GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama tayi k’asa da murya”to d’agani tunda bazaki daina kukan ba.Tayi shiru tana share hawayen sannan tad’an marairaice “Dan ALLAH har yanzu baki zo na ganki ba,ai dama na san ke kad’aice za ki zo,ko Umma ce tazuga ki?Mama tayi murmushi”au dalilin kukan kenan?Eh mana Mama.To karki damu inanan zuwa ni ba wacce ta isa ta hanani zuwa inda kike.Yauwa Mama ALLAH yabar mana ke,suna ta hira sai da Baba yafito yace su tafi gida haka dare yayi gashi sammako Julaibib zai yi.Sudaida tabi Umma d’aki tafito daga bayi alwala tayi tanasa hijab Sudaida tashigo.Suka kalli juna sai Umma tad’anyi murmushi”za ku tafi ne?Ta amsa cikin ladabi”eh Umma.Kun san Umma Boss ce bata d’aukar raini.Tabata wasu humrah masu k’amshin fita hayyaci”gashi nan dama ke kad’aice ba a kai miki ba.Tasa hannu biyu takar6a tana godiya. Umma to yaushe za kizo? Ke! Umma tafad’a cikin d’an bud’e idanu.Sudaida tasunkwui da kai.Sai kuma ta sassauta murya”Sudaida me zanzo in miki ne?Duk abinda kike so kima Mama waya ko ni,ko ki turo mana ta sak’o a rubuce ba shikenan ba?A sanyaye tagyad’a kai sannan sukayi sallama.

Tafiyar Julaibib da yammacin ranar tadawo makaranta tana so tayi girki tatafi gidan Inna sai ga Asma’u tashigo.Tataro ta cikin murna ‘oyoyo Yaya Asma’u sannu da zuwa.Ta amsa da yauwa tashige d’akin-shak’atawa,ganin haka yasa Sudaida tayi sauri tagama markad’a kayan miya taje suka gaisa,kamar kullum yau ma haka ta amsa gaisuwar cikin halin-ko-inkula tun bayan auren ta da Julaibib Asma’u take mata wani gani-gani data kasa gane manufarta.Tabi d’akin da kallo sannan ta sauke idanun ta akan Sudaida, tana sanye da riga da zani da dankwali na kamfala, ta ta6e baki”ina d’ansarai?Baya nan yatafi.Yatafi fa kikace?Tajijjiga kai”eh ya tafi.Toh yayi kyau… Bani sak’ona sauri nake yi.Sudaida tagirgiza kai “bai bani kome in ajiye miki ba.Bata sake magana ba wayar ta taciro ta kirashi.Yana d’agawa ko sallamar daya mata bata amsaba tafara hayagaga…

Kai d’ansarai haka mukayi dakai? Tayi shiru tana sauraranshi…wucewar wasu dak’ik’u sai kawai taja dogon tsaki”kai malami wallahi daga bayane sadaka da karuwa…eh to naji sai ta mik’a ma Sudaida wayar “Zaujatiii… Kud’in dana baki kin kai gidan kud’in ne?(bank)A ah sai gobe Litini…Yauwa toh kiba Yaya Asma’u dubu goma a ciki,ki bar sauran idan nadawo nabaki duka sai ki kai kinji ko?To Yaya Julaibib, ALLAH yadawo dakai lafiya.Tamik’a mata wayar sannan take ta d’auko takawo mata,a wulak’ance takar6a kamar wacce aka bata najasa.

Sudaida takawo mata meatpie da lemu dan bata gama abinci ba.Tagirgiza kai”bani dankalin turawa da kwai zanje in soya a gida, tamik’e bani leda,inda suke ajiyewa ta nufa, Sudaida tabiyo ta da ledar tana fad’a mata amma fa kwan ya k’are.Sai tabi d’akin da kallo gwangwanayen madarar Nido tagari guda biyu dana Ovaltine guda d’aya sai siga me y’aya na kwali(cube sugar)sai tasa hannu ta d’auki gwangwanin madara d’aya da siga kwali biyu a ranta tana mita”ni nasan d’ansarai baya shan shayi da madara,yanzu nan ita za taita shansu? To aiko bazata shanyesu ita kad’aiba dan nima wannan ai yafi min dankalin.Sudaida tabita da kallo itama tana jiinjina k’arfin hali fin me kora shafawa irin na Yaya Asma’u.Toh sata za a kira wannan abun kome?Tunda bata tambayi wanda yasiyo ba.

Abinda Yaya Karima bata dashi kenan ganin gari da san na Bello-badin,ko wajen Inna taje haka take mata d’auki d’ai-d’ai d’in duk wani abu daya bata sha’awa,abin mamaki kuma Baturiya da suna manga,kamar ba Inna da Baba ne Iyayen taba dan su sun san mutumci da karamci wallahi.Idan an mata magana ta ta6e baki tana fad’in to menene a ciki? Sata a gida ai rance ne…bare ita ai bama sata tayi ba tunda a gaban idanu take d’aukar abu.To amma dai ai ba ace an ba taba kai ALLAH yasauwake. Takar6i ledar tasa a cikin sannan tajuya”sai anjima.To Yaya Asma’u ki gaida gida.

Kwana biyar bayan nan da yammacin la’asar tadawo daga makaranta kawai tawuce gidan Inna. Asma’u tana zaune tana cin dafaffiyar masara takalli Sudaida sama da k’asa bata amsa gaisuwar da take mataba,sai tambayar ta tayi”hala daga awo kike? Fuska a d’an yamutse dan tafara gajiya da irin abubuwan da Asma’un take mata tace”awon me? Asma’u tamata wani kallo me kama da harara “awon me mata suke zuwa yi a asibiti? Tamotsa kafad’a tare da watsa hannu”oho nima ban sani ba tunda ba ta6a zuwa nayi ba.Tawuce randar Inna tad’ibo ruwan sanyi,tashiga d’akin-girki tazuba abinci, tayi bismillah ta faraci.

Inna ta idar da sallar la’asar tajuyo tana shima Sudaida albarka”kin kyauta dakika bata wannan amsar.Ke Asma’u tanuna ta da yatsa”me yasa kike san zama babbar kwabo ne?Asma’u tamik’e”to yanzu Inna me nayi?Ni fa dama kullum a gidan nan a ban iyaba aka d’auke ni.Eh ai halinki yake ja miki.ALLAH yabaki hak’uri Inna ni tafiya ma zanyi,me zaki bani?Inna ta d’aure fuska”ba abinda zan ba ki sai dai in omon wanke-wanken da kika kawo min za ki koma dashi.Kai Inna haba-haba dai,tashige d’akin bacci tana fad’in”ni ai na ga abinda nake so,sink’in sabulu da man shafawa guda d’aya ta d’auko. Inna takalle ta”Asma’u na ba ki ne?Tayi yar dariya tana turawa a jaka”Inna kayan ALLAH ai na annabine,ba sid’i ba sad’ad’a ma kinyi kyauta ga wasu bare kuma ni?Tajuya na tafi Inna,idan Baba ya dawo a gaishe shi.Suka bita da kallo kowacce da abinda zuciyar ta ke rayawa.

Kwanci tashi a sarar me rai…Shekara d’aya da auren su a’isha,Khausar da Nasmat ne suka fara haihuwa,a’isha da Nasmat rana d’aya,ranar suna Sudaida tarasa inda za tayi ga makaranta,ana tashi Kafanchan tawuce gidan a’isha aka sha suna,ba ita taje gidan Nasmat ba sai da akaci aka kusa cinyewa dan ma na ka na kane…a yadda tagaji lik’is d’in nan,gida za ta tabi lafiyar gado.

Tak’arema jaririyar kallo tad’ago cikin murmushi “ALLAH na rasa da wanda tayi kama,ranar da aka haife ta sak babanta yau kuma ta canja batayi kama da ku ba, tamaida ita k’irji ta rungume ta lumshe idanun ta”ina son yarinyar nan ki bani ita mana.Nasmat tayi murmushi”ai dama ta kice na kuma bar miki.Tabud’e idanun ta suka kalli juna sukayi dariya.Nasmat ta kalle ta”d’azu dangin mijin ki bakiji irin habaicin da suke yi ba wai wasu sai dai suci su juye shi a masai,wani abin mamaki kuma Yaya Asma’u itace shugaba,sai da Hajiya ta musu wankin babban bargo sannan sukayi shiru.Sudaida ta d’auki kunun aya tana sha”kar ki wani ce abin mamaki,yau kika san Yaya Asma’u da halinta?A ah ai ni abinda yabani mamakin shin ke d’in ba matsayin kanwar ta kike ba? Tad’anyi murmushi”da ne nake kanwarta lokacin ina gidan mu,toh yanzu kuma ai k’aninta nake aure ina zaune a gidan shi,ita kuma dangin miji ce,wasu dangin mijin kuma ba mutunci suka sani ba.

Asma’un ce tashigo ma da Nasmat farantai takalli Sudaida sama da k’asa cikin ta6e baki “hamshak’iya,maduga ke sai yanzu kika ga damar zuwa? Komu da muke tare da Iyali ai hidimar su bata hana mu zuwa anyi kome damu ba,bare kuma ke da kike zaune ke d’aya ba wata hidima a kanki.Sudaida tayi lallausan murmushi”toh Yaya Asma’u dan ALLAH ina ruwan maza da wankan jego?Abinda tafad’a mata kenan tajuya suka cigaba da hirarsu dasu Nasmat.

Ta koma gida tayi wanka tana so tatafi gidan Inna,kiran Julaibib yashigo tad’aga da sallama”Zaujiii…afwan yanzu nake shirin kiranka “kasha ruwa lafiya?Yau banyi azumi ba Zaujatiii… Bana jin dad’i.Wayyo! Sannu ai naji muryar ka wata iri,sannu kasha magani sai ka kwanta,dan ALLAH yau dai karka tsaya yin wani nazarin karatu,lafiya ai tafi kome.Toh nagode,kin tafi gidan Inna ne?A ah sai nayi sallar Isha’i.Kiyi zamanki ina hanya.ALLAH yatsare, yakawo ka lafiya.Amin,nagode Zaujatiii…Sai kuma tad’an turo baki kamar yana ganin ta”ni dai ALLAH na tsani dawowar cikin daren nan.Yayi murmushi”sai nazo kawai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button