GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Jakar Magori take ji a k’aramar rediyo taji kwankwasa k’ofa,talek’a ta taga sai tagan shi a tsaye. Tabud’e ta k’ar6i jakar shi”sannu da zuwa Yaya Julaibib ina motar?Bazan iya tuk’i ba shi yasa nashiga tahaya.Har ta ajiye jakar bai shigo ba tasake fita sai taga a hankali yake tafiya,yashigo d’akin-shak’atawa yazauna tare da maida kanshi saman kujerar ya rufe idanun shi.Tazauna a hannun kujerar”sannu…ALLAH yasauwake.Bai amsa ba yamik’e wani jiri yakwashe shi luuu…sai ya durk’usa a gaban ta,yadafa gwiwoyin ta dan saura k’iris yasha k’asa. Sannu Yaya Julaibib. Yagyad’a kai ya yamik’e da sauri yafita,tabi bayan shi”Yaya d’ansarai ina za ka?

Abakin famfo yatsuguna yana amai,itama ta tsuguna tana ta jera mishi sannu, yagama aman yabud’e famfo yana taro ruwan da tafukan hannayen shi yana wanke kanshi zuwa fuskar shi.Yad’an kalleta yamik’e dakyar jikinshi a mace kamar yayi awanni yana aikin dabai huta ba,yasake kallanta…yayi magana amma bataji me yafad’a ba,tamatsa kusa dashi “me kake fad’a Yaya d’ansarai?Idanun shi sun k’ank’ance, luuu kawai taga ya tafi zai sha k’asa,a tsorace tarik’o shi wani abu mara dad’i ratsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta,nauyin shi ya rinjaye na ta, gaba d’aya sukayi jikin bango,dakyar yasa hannunshi nadama yadafe bangon, kome yana hautsine mishi,kanshi na mishi matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu,cikin dukan zuciya tafara kiran sunan shi”Yaya d’ansarai… Yaya d’ansarai… Zuciyarta tayi rauni sharrr… Sharrr…hawaye suka fara sintiri a fuskarta,jikinta yafara rawa”Yaya Julaibib ta fara jijjigashi sai tana Istirja’i dan wallahi a tsorace take,tana sake shi ko shakka babu zai zube mata a wajen,gashi baza ta iya rik’eshi gaba d’aya ba, k’arfin namiji da mace bambancin a bayyane yake.

Dak’yar tazame suka zauna a k’asa ta jingina bayanta da bango…tazuba mishi idanu a cikin hasken farin watan tana zancen zuci”gashi bata fito da waya ba bare takira wani daga cikin Yayyinta su zo su taimaka mata,takai hannu tana d’an ta6ashi”Yaya d’ansarai kata shi,Yaya d’ansarai dan ALLAH kabud’e idanun ka ka ji?Bazan iya bane dana kaika d’aki,a hankali yabud’e idanu yad’an kalleta sai kuma yamayar rufe…Tanata kallanshi tana ayyane-ayyane a zuci tana kukan shar6e, wucewar wasu dak’ik’u masu yawa sannan taji hucin numfashin shi me zafin gaske “Sudaida ki daina kuka naji sauk’i.Tahad’iye kukan tana kallan shi ta san fad’a kawai yayi dan hankalin ta yakwanta amma ko wannan hucin numfashin me zafi ai bana lafiya bane”Yaya Julaibib to za ka iya tafiya mutafi d’aki?Yagyad’a kai tamik’e tarik’o hannayenshi duka biyun sannan shima yamik’e suka tafi yakwanta, dan yak’i cin abincin data kawo mishi,shayin ma bai shaba…

Yi dai-dai dan dai-dai,dai-dai ne ba dan wasu sunyi dai-dai ba.

Facebook:سودة ا.باب
Facebook:Bilkisu Ibrahim Bilkisu Ibrahim
Email:Saudatibrahim333@gmail.com

23 Jumaada Thani 1441
17 February 2020

We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJI DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba ( Aadilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na ashirin da d’aya.

Dasafe yayi wanka yana sanye da yadi ruwan madara mara nauyi,yayi lamooo a cikin kujera.Tashigo da sallama tabi kayan abincin da kallo yana nan yadda ta ajiye”Yaya Julaibib har yanzu baka karya ba? Yagyara zama”na d’an sha kunun gyad’an, ina jin bakina ba d’and’ano ne.Tad’ago tana mishi kallan tuhuma bayan ta bud’e kofin”na ce bakaji sauk’iba ka ce ba haka ba,yanzu wannan kunnun an sha shi kenan?Kur6a d’aya kayi ko? Yad’anyi murmushi”afwan Zaujatiii…zan sha anjima.A hankali yamik’e”barin je gidan Inna ko za kimin rakiya?Uh uh adawo lafiya.ALLAH yasa.Ta amsa da amin tabi bayanshi da kallo wata irin k’auna da tausayin shi suka tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarta,bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin na daren jiya ba.Tasauke gwauran numfashi”Ubangiji yasa kaffarace Yaya d’ansarai nah… Takoma d’akin-girki tak’arasa ayyukanta sannan taje tayi wanka ta shirya cikin shigar mutunci da sanin kimar kai kamar ko yaushe tatafi makaranta.

