
Tazuba mata idanu har tayi tagaji dan kanta tayi shiru,sai kuma tayi kwafa”banda ina duba darajar yan’uwantaka da dangantaka kinaga zan bar Yaya Asma’u tacigaba da cin dunduniyata tana min hawan k’awara yadda taga dama?Nasmat tagirgiza kai sannan ta amsa cikin natsuwa”a ah baza kiyiba, to amma karki manta hak’uri kan tadda rabo…idan ka gaida wada da tsawonka zaka mik’e…Sudaida ALLAH yana son masu hak’uri masu had’iye fushi,da dama su rama abinda aka musu amma sai suyi hak’uri ba saboda kowa da kome ba sai saboda zatin ALLAH… Tacigaba da rarrashinta har fushin daya mamaye zuciyarta yalafa,ta kuma yi nasarar janta suka tafi dubiyan…
Da kunu da miya har abadan duniya ba za su had’uba sai dai a cikin ciki.
27 Jumaada Thani 1441
21 February 2020
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na ashirin da biyu.
A wulak’ance da halin-ko-inkula kamar yadda tasaba haka yauma ta amsa gaisuwar Sudaida, amma tanata jan Nasmat da hira suna shirin tafiya sai ga Hauwa’u itama ta zo dubiya,suka tsaya ana gaisawa, Hauwa’u tamatsa kusa da Sudaida “yar’uwa yayane jikin ne ko garin ne,ko wannnan bak’in mijin na kine dayaje yashare waje a Gidan-Waya?Takai mata duka a kafad’a,tagoce da sauri yabi iska.Kin sama mijina rabin raina idanu fa,meye darin gamarki dashine wai?Asma’u da wata k’awarta yar duniya me irin halinta sukayi dariya suka tafa”haka fa kullum ana nuna ana k’aunar miji amma an k’i nuna mishi k’aunar a zahirance,ta hanyar barin Ya’yanshi suzo su shak’i iskar duniya,takad’a kai cikin ta6e baki”kullum ana ba mutum amma har yanzu ya kasa yin zuciya yak’ar6a ko da sau d’aya ne,sai dai ayi ta asara,a wanke abun yabi rariya.
Hauwa’u takalleta”ke wai Asma’u kullum ba ki da abinyi sai gori?Sannan ma dake ake magana me ko ko ita tace miki ba tajin dad’i?!Nasmat ma ranta ba dad’i tace”haba Yaya Asma’u wannan ba girmanki bane wallahi,kin san duk me gori matuk’ar bai tuba ba to yana haramtama kanshi rabon alheri ne a lahira, sannan wannnan gorin ma d’an Adam d’in doron duniya ba shi da iko akanshi,wannan ba huruminki bane Yaya As…kafin tak’arasa sai ga Hajiya tashigo d’akin tana d’agama Nasmat hannu “dakata Nasmat in dai gori ne ta tara ta samu, Hajiya tanuna kanta”ni d’in nan yau har goruba zan mata, zanyi maganin iya shegen nan k’auri da kare.
Tayi d’as d’as d’as da yan yatsunta”ki bud’e kunnuwanki da kyau ki saurareni,na rantse miki da girman ALLAH in har Sudaida bata haihuba to ba itace ba ta haihuwaba,k’aninkine Julaibibi,matan kakanku ai su biyune uwargidan shice mahaifiyar ubanki,su uku tahaifa,amma amaryar shi sai da ta haifa mishi Ya’ya goma shabiyu, ubanki gashinan shima Ya’ya uku yahaifa,d’aya kanin na shi yahaifi Ya’ya biyu, d’ayan kuma ai har yakoma ga ALLAH bai haihuba,matar shi data gama takaba tayi wani auren bagata can da Ya’ya bakwai ba?
Karima Yayarki Ya’yanta biyu,ke kuma yarki d’aya jallin-jal kamar rai,sai 6ari da kika ta6a yi sau d’aya duk shekarun da kukayi a gidan miji,mata nawane ta dangin kakar ta ku ga sunan a gidajen miji ba haihuwa sai dai suci su k’oshi suje masai su juye kayansu?Ai suna da yawa saboda ku ba irin haihuwa bane,toh Sudaida fa?Su goma sha takwas ne a gidansu,kuma duk cikin Ya’yana ba uwarki ce kawai me Ya’ya uku ba?Tanuna ta da yatsa”to dan haka ahir d’inki hawainiyarki takiyayi ramar Sudaida, kuma ko yanzu da k’anin na ki zai rabu da ita,toh idan ma na rantse ba kaffara a kaina bazata rufe shekara a wani gidan auren dazata yiba za ta haifo gudan jininta takuma sa zani tagoye abunta,ai ga sa’o’in auren na ta nan kina ganinsu ganin idanunki kowaccensu ta fara kafa na ta Iyalin…
Tambayar me jikin da batayiba kenan ta ajiye ledar ayaba da lemun tajuya cikin fushi”jahilar addini kawai wacce bata yadda kome muk’addari ne tun daga lauhul-mahfus ba,na rasa a ina kika d’auko wannan bak’in halin na ki,banda ma ke shimmeruwa uku ce(sha-sha-sha)Sudaida ba yar’uwarki bace da zaki iya tare mata fad’a a inda kikaga za a wukak’anta taba?Toh karki daina abinda kikeyi ai hassada ga me rabo ta kice…Nasmat da Hauwa’u sukayi lallausan murmushi suna shima Hajiya albarka”ALLAH yak’ara girma me amfani Hajjaju makkatan…kaza dai garin tuno-tone take tono wuk’ar yanka kanta…baki shi ke yanka wuya.Sai da Hajiya tabar gidan sannan Asma’u tafara nad’e tabarmar kunyarta da hauka.
Da wannnan 6acin ran Sudaida tawuce ATM taciro kud’in da za ta kaima Inna,sukayi kaci6is da Aminu shima ya zo ciren kud’i yabud’e mata murfin motar”shigo ki jirani tunda yau na ga ba layi.Dak’ik’u basu wuce goma ba yadawo.Yaya Aminu gida za ka koma? Yana tayar da mortar yake amsawa “Jos zani,amma ke zan mayar gida wani abune?Tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sharrr… “mutafi kawai sai ka saukeni a Gidan-Waya.
Sun d’auki hanya sosai sannan yajuyo cikin kulawa yakalleta”wai yau waya ta6a kanwata rabin raina ne?Tad’anyi murmushi”share kawai Yaya Aminu ni da Yaya Asma’u ce.Yakama ha6a wuuu… Asma’u ciwon idanu sai hak’uri,ai ko jiya danaje dubiya nima sai da muka hau sama muka fad’o,wai nayi kud’i bana son zuwa gaisheta,kinji sai kace wata Yayata.
Sudaida takawar da zancen ta hanyar tambayar Siddiqa nan da nan ko yayi lallausan murmushi suka shiga hirar arziki har suka iso Gidan-Waya,har k’ofar gidan da Julaibib yake yakaita anan rukunin gidajen malamai,yasake kallanta cikin kulawa”Sudaida kiyi hak’uri na san kinayi amma ki k’ara wata rana sai labari,ai duk abinda yayi farko to tabbasss yana da k’arshe,wallah-azim da ana siyan haihuwa da kud’i toh dana sai miki kome tsadarshi,toh ina abin na ALLAH ne “ance da kare me sunan maza.Tajijjiga kai”na sani Yaya Aminu na kuma gode, duk cikin Yayyina kaine taurarona”Ina sonka sosai.Sukayi murmishi”nima nagode kanwata rabin raina data za6eni sama da kowa a matsayin tauraronta,toh me kike so in siyo miki a matsayin tsaraban mutan Jasawa?Tagirgiza kai”bani da za6i kasiyo min ko menene nagode.
Yayi yar dariya”tunda kin bani wuk’a da nama Insha-ALLAH za6in nawa zai burgeki,idan nadawo zan shigo in baki tsaraban,sai in kar6i kud’in da kikace zan kaima Inna,kiyi hak’uri ko?Nagode Yaya Aminu tabud’e motar tafito,tarufe mishi”adawo lafiya ALLAH yatsare,suka d’aga hannu suna ma juna adabo.Tabi danjojin motar da kallo har ya6ace ma ganinta.Tarik’e k’ugu tana fesar da iska ta baki ta hanci sannan tasa hannu a jaka ta d’auko mukullin gidan tabud’e tashiga.
Wani k’amshin turaren d’aki da sassanyar iskar da take shigowa ta tagogin da suke bud’e yamamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta,sai taji ta samu natsuwa ta lumshe idanunta tana jan numfashi”Yaya d’ansarai wallahi me tsabtane,ji yadda yazauna yagyara gidan kamar mace. Tashige d’akin bacci,tazauna a gefen gadon tad’auki wani d’an k’aramin hotonta da ya ajiye a dirowar gefen gadon,ta d’auki hotonne a wani excursion da sukaje a Wadom akan harkar gona tun tana aji biyu a k’aramar secondary,tak’arema hoton kallo tana tuno irin kyan da Julaibib d’in yace wai tayi…Wanda ita dan haushin irin munin da tayi ta turo baki gaba zata yaga sai gashi ya shigo gidan shine yakar6a,tamaida hoton ta ajiye tana murmushi ita tama manta ta ta6ayin hoton.