GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Maimun yakalli Julaibib cikin tsokana “Yah d’ansarai inane k’auyan mutuniyar takane?Na ta6a tambayarta tace min Mabushi ko Madakiya?Ko mene?Ni na manta.Shiruma amsace. Yagyad’a kai “To da alama yan miskilancin sun motsa kenan.Aminu yamik’e”Maimun zo muje muyi shawagi kaji,zama waje d’aya tsautsayi.Suka bar Julaibib a d’akin,sunyi yawo sosai har Fadar Sarkin hausawan garin saida yakai Maimun yakwashi gaisuwa,Sarki me kirki da karamci yayita sa musu albarka yamusu addu’ar sumu ALLAH yabasu mata nagari,sai bayan la’asar suka koma gida dan shirin tafiya wa’azin maza da za ayi agidan Bak’i,bayan sallar magriba aka rufe taro da addu’a abokansu suka dauki hanyar Gidan-Waya, Aminu dai yarik’e Maimun wai dole sai ya kwana.A kwana d’aya da sukayi sunyi sabo naban mamaki kasancewar duk su biyun baki abin magana ne, sukayi sallama da alk’awarin kaima juna ziyara a duk lokacin da suka samu sarari.

Yafito daga cikin dalleliyar motarshi kirar Toyota bak’a wuluk sai walainiya takeyi a cikin hasken rana.Yana sanye da kakin soja,tafiya yakeyi cikin isa da gadara dajin cewa eh ya ne kayi hattara,ka kuma kiyaye ni ko kasha na jaki.Kwan kwan kwan…ahankali yake rank’washin k’ofar kwan kwan kwan…Just come in… Yajiyo muryarta daga ciki.Yasa hannu a marik’in k’ofar yamurd’a yashiga.

Yabita da kallo tana kwance ruf da ciki da kayan bacci,dasauri yak’arasa gadon ya d’agota…suka kalli juna na wucewar wasu dak’iku, sai ta kauda kai a maimakon tabashi sumba kamar yadda tasaba.Yajuyo da fuskarta yana k’ok’arin sumbantar ta amma ta fuzge da sauri. Takoma ta kwanta “Beauty…tashi muje asibiti me ke damunki ne haka? Nace maka bani da lafiya ne? Hey don’t fool me,idan ba ciwo ba me zai ramar dake haka?Idanun ta suka ciko da kwallah sai kawai tafad’a kirjinshi tafashe da wani irin kuka.

Lidiya tashigo da murnan ta sai kuma tayi saroro tana kallansu,Ya juya yana kallanta. Lidiya me yasamu Beauty haka?Tad’an motsa kafad’a”Ga kai ga k’afa ka tambayi me aka yanka? Ai ita zata fad’i meke damunta.Baranzan yayita rarrashinta dak’yar yasamu tayi shiru.Ya gewaye hannayenshi ajikinta,yana mata magana a hankali “na fa shirya mana party na Birthday d’inki da akayi bana nan.Lidiya tabashi hannu suka tafa. “Good Baranzan a ina za a yi?Yakalli Kasham yana murmushi”Kasham Hotel Kafanchan”Lidiya tayi d’an tsalke tana ihu “Hallelujah”.

Tad’an daki kafad’arshi ta hagu,suka kyalkyale da dariya.Tad’auki jakarta”to yah ne? Bani kud’i zanje inyi nail fixes da gyaran gashi.Ya zarosu da yawa baiko tsaya k’irgawa ba ya bata.Tak’arba tare da sara mishi”Yes Sir ta buga kafarta da dama a k’asa”Thank you Sir.Tafita da sauri.Yasaki Kasham ya kunna taba sigari, yamata kyakkyawan zuk’a sannan yafara fesar da hayak’in tabaki ta hanci cikin shakara yana mata wani kallo.

I miss you deadly Beauty…

Yamik’a mata karan taban,tagirgiza kai “No I’m not in the mood”yakalleta nifa gaskiya yunwa nakeji saboda d’okin ganinki ko karyawa ban tsaya na yiba dan nasan zaki dafamin abinci me rai da motsi amma gashi baki da lafiya “Tashi muje in nemi abinda zanci”.

Tacanja kayan baccin jikinta da wando legging ruwan zinare da wata shirt checker,tana sa ma6allan gaban rigar shi kuma ya d’auko katon ribbon ruwan zinare ya tattara gashinta daya hargitse yad’aure, yana kallan d’an k’aramin bakinta daya d’an bushe dan bata shafa mishi mai ba”ni fa da yunwan kome na zo, kema kuma kin sani,amma na ga kamar hak’ata bazata tadda ruwa yadda nake so ba ko?Tayi kamar bataji abinda yake fad’aba.Tarik’o hannunshi”dan ALLAH mutafi dan idan nakoma na kwanta wallahi ba inda zani”.

Yana sanye da fararan kaya, bak’ar hula da bak’in takalmi sau ciki yayi sharrr dashi,ya rataya bak’ar jaka a kafad’arshi.Daga bayanshi yaji k’arar mota, sai ya kauce gefe.Tasauke gilashin bangaran da take zaune.

“Barka da safiya d’ansarai…

Yayi kamar ba dashi take yiba, yacigaba da tafiyarshi har yasha kwanar lecture hall d’insu ya6ace ma ganinta.Baranzan yaja motar yana tambayarta”waye wannnan ana mishi magana yayi banza da mutane?Tamaida kanta jikin kujerar motar”Ina ga baiji bane dan naga da headphone a kunnuwanshi.Jikinta yayi sanyi bata so yaganta da Baranzan ba wallahi,duk maganar da yake mata tamishi shiru kamar me bacci.

Wannnan party baiyi wani armashi kamar yadda suka saba yin chasu da rawar mak’osa ayi shaye-shaye yadda a kaga dama,dan gaba d’aya bata da walwala banda ma ya takura mata da ba inda zataje, kwananshi uku awajanta sannan yayi shirin komawa Jaji Barrack bakin aiki amma yayita rok’onta idan ta samu sarari tabiyoshi,ta amsa da to,amma tayi alk’awari ba wanda zata sake bi har ta kwana dashi indai ba Julaibib ba.

Ranar talata Musaddiq baije ko ina ba yana zaune a d’akin-shak’atawa yaji ana k’wank’wasa k’ofar,yace shigo dan yasan kila Asma’u ce amma sai ta fad’a mishi dalilin ta na k’inyi sallama,amma me?Kasham yagani a tsaye. Kasham? Yafad’a da mamaki kece?Dama kinsan gidana ne?Takasheshi da lallausan murmushinta “Kabar mamaki,dan matambayi ai baya 6ata.

Naji kayi aure shine nazo tayaka murna, I’m I not wellcome? Bata jira amsar shiba tama kanta mazauni a d’aya daga cikin kujerun d’akin,tad’anbi d’akin-shak’atawar da kallo, sannan takalleshi “To ina amaryar taka?Yamike bari akirata yashige d’aya d’akin sannan ya kullo k’ofa”Safiyya takalleshi lafiya?Yarungume hannayen shi a k’irji lafiya lau,tashi kije ku gaisa wata yar makarantar muce tazo mana ALLAH yasanya alheri.Tamishi kallan tuhuma”Oh wanda tamaka a makaranta bai gamsar da itaba har sai ta biyoka gida?Yayi murmushi”Haba amaryata yaushe akai daren da gari zai waye? Kasham…she mean nothing,ai kece komai na, yafara Istirja’i, shaid’anne yake so yasak’a miki mummuna,kinji amaryata?Tayi murmushi suka fito tare.

Wani Ovation take dubawa tad’ago tana murmushi”Amarya barka da fitowa,tanuna Musaddiq kinga mijin kin nan kirkinshi ragaggene a wajena tunda har zaiyi aure amma bai fad’a minba,ni kuma ai naga abin farin cikine to meye na 6oyewa,?To koma dai yayane ba a gayyace niba amma danaji labari gashi na zo” Musaddiq ina tayaku murnar aure,kuyi hak’uri Ku zauna lafiya for better for worst.Suka mata godiya, tace haba ba komai fa,wata kilama mutumin nakane yace karka fad’amin. Kamar bai gane wanda take nufiba yace”Wa kenan? Tad’an kalleshi “Wa kake dashi a Gidan-Waya daya wuce d’ansarai?Yayi murmushi”au shi kike nufi?To ba ruwanshi,Julaibib bai ta6amin maganar kiba.

ALLAH da gaske!???

Ta tambayeshi cikin mamaki zata cigaba yatari numfashinta”Indai maganar d’ansarai zakiyi tona rok’eki kiyi shiru kawai tunda bashi da wani amfani.Yafad’a miki gaskiya… Takatseshi da sauri “Karkasa jinina ya hau,danni nayi alk’awari ko ana ha maza ha mata sai na auri Julaibib dan ina sanshi,takalli Safiyya” Madam ku taimakeni dan na san za ku iya wallahi,sallah ne dai da banayi yasa kuke k’ok’arin nisantani daku ko?To nace zan iya, ai ko bai kamata a k’wacemin gatarin danace zan iya had’iyaba…

Safiyya ta jijjiga kai kenan a yadda take magiyar nan ta dad’e tana yak’in neman soyayyarshi ALLAH ne kawai yatsare shi daga fad’awatarkonta,tasake kallanta masha-ALLAH tanada kyau najan hankali,d’an k’aramin bakin ta da manyan idanunta masu maik’o su suka k’ara mata kyau na musamman ga ta da yalwan gashin kai,gashi kuma da alama ma’abociyar kwaliyar jan hankalice,dabara tazo mata dan haka ta kalli Musaddiq cikin tashin hankali”Dama baka fad’a mataba?To bari kiji Kasham kike kowa?Ki bud’e kunnnuwanki ki saurareni dakyau”Julaibib yana da matar aure karatu ake jira tagama musha biki kuma kanwata ce,dan haka kitashi kibar min gida.Tamik’e rai a 6ace ta wuce cikin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button