Bayan sallar Isha’i yashigo yana kallanta, itama ta idar da sallah tana azkar,tagama ta mishi sannu da zuwa zata cire hijab yarik’o ta”bar hijab d’in ki muje kimin rakiya gidan Hajiya d’azu ban samu na shiga ba, muna ta hidimar jama’a a shago.Tad’an turo baki gaba”a hakan da ba ka da lafiya me makon kadawo gida kayi kwanciyar ka,kaima kahuta ma ranka?Ai naji sauk’i. Tazuba mishi idanu nawasu yan dak’ik’u sannan tace”tun safe har zuwa yanzu me kaci?Na sha shayi a gidan Inna. Tad’an harareshi”shayi dai shayi dai ai sai kaje kayi ta sha, toh yanzu ga abincin dare na jiranka muje kaci sai mutafi gidan Hajiyan.Yagirgiza kai”bari mu dawo sai in ci yanzu banajin yunwa.

Hajiya tana shan dabgen bindin sa suka shigo da sallama.Sudaida tasa hannu wai wai wai gaskiya matar nan kina sha’aninki wallahi,tagalla mata harara”kema wa yahanaki na ki sha’anin? Sakarya kanki kawai kika sani,toh maza d’auki faranti ki zubama mijin naki mana.Yad’aga hannu”a ah barshi kawai Sudaida bazan iya ciba.Suka zuba mishi idanu”har yanzu jikin ne Julaibibi? Hajiya ta tambaye shi.A ah naji sauk’i Alhamdulillahi.

Ganin ya sake anata hira yasa suka saki ransu.Hajiya ta ajiye tsinken data gama sakacen naman daya mak’ale mata a hak’ori”to ko wannan zirga-zirga da kukeyi ai dole yakarar daku daga kai har matar taka,duk da yanzu na ga tafara sabawa, tana maida jikinta a hankali.Yad’anyi murmushi yana kallan Sudaida”ai Insha-ALLAH zirga-zirgan zai ragu dan an d’aukeni koyarwa a Gidan-Waya, farkon wata me kamawa zan fara zuwa.Hajiya tafad’ad’a murmushinta zuwa dariya”kai Masha-ALLAH…Wow Congratulations.

Suka kyalkyale da dariya”Hajjaju makkatan ashe dai baki manta karatun ba?Inji Sudaida.Tamata dakuwa”ungo nan,mu turancin muma gangariya turawa yan misionaries su suka koya mana baki da baki.Toh Hajiya kingama aji bakwai d’in danaji ance anayi a zamanin da amma bakiyi aikin gwamnati ba?Oh oh k’arya ciwo aji hud’u nayi Baba ALLAH yajik’anshi da rahama yamin aure.Sudaida takalleta cikin natsuwa”toh kema nan kunyi soyayya ke da mijin naki?Hajiya tafara tafa hannaye cikin salati da sallallami.

Sudaida tad’an yamutsa fuska “daga tambaya sai ki fara salati.Hajiya tajawo carbi zata shaud’a mata tamik’e dasauri tafita da kwanan da tagama cin dabgen tawanko hannunta sannan tadawo tana kallan Julaibib daya tsaida gwiwoyinshi yasa duka hannayen shi ya rungumesu,tazauna kusa dashi tad’an marairaice” Yaya d’ansarai anya kaji dad’in zaman nan?Yakalleta me kika gani?Kamar kana jin sanyi…Tabbasss sanyin ne yafara ratsashi amma bai nuna ba,sai yamik’ar da k’afafun na shi yasa hannu yana shafa kwantaccen bakin gashin kanshi “ba kome fa.Tagyad’a kai.Hajiya kuma tagalla mata harara “to iyayin yace me?Julaibib yakalli Hajiya “Sudaida fa amaryace kin kuma san amarya bata laifi,idan kina matsa mata to abu me sauk’i ne tayi yajin zuwa gidan nan.

Takad’a kai tana yar dariya ALLAH sarki wacece amaryar? A in da ba amarya dai a kira ta da hakan,to dan ta daina zuwa gidan nan sai me? Sudaida takalle shi”lallai naji da kunnene dan haka Yaya Julaibib tashi mu kama gabanmu wannan farin watan sai yamana illah gwamma dake Hajiya auren ki da gata.Hajiya tagyad’a kai”ba shakka ai wuyanki ya isa yanka.Suka mata sallama tarako su har zaure “ALLAH yamuku albarka nagode,nagode Ubangiji yabamu alheri, yatashe mu lafiya.Amin Hajiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button