GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yaya d’ansarai ALLAH yakiyaye hanya…

Tad’an sunkuya tabashi sumba sannan tayi furucin da wani salon shagwa6a”sai munyi waya ko?…tajuya tayi tafiyarta dan tasan ba magana zaiyi ba in dai yayi wannan sunkuyar da kan”sanin hali ai yafi sanin kama.

Yabita da kallo yana lallausan murmushi yayi d’as da yan yatsunshi”hak’ata zata tadda ruwa Insha-ALLAH ai ni dake mutu karaba yarinya.Yakalli agogon dake d’aure a hannunshi na dama,lokaci yaja a gurguje yagama karyawa,yad’auki jakar shi ta matafiya ya rataya a kafad’a da mukullin mota yakulle gidan yana addu’ar fita daga gida”bismillah tawakkaltu alallahi walahaula walaquuwata illah billah.Yashiga mota ya zauna yana d’aura belt yana kuma amsa wayar wani abokinshi na koyarwa da za suyi tafiyar tare.Tun daga ranar Julaibib yacanja taku tunda abin iya ruwa ne…

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar litini (Monday)ranar aiki ko nasara na tsoron ki tana kwance cikin bargo tana baccinta na tofan gira dan yau sai yammaci zata shiga makaranta kiran wayar Inna yashigo tad’aga da fara’a”Innarmu Sudaida takirata tana yar dariya”na’am yar gidan Inna,suka gaisa Inna tace”na ji autana shiru ni da Alhaji har mun gaji min kira layinshi sau shurin masak’i,da tana shiga baya d’agawa amma daga baya kuma ta daina shiga kwata-kwata.

Dasauri cikin d’an bud’e idanu dan mamaki tace”shi Yaya d’ansarai d’in Inna?Eh shi d’in,ko baya jin dad’i ne kuke 6oyewa?Fargaba takamata dan kwana biyun nan itama fa bata gane mishi wallahi”a ah Inna lafiyar shi k’alau,yanzu ma yana cikin makaranta bari ya shigo inji abinda yafaru.Toh ALLAH yadawo dashi lafiya,ALLAH ya jishshemu alheri sukayi sallama Sudaida tana amsa addu’ar Inna da amin,amin Inna.

Tafito d’akin-shak’atawa kawai taganshi kwance a doguwar kujera.Yaya Julaibib takira sunan shi. A hankali yabud’e idanun shi yana kallanta”har ka dawo ne amma baka nemi ni ba? Ni banji shigowar kaba.Yauwa sai tajuya ta d’auko wayarta”munyi waya da Inna d’azu barin kirata,yafizge wayar ta bishi da kallo yakasheta gaba d’aya sannan yatura a aljihun gefen rigarshi ta dama”rabu da ita Sudaida.Tazauna a k’asa gefen k’afafunshi tana bud’e idanu da mad’aukakin mamakin furucinshi”Innarce za a rabu da ita? Bai bata amsa ba yamaida idanun shi yarufe.

Tasake bin shi da kallo cikin tsoro da shakka”to ko dai Yayi Julaibib ya fara k’arama sama hazo ne?Data isheshi da tambaya sai kawai yamik’e yashige d’akin baccin su har yanasa mukulli,bai fito ba sai da za shi masallaci sallar azahar.Tamik’e ta tare k’ofar.Yad’an yamutsa fuska “ke bani hanya yanzu za tada sallah.Tagyad’a kai”ba in da za ka har sai ka fad’amin abinda yake damunka da har za kace a rabu da Inna..

“Adai-daita sahu a had’a kafad’a…

Suka fara jiyowa daga masallaci yad’an kalleta cikin natsuwa”barin dawo daga sallah sai muyi maganar ko?

Daga masallaci makaranta yawuce bai koma gidan ba,tagaji da jiranshi,itama tatashi tabishi,yana jin an kwankwasa k’ofar ya amsa daga ciki”na’am bismillah shigo,bai zaci itace ba.Takulle k’ofar tazare mukullin”Yaya d’ansarai ni fa ka sani a rud’ani wallahi, wai me yake damunka ne Inna za tayi magana dakai kace wai a rabu da ita sannan ka k’wace waya ta ka kashe,ta kama ka kashe me yafarune?Ni ma kwana biyun nan kwata-kwata bana gane maka.Yamaida kanshi jikin kujerar”to Inna me za tamin?Inna bata da maganin damuwata fa.

Da rawar murya tafara nuna shi da yatsa”Kai Yaya d’ansarai Innarce..ba..ta da maganin… Damuwarka?To duk fad’in duniyar nan ma kana da kamar tane?Takalleshi cikin takaici”to wa yake da maganin damuwarka?!

Yajanye kanshi daga jikin kujerar yad’ora duka hannayenshi a saman tebur d’in sannan yakalleta cikin natsuwa”Zaujatiii…ke ce maganin damuwata,ina k’aunar ki, ina jin takaicin ace wai ni Julaibib yanuna kanshi da yatsanshi wai ni zan rabu dake dan kawai ba kya haihuwa, ni ina son ki a kowani irin hali da yanayi na rayuwa,Sudaida ko baki haifa min Ya’ya ba ba na nadamar aurenki.

Ni yanzu abinda yake damuna yahanani rawar gaban hantsi shine na kasa samo mana mafita ta yadda zamu rabu salin-alin ba tare da Inna ko Kawu ran wani daga cikin su ya sosuba, kema kuma na san kin k’osa amma kina min biyayyane kawai saboda na rok’i alfarma kar kice kome…Dammm… Zuciyarya tabuga…tanajin wani irin yanayi mara dad’i yana bin ilahirin gangar jiki da zuciyarta,gaskiya idan tarabu da Yaya Julaibib…kai anya? Sai tabar wannan ayyane-ayyanen na zuci.

Yawani marairaice”ALLAH yamiki albarka Zaujatiii…yarik’ota da wani salo”ko ke zan d’aurama wannan aikin na lalubo mana mafita danni dai har yanzu na ka sa, amma ko bama tare Zaujatiii…ki rik’e wannan a zuciyarki “ke ce mace ta farko dana fara k’auna,k’auna irin wannan ta aure zan kuma cigaba da k’aunarki ko da bama taren.Jikinta yadad’a yin sanyi da jin kalmar nan ta rabuwa…ganin hakan da tayi sai yacigaba da zugata ta hanyar kambama halayenta na kwarai,da kuma mamakin da yakeyi wai ita da kanta take ikirarin saki bayan ta san hadisin Manzon ALLAH da yace duk macen data nemi mijinta yasake ta batare da wata hujja ta shari’aba toh k’amshin aljannah ma bazata shak’aba,kuma shi k’amshin aljannah ana fara shak’arshine tun daga tafiyar shekara d’ari biyar,haba Zaujatiii…da ilminki da wayonki da kome na ki,tayaya wasu dangin miji can za su rabamu,bayan basu suka had’amu ba,ni fa nake auren nan ba wani ne yakemin ba,ai nine zan miki gorin haihuwa kece kin d’anji haushi ko?Karki kuma d’aga hankalinki a kan duk maganar masu magana,sau nawa muna zuwa ganin likita akan rashin haihuwa ana kuma bamu tabbacin dukkanmu lafiyar mu k’alau lokacine kawai baiyi ba,ba da bakinki kikace ke kin daina shan wata k’waya dan neman haihuwa kin barma ALLAH ba?Me Yaya Asma’u za tayi ta6ata miki rai?Yau kika san halinta?Ai tun kafin mu zama ma’aurata kin sani dan ko gidanku taje sai tanuna wannan halin na ta,kin gani ganin idanunki ke ganauce kuma jiyau..

Rashin haihuwa ba k’ask’anci bane wallahi,Idan kika duba gidan Manzon ALLAH a duk matanshi ba wacce ya keso sama da Nana a’isha kuma har ta koma ga ALLAH bata haihu ba,bayan ita a kwai wash matayen na shi da basu haihu ba,to me garage darajarsu?Annabawan ALLAH nawane da basu haihuba?

Ganin damar ALLAH me idan yaga dama yabaka Ya’ya maza zallah,ko yabaka mata zallah,ko yahad’a maka maza da mata,haka kuma ganin damarshice yabarka bakarare(Mara haihuwa) kinga da…

Bai k’arasa furucin shiba ta k’ank’ameshi tana kuka,yayi lallausan murmushi dan hak’anshi ta tadda ruwa,yacigaba da rarrashinta”Zaujatiii…ni d’ansarai ni ne me auren nan kuma na ce mutu ka raba,ko kin haifa min Ya’ya ko baki haifa min Ya’ya ba,kuma na miki alk’awari zan yima tufkar hanci,ba me kuma samun ke a damuwa a dangina,su suje su rungumi mazajensu cikin annashuwa ni kuma su dagulama Zaujatiii…nah lissafi?Toh karki damu kinji ko?Tad’ago takalleshi”Ya’ya d’ansarai nagode maka da wannan tunatarwar ta ka”idan rai ya 6aci to bai kamata hankali ya gushe ba…kai mijin alheri ne;tasauke gwauran numfashi

“Rayuwata idan babu kai a cikinta za a samu tasgaro me tarin yawa,tadad’a k’ank’ameshi tana shak’ar k’amshin deodorant da arabi’an perfume d’inshi,yad’ago fuskarta suka kalli juna yad’an dage kira yana mata wani kallan k’auna yana murmushi “mun zama k’arfe da mayen k’arfe ko? Tajijjaga kai”eh wallahi autan Inna,d’ansaran Baba,Zaujiii… Ustazun Sudaida yar Ibrahim,jikar Ibrahim Me-Lambu.Suka sumbanci juna yace kuma”mayyar rake abin ma yasamu shiga wai d’an wake a hotel har da injin d’in matse ruwan ko da ta zama tsohuwa ba hak’ora ko?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button