GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Suka jera suna tafiyarsu a hankali suna hira har suka zo gida.Takawo mishi abinci yabud’e yana gani tuwon alkama miyar ku6ewa d’anya,yad’an kalleta a marairaice”Zaujatiii…dare yayi fa…itama ta kalleshi”uhun me yafaru?Yamayar da murfin miyar ya rufe”bai kamata in ci abinci me nauyi da yawa ba tunda kwanciya zan yi.Tayi shiru kamar bataji abinda yafad’a ba.Zaujatiii…ba ki jine?Na ji…amma da kasan baza kaci ba tun farko ai da mun tafima da almajirai suma suci da d’uminshi,takalleshi cikin kulawa”toh yanzu me za kaci?Yasake wani marairaicewa yanata kallanta yak’i magana,ta kyalkyale da dariya dan abin dariya yabata”Yaya d’ansarai wai meye haka kake ta wani kallo na kamar wata bak’uwarka? Me za kacine?Za ki bani abinda nake so?Tana yar dariya tagayd’a kai”ALLAH zan ba ka.To ni dai shayi zaki had’a min kuma dan ALLAH kar kimin mugunta kisa min siga,dan haka take mishi wani lokacin idan ba taso yasha shayin shi kuma ya nace sai yasha.

Angama autan Inna”ke zo nan dawa kikeyi ne? Tashige d’akin-girki da wanda ya tsargu nake yi.Taje tahad’o kofi biyu tamik’a mishi d’aya ta rik’e d’aya yabita da kallan k’arin bayani,tagyad’a kai “tayaka shan abinda kake so zanyi ko ban kyauta bane?Yayi murmushi”kin kyauta mana,tad’ibo donut tabashi amma baici ba haka yasha na shi,itace dai taci guda d’aya suka gama takai kayan d’akin-girki sukaje suka wanke baki sannan sukayi shirin bacci.

Cikin sulusin daren yaketa juyi dan ya kasa bacci,yatashi yazauna,yakoma yakwanta yayi hakan kusan sau biyar,har bacci yafara d’aukeshi yasake tashi zaune yakama kanshi da duka tafukan hannayenshi abin ba sauk’i wai ciwon arna,wani zazzafan zazza6i yarufeshi sai kuma sanyi yafara ratsashi”Sudaida…a hankali yafara kiranta ita kuma baccinta yayi nisa,yakai hannu yana d’an bubbuga k’afarta Sudaida…kamar a mafarki taji kiran tayi juyi sai tasake jin kiran tabud’e idanun ta taganshi jingine da gadon yana cigaba da kiranta,dasauri tamik’e zaune kamar zata hantsila zuciyarta na bugawa da k’arfin gaske tayi Istirja’i”Yaya Julaibib wai meke faruwane?

Wani irin ciwone haka sai cikin dare? Yadamke hannunta gangam Sudaida sanyi nake ji rufeni.Tagyad’a kai” tabbasss garin akwai sanyi ga sanyin farin wata daya haske doron duniya kaafatan, dole mara lafiya yaji sanyi,to amma jikinshi yayi mugun zafi kuma yana jin sanyi to bai kamata kuma a rufe shi da abu me nauyi ba dan ba a so zafin yakoma jikinshi.Yana karkarwa yace”Sudaida rufeni sanyi nake ji,dakyar yayi furucin,tamik’e ta d’auko zanin a tamfa ta rufeshi. Yagirgiza kai”ban daina jin sanyin ba d’auko bargon mana,ta lalla6ashi yakwanta”yanzu zan d’auko kaji?Tarik’o hannunshi”kayi hak’uri Yaya d’ansarai tajik’a k’aramin tawul a ruwa tana fara goge mishi jiki yarik’e tawul d’in tamauuu”kyaleni bana so,kwanta kiyi baccin ki.Takwanta tanata kallanshi har wani baccin wahala yad’aukeshi dan daga ganin yanayin fitar numfashin ka san baya jin dad’i.

Yashigo da sallama yazauna a kujera yana kallanta har ta idar da sallar,ta sunkuyo tana mishi sannu da jiki tana ta6a jikinshi har yanzu da zafi, a ranta tana yaba k’ok’arinshi dakyar yayi alwala saboda ciwon kan bai sake shiba,amma a haka yagangand’a yatafi masallaci dan samun jam’in sallar asubahi”ALLAH gari na dad’a wayewa asibiti zamu tafi,ni ciwo cikin dare tsoro yake bani.Yayi yar dariya”tsoro kikeji kar in mace miki? Sudaida ai ko da rana idan lokaci yayi tafiya zan yi. Tamishi wani kallo dayaji tasirin shi har a zuciya”ni bana san irin wannnan kalaman fa gaskiya,cuta ai ba mutuwa bace, wata kilama ni zan rigaka macewa,ba dai wanda yasan gawar fari”ALLAH dai yasa mucika da kyau da imani.Amin Zaujatiii…yazame yakwanta yanata kallanta tana shige da ficenta har wani bacci yasake awon gaba dashi.

Sai da tagama shiryawa sannan ta tasheshi yaje yayi wanka su tafi asibiti.Yamaida kanshi saman kujera yana kallanta cikin shigar doguwar rigar atamfa da dogon hijab me hannu”ba makaranta za ki tafi bane?Can ne amma sai mun gama da asibiti zan wuce.Yamik’a hannu yakar6i jakarta yasa mata kud’i a ciki yamik’a mata,tasa hannu biyu takar6a tana godiya “ALLAH yak’aro bud’i Yaya Julaibib.Yayi murmushi kawai sannan yamik’e muje in taka miki.Takalleshi kayi wanka dai mutafi ko? A ah naji sauk’i fa ni anjima kad’an ma Kafanchan zan tafi.Takalleshi wani iri kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru.

Yau da wuri tadawo sai kawai tawuce gidan Inna suka sha hirar su Inna tamusu faten tsaki sai bayan la’asar tamata sallama takoma gida,tana ganin kiran Julaibib tad’aga a kame sallama kawai tamishi tayi shiru”Zautajiii…kin dawo daga makaranta ko kina can in biya in d’auko ki.A takaice ta amsa”nadawo.Lafiya kuwa?Tasake amsawa da”Uh batare data bud’e baki ba.Baki da lafiya ne najiki wata iri”k’alau nake.Yasauke numfashi”toh shikenan ganinan zuwa.Ta amsa da uhun.

Taje tayi wanka tana zaune a gaban madubi tana kwalliya ya shigo da sallama ta amsa sallamar tare da mishi sannu da zuwa tacigaba da abinda takeyi bata wani damu da ganin shiba,yanad’e hannayen shi a k’irji yana k’are mata kallo,yau ta mishi kyau fiye da kullum,yak’arasa wajen ta da karsashi “Zaujatiii…kinyi kyau fa.Ganin ya d’okantu da ita yasa tad’an tsuke baki kamar me shirin yin fito,kamar bataji abinda yafad’a ba tacigaba da shafama la66anta jambaki ruwan hoda.

Sai yad’ora mata ledar raken a jikinta”ga mutumin ki.Tad’anyi tsaki. Yabita da kallon nazari”tun a waya nakiji wata iri yanzu kuma tsakin me kikeyi Sudaida?ALLAH dai yasa banine na 6ata miki rai ba.Tad’an harareshi tana k’unk’uni.Ke karki sani a uku fa kin san ina k’aunarki.Ganin ta mik’e zata bar d’akin yasa yarik’ota da sauri sannan yakalleta cikin natsuwa”fad’a min laifina zan baki hak’uri,durk’usama wada ba gajiyawa bane.

Haushin shi yakamata”na rantse maka da girman ALLAH idan bakazo munje asibiti ba to ko ciwon ka yatashi cikin dare ni karka tasheni ina tsaka dajin dad’in bacci na eheee,yasan za a rina…wannan fushin,haba-haba dai ke kuwa ya zaki fad’i haka? Yanzu lalurata ba taki bace?Takwace hannayenta tana turo baki gaba”eh batawa bace,ta kace kai kad’ai dan haka kaje kaji da ita kai kad’ai tunda na baka shawara baka jiba…Yayi yar dariya”kinga to kisha kuruminki Sudaidan d’ansarai yajata suka zauna a kujera sannan yaciro ledar magani da d’an k’aramin katin shi na ganin likita”duba kigani”daga asibiti nake abinda yasa ban dawo da wuri ba kenan,likita yamin test,wai typhoid ke damuna ga magungunan daya bani da allurai”anjima bayan sallar Isha’i za ki rakani allurar,kin san bana son allura idan nak’i tsayawa sai ki d’an bud’e idanun ki nan da nan sai kiga na tsaya amin ba tare da ankai ruwa ranaba ko kuwa?Tayi dariya”lallai kuwa wannan shine ta6ara megida da kukan yunwa.

Tad’auki rakenta tafara sha da bismillah”da fa yau har yajin shan raken nan zanyi da bakaje asibitin ba.Ke d’in kuwa?Ke mayyar rake ce kuma ban ta6a k’in siyo miki ba,amma ni idan nace ki had’a min shayi sai kawai ki kama fushi wai bazan sha bak’in ruwa ba to haka a ke rayuwa?Kowa ba da abinda yafi so ai ko kuwa? Tajijjiga kai”ka fini gaskiya, toh kayi hak’uri na dai fushi da shan bak’in ruwa… Tawani shagwa6e”nima ai gashinan a hankali na fara koyan sha,shekaran jiya ba tare muka shaba? Yagyad’a kai”Yau me kike dafa mana be?Tad’an kalleshi”ni fa da bazanyi wani girki ba,idan zamuje allura muje gidan Inna kaci tuwo ni zan sha Yoghort dan bana jin yunwa.Yamik’e”to shikenan,yatafi d’auro alwala dan anfara kiraye-kirayen sallar magriba daga mabambantan masallatan unguwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button