GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Sudaida ta kalleta cikin kukawa”Habiba kenan kisa ranki a inuwa dan ko ba iko dama ALLAH ai ya isa da kome,shine dama me kowa da kome na doron duniyar nan. Asma’u tamik’e”ke fa yarinyar nan wato salan mulkin ki kenan ki hana mutum rawar gaban hantsi ko? Batayi niyyar maida martani ba to amma Yaya Asma’u ta dad’e tana shiga mata hanci da k’udundune ya kamata ta fyaceta,kuma kunyar mara kunya ai asarace,idan babba ya yadda girman shi to ai ba laifi bane dan an taka.

Sai tagyad’a kai”ai kuwa dai Yaya Asma’u na zama kuturwar uwa zama dani dole,kuma duk wanda zai zauna dani d’in to d’aurin gwarmai nake mishi.Habiba da take ji kamar ta shak’e Sudaida dan haushi tace”to ai barewa baza tayi gudu yar ta tayi rarrafeba.Sudaida ta kyalkyale da dariya”ai dama kyan rawa da makar6i,kyan d’an yagaji ubanshi. Asma’u tafara tafiya “to Sudaida na yi gida amma dai kiyi a hankali dan ni bazan mulku ba, idan kuma kika matsa da yawa to abu ne me sauk’in gaske cire wando taka inyi waje dake.tak’arasa fita ba dan bata da sauran abin fad’a ba,a ah sai dan kar k’ilu taja bauuu…ga Hauwa’u nan itama munafuka ce idan anzo maida magana Sudaida za ta goya ma baya sai a d’ora mata sata da maitar,amma lallai sai tasa Dannarai ya k’ara aure, itama Sudaida ta so data tsaya ta ba ta amsa dan haka duk sunji ciwon kalaman juna.

Tacire hannun Hauwa’u da tayi tagumi dashi tana kallan su kawai,ta kashe ta da lallausan murmushi tunda ance iya ruwa fidda kai.”kiyi hak’uri ba kud’i a hannuna amma idan bafade na autan Inna yadawo ranar jumma’a to zan turo miki shi wallahi har gida yazo yabaki kud’in d’inki dana takalmi da hijab,dan kin san ni a gidan nan k’arfine dani na gaban shari’a kum…Hauwa’u tasa tafin hannun ta rufe mata baki”dan girman ALLAH ya isa haka Sudaida.

D’akin-shak’atawar ya d’auki shiru na wucewar wasu yan dak’ik’u.Habiba tayunk’ura tamik’e cikin fushi bata musu magana ba tayi hanyar fita.Sudaida tad’an d’aga murya”toh uwar biyu sauka lafiya sai kin kiramu,ALLAH yaraba lafiya.A ciki ta amsa da”uhun.Tana fita Hauwa’u ta kyalkyale da dariya”matar d’an Sarai yau kin burgeni.Takad’a kai”ni har ga ALLAH banyi niyyar kula suba to amma naga abun na su yana neman wuce gona da iri ne,shiru-shiru kuma ai ba tsoro bane gudun magana ne”dodo d’aya akema tsafi,ba su suke aure na ba Yaya d’ansarai ne dan’uwan ku,duk fad’in mutanan doron duniya idan za suce yarabu dani idan yana so na,yana san zama dani to ba wanda ya isa ya rabamu,tunda ba wanda yake mishi auran nan,shi d’in da kanshi yake abinshi,haka kuma idan yace ba yayi ba wanda zai tilasta mishi zama dani.Hauwa’u tajijjiga kai “tabbsss zancen ki dutse”ALLAH yashirye su da sauran dangin miji masu mugun hali na mugunta “abun wani banza na su dukiya.

Tana kallan shirin Akhbar-Al’an tana cin awarar madarar shanu Khadija yar Khausar tashigo da gudunta cikin d’oki tafad’a jikinta”Inna Mamace tace in zo in tambayeki wai anjima za tayi tuwon shinkafa miyar shuwaka,shine tace wai a k’aton kwano guda nawa za a zuba miki? Sudaida tayi murmushi ta san wayau aka mata, kafin tayi magana kiran Khausar yashigo”Nana Khadija ta k’araso kuwa?Eh gatanan ta kuma fad’a min sak’on,ina za ki?Asibiti zan kai Misbahu ta kuma na ce dole sai munje da ita.Wayyo! Har yanzu jikin ne?Shine Sudaida daren jiya kusan kwana mukayi bamuyi bacci ba saboda kukan shi. Toh ALLAH yasauwake zan shigo anjima idan kun dawo. Sukayi sallama.

Inna me zan fad’a mata?Takalleta da kulawa”bari sai anjima idan nayi wanka sai muje can muci ko?Toh Inna amma kamar kinyi wanka ga shi kina ta k’amshin irin turaren Baba d’an Sarai,ina son k’amshin. ALLAH Khadija?Khadija tayi d’an tsallan murna kamar yadda yara keyi”ALLAH Inna,to maza shiga d’aki ki d’auko kema in fesa miki,da gudunta ta d’auko Sudaida tafesa mata.Nagode Inna.Tad’an kama ha6arta”yauwa Khadija ga yoghort can kije ki d’auka,tad’an mak’ale kafad’a”Inna ni dai nafi son Caprisonne.Tamik’e shikenan muje in baki.

Sudaida tazuba mata idanu cikin tasbihi ga Ubangiji,k’udurar ALLAH dayawa take,wai yaushe-yaushe akayi auren su amma gashi har an haifi yar da za a aikota daga wani gida zuwa wani gida da k’afafunta da bakinta”oh ALLAH kaine ALLAH.Sharrr…sharrr…hawaye masu d’umi suka zubo mata”anya za taga gudan jininta a doron duniya kuwa?Ta rungumeshi a k’irjinta yaji d’uminta na uwa itama taji d’uminshi na d’a?Ta tuno da bak’ar magana habaici da dangin Julaibib suke mata,wanda in dai da mutum shi yake da ikon ba kanshi haihuwa to kuwa da tayi zuciya ta haifo musu yan hud’u a haihuwar farko,to ina ALLAH ne,ba kuma a mishi dole…tasake tuno kalaman Inna,Mama,kai rannan har Umma sai da tadinga kwantar mata da hankali akan dai tayi hak’uri tayi hak’uri,kullum haka suke fad’a mata musamman idan sun ganta cikin damuwa ko da ba wannnan ne abinda yake damunta ba “kiyi hak’uri Sudaida hak’uri kan tadda rabo,wata rana sai labari..

Khadija tamatsa wajenta”kukan me kikeyi Inna?Waya dake ki?Tarungumeta kawai tacigaba da kuka Khadija na tayata,sai da sukaci suka k’oshi dan kansu sannan sukayi shiru a hankali kuma bacci yayi awon gaba dasu.

Kiran wayar Julaibib yatashe ta daga bacci”wash ALLAH Zaujiii…yatare ta da sauri”me yafaru ne Sudaida?Tayo k’asa da murya”ba kai bane ina cikin baccina me dad’i ka tashe niba.Yayi murmushi”to fa tawa tasameni kenan malami da tallan jigida,kiyi hak’uri ki koma baccin anjima mayi magana.Uh uh ai kuma ko na koma baccin ba lallaine yazo ba sai dai in ta juyi”goben zaka dawo?Na so haka to amma bazai yiwuba dan gobe muna da serminar a jahar Katsina idan na dawo kuma akwai jarabawar da zan ma d’alibai,nima na so zuwa dan zan ba Inna wasu kud’i,amma barin miki transfer idan kika ciro sai ki kai mata,yanzu zan kira ta in mata bayani.Ranta bai mata dad’i ba amma ta daure ta amsa da to tare da addu’ar ALLAH yakiyaye hanya,sukayi hirarsu ta kewar juna sukayi sallama.

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba tabawa ranar sa a,Nasmat tazo gidan,suka rungume juna”oyoyo Nasmat…Sudaida ta d’auki Ahmad tana mishi wasa shi kuma ya bud’e wawulan bakinshi yana kyalkyala dariya.Nasmat taje tad’auko lemun sprite tabud’e tana mita “Sudaida kin zama abinda kika zama wallahi,abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tamata kallan k’arin bayani…Nasmat tagyad’a kai”in dai na zo gidan nan ni zan ba kaina ruwa ko abinci?Haka ake ma bak’o?Taja tsaki”na d’auka wani laifin nayi to kar kisha ruwan mana cikin wa zai shiga?

Takama ha6a”kar dai zama da mad’aukin kanwa Yaya Asma’u ya sa kema kin zama abinda kika zama? Haushi yasa Sudaida tak’i magana tanama Ahmad wasa yana cigaba da dariya.Itama tamik’e zuwa wajan taga tana amsa waya,tagama wayar tad’an kalli dai-dai kun mutanen da suke kai-kawo a safiyar sannan tacema Sudaida”na biyo miki ne muje duba yar gidan Yaya Asma’u da jiki.Hu’un tafad’a ba tare tadata bud’e bakintaba.Menene kuma hu’un?Nasmat ta tambayeta.Tamik’e zaune daga kwanciyar da tayi tad’ora Ahmad a cinya”ke ni fa bazani in da raina zai dinga 6aci a banza ba,dan na riga na k’una bana tsoron wuta.A ah Sudaida kiyi hak’uri kawai idan an miki kan kara karkice za kiyi na itace.Tayi wani huci cikin kad’ai”ai na rantse da girman ALLAH ni yanzu har na gungume zan iyayi yadda zai shekara yanaci,kawai sai tarufe idanu tana zazzaga fad’a,Nasmat bata kar zomo ba amma an bata rataya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button