
A sanda hantsi yadubi ludayi rana ta haske ko’ina na safiyar talata,tana zaune a in da ta idar da sallar walha Hauwa’u tashigo tana fad’in”ina wannnan mijin naki me bak’in idanu da ba ya san zuwa gaisheni? Abokan wasa suke da Julaibib Ya’ya maza amma tasu da Sudaida ta zo d’aya,suna mutunta juna.Sudaida takama ha6a”yanzu mijin nawane me bak’in idanu Hauwa’u? Tajijjiga kai ‘tabbasss,to ni duk zuri’ar d’ansarai da wanda yafishi bak’i ne?Sudaida tad’an harareta”lallai daga yau na san in da zan ajiyeki tunda kike cima rabin raina fuska a gaban idanuna,to amma kuma kyau tsagwaron shi da wanda yakama k’afar Yaya d’ansarai nahhh a duk zuri’ar Doctor Julaibb d’ansarai? Bata bata masa ba taje tad’auko lemun peach.
Sudaida tawatsa hannaye”ahab ni dama na san irin abin nan ne na na makaho da yace ido da wari.Hauwa’u tayi murmushi”mu ai gaba d’aya a zuri’ar Doctor Julaibib Abdullahi d’ansarai kyawawane.Sudaida tagyad’a kai”muma ai hakan take a zuri’ar Ibrahim Me-Lambu.Sukayi dariya sannan suka gaisa suna hirarsu ta yaushe gamo dan sun d’an kwana biyu basu ga juna ba saboda yanayin karatun Sudaida da baya barinta zama a gida musamma tada fara karatun degree.
Hauwa’u tafara ba Sudaida shawara”ku k’ara komawa asibiti mana ko wannan karan ALLAH zai sa a dace.Takalleta cikin natsuwa”Hauwa’u a asibiti ake ba da haihuwa?Tagirgiza kai”ba a asibiti bane,amma idan kunje d’in ai zasu k’ara dubaku,idan har yanzu ba me matsala a cikin ku za su iya canja muku magunguna da k’arin yan shawarwari ko kuwa? Tagirgiza kai”uh uh ni dai bazan koma ba,sauran magungunan ma na daina sha shekaran jiya na zubar dasu nagaji da shan k’waya kullum kwanan duniya bayan an tabbatar mana lafiyar mu k’alau, na fauwalama ALLAH duk yadda yayi dai-dai ne.
Duk san mu da haihuwa idan ALLAH bai k’addaro mana ita a rayuwarmu ta doron duniya ba, toh fa bawani magani da dabaru da likita zai bamu da za suyi amfani,tad’an yi murmushi”ki cigaba da tayamu da addu’a itace babbar makamin mu.Hauwa’u tarik’o hannayen Sudaida cikin k’auna da tausayi “wannan halin na ki na maida al’amura wajen ALLAH me kowa da kome yasa nake dad’a k’aunarki,addu’a ina tayaku da ita kuma zan k’ara,Ubangiji yamana jagora ya iya mana kar yabarmu da iyawarmu dai-dai da k’iftawar idanu.Amin Hauwa’u.
Asma’u tashigo da sallama tana musu wani malalacin kallo ganin hannayen su a had’e”to fa wani sabon salo ne wannna zuwa karuwanci da uwa? Hauwa’u ta amsa”eh mana to ya san ranki Ma’u?Kafin tayi magana Habiba Yayar Hauwa’u tashigo,tafad’a kujera tana wata yatsina wai ta gaji daga shagon d’inki take.Asma’u takar6i ledar ta zazzage kayan”toh bari muga style,material ne da da leshi kuma d’inkunan sunyi kyau sosai,wai ankon sunan da za ayine idan ta haihu.Hauwa’u ta d’auki material d’in tana dad’a gani dan shine ya burgeta “gaskiya da ina da kud’i da sai na yi shi.
Asma’u tace”tunda baki da kud’in wannan ai akwai atamfa ta yaku bayi,dama ai dai-dai ruwa dai-dai k’urji.Habiba ta cafe”ah to shi mutum ba zai tashi ya nemi na kai ba,kome an dogara da miji har abinda ba wajibinshi ba a gida yakamata Iyayenshi su mishi amma basuyi hakan ba,kai ni wannan rashin tausayi dame zan kwatantashine?Kome dai miji?Taja dogon tsaki,toh gwamma dai mutum yasani shi mijin nan ba dan mace d’aya aka halicceshiba,ko bajima ko ba dad’e dole wasu mata ukun da izinin ALLAH sai sun shigo an dama dasu suma.
Sudaida tayi tsaiii…cikin nazarin kalaman Habiba,babu kome a cikin su daya wuce shagu6e. Hauwa’u da bata gano dawar garin ba tace kai”sharri dai ba kyau wallahi,kuma kun sani ai ina sana’a sai dai banyi k’arfi bane,yaro kuma ai da rarrafe yafara,ni kuma dan san a sani yaji da kwarin miji da banten suriki da d’an masu gida bazan kwashe jarin nawa dan yin ankon suna na rana d’aya in dawo in tsuguna ba,kuma da kuke maganar kome miji toh dan girman ALLAH wace macece a doron duniya da baza taso ace kome mijin na tane yake mata harma da wanda iyayen nata suka kasa mata ba?Kudinga adalci a kalamanku fa…Asma’u da Habiba suka kalli juna suka kyalkyale da dariya Asma’u tace”ballagaza bankaura, sakarai ba ta da wayau…inji Sa’adatu(Barmani Choge)
Sun so wacce sukai hakan dan ita ta tanka amma sai batace kome ba tashige d’akin baccinsu tad’auko material da leshi launinsu d’aya dana Habiba sai dai zanen jiki ya bambanta,tana fitowa ta d’orama Hauwa’u a cinya”gashinan ki d’auki d’aya,wannan karan dai na ceceki,dan haka daga yau ki tashi haik’an da niman kud’i dan ki huce takaicin zamani,duk da dai na ga zafin nema ba shi yake kawo samu ba,haka kuma dare d’aya ALLAH kanyi bature, indai kina da wadatar zuci to abun kowa bazai tsone miki idanu ba.Hauwa’u Tajijjiga kai “tabbasss zancen ki dutse.
Tabi kayan da kallo”kai ko wanne fa ya d’auku,sai dai kawai in rintse idanu in d’auki d’ayan. Sudaida ta koma ta zauna”toh barinyi maganin ruwan idanunki kawai,kirik’e su duka na bar miki.Hauwa’u tad’an zaro idanu cikin mamaki”duka na wa?Kin barmin? Sai tafad’ad’a murmushinta zuwa dariya”kai masha-ALLAH jazakillah khaira-khaira jaza’ih…ALLAH yabarki da Alhaji d’ansarai me bak’in idanu har gaban abada.Takallesu ku tayani godiya mana.
Zuciyar Asma’u ta gama tafarfasa har ta k’one,ankon fa takema d’ansarai magiya yamata yace shi bashi da kud’i shine yanzu matarshi har take kyauta da kala biyu,itafa d’aya ma tace mishi tana so..Lallai wanna akwai shegiyar yarinya wato kome na shi ya tattara mata kenan?Taja tsaki”itama Inna tana da matsala(????kunji fa)wai idan an fad’a mata sai tace wannan dai sa’idanune a abinda bai shafe kaba, ita ba matar shi bace?Ai ko ba aure a tsakaninsu yan’uwan junane,kuma duk Ya’yantane,tanuna Asma’u da yatsa”wallahi kina tare da wahala idan baki bar wannan banzan halin na kiba,ke wayasan damfarar da kike ma mijin ki da wannna shegen wayan na ki?Tasake jan tsaki Inna bazaki gane irin bautar da yakema wannan yarinyar ba wallahi dan ba kyau zuwa gidan nan kina gani ganin idanunki ne.
Habiba ce taja dogon tsaki”kina ta wani zuba godiya kamar wacce a kamata gafara,ba fa sai kin gode ba tunda kowa ya san ai k’oshin wake na ruwa ne,da kud’in d’an uwanki d’ansarai aka siyesu, kuma ko ke zai iya sai miki wanda suka fisu ma… Hauwa’u ta tari numfashinta”a ah wallahi k’arya da ciwo gyambo da wari.
Sudaida tayi dariyar tura haushi”ah toh gwamma dai da kika tuna mata,takalli Habiba tana murmushi”wad’annan da kike ganinsu tanuna kayan data ba Hauwa’u ni na siyesu da kud’i na,ai idan zan siya da kud’in Yaya d’ansarai toh bazan sai wad’annan masu rangwamen farashin irin ta gama-gari yakubayi ba,tunda kud’in ni nake zamansu.
Kufa yan uwane ba dole ne ya mukuba,sai dai yayi dan kara yasamu ladan zumunci, idan kuma yak’iyin haka ba wanda zaice dan me?Kuma ko a wajen ALLAH bashi da laifi ko na sisin kwabo tunda ku ba a hakk’unshi bane,ni ce nan tanuna k’irjinta da kwibinta ni ce k’ashin hak’ark’arinshi,kinga ni ce nazama dolenshi, wallahi idan ana san zaman lafiya dani toh fa sai na fad’i irin wanda nake so,idan an kawo naga kalar bai min ba dole yakoma yaza6o wani, ko kuma in ce yad’ibo su da yawa in za6i wanda suka kwanta min a rai…Habiba ta tari numfashinta”tabbb ai ko baki isa ba,tamata wani kallan uku ahu kai… ALLAH ko ya isa da wannan iko sai kace ke kika kawo shi duniya.