
Tad’an daki k’irjinshi,shi kuma yabata marin soyayya suna dariya.Tad’auki wayarta a saman tebur d’in ta kunna”toh kira Inna gaskiya dan ta damu da rashin jinka tunda har takirani.Yagirgiza kai “gwamma mutafi Zonkwa ayi kome idanu na ganin idanu”zan fad’a mata kece kika hanani.Tad’auki jakarshi taraya a kafad’a suka fito daga office d’in, suka jera suna tafiya zuwa inda ake ajiye motoci da mashinan malamai tana fad’a mishi”Inna baza ta ta6a yadda ni na hanaka kiran taba,tunda ni kullum sai mun gaisa ko ta kirani ko in kirata.
Watannin Sudaida bakwai kenan da tafiyarta Gidan-Waya,duk wannan watannin zuwanta Zonkwa sau hud’u,yanzuma tanata mishi magiya yabarta taje tunda sun samu hutu amma ya hana,wai tayi zamanta a in da mijinta yake ai shine zai fi mata kwanciyar hankali,tagyad’a kai”ni ma na sani ai bawani dad’e wa zanyi ba mak’o d’aya dan ALLAH, amma ya hana,haka dole ta hak’ura,dangin Julaibib kuma sun barta tana rawar gaban hantsi bata san me yafaru ba,amma tabbasss…ta dad’a yadda da kalