yamata alheri me yawa,ada tana damuwa da irin hidimar da yake musu har tazo ta daina,tun ranar daya kalleta cikin natsuwa da girmamawa”Inna ki d’auke ni matsayin d’a,idan kika d’auke ni a haka toh na san duk abinda zan baki zaki kar6ane da dad’in rai kina kuma shimin albarka tare da min addu’ar dacewa a doron duniya da lahira.
Megado ita tahad’a mu,koda ba ta, bazamu rabu ba dan kuma baku k’ini ba.Inna tajijjiga kai tasa gefen hijab d’in ta tana share kwallah”gaskiya ne d’an nan,toh ALLAH yamaka albarka,ALLAH yabaka zuri’a d’ayyiba,ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi, yasa hakan a mizanin kyawawan ayyukanka.Yanzuma irin addu’o’in data dinga musu kenan shi da Sudaida.Suna ta amsawa da amin,amin.
Gidansu Sudaida suka wuce…Sauran k’anninta suka dinga murnar ganinta,itama taji dad’i sosai dan basa wani zuwa gidan ta,to yaushe ma suke da lokacin yawo?Daga andawo makarantar boko za a tafi ta allo,ko ta Islamiyya da daddarene kawai suke da lokacin kansu,idan ma ranar ba a had’o mutum da aikin gida ba (home work)Tasaki hannnunsu,taje ta rungume Mama kawai sai tasa kuka,Umma,Julaibib dasu Asma’u suka bita da kallan mamaki yanzun nan fa tagama kyalkyala dariyar shirmen gwarancin da Nana take mata…
Mama tace ashsha”to me yayi zafi haka da idanu za suci wuta?Tana k’ok’arin d’ago ta Sudaida tadad’a k’ank’ameta.Umma ta fusata”ke menene haka yau naji shashanci rok’o a gidan bebe.Mama tad’aga mata hannu”na ki idanu 6arin mai a yashi.Umma takyalesu suna magana da Julaibib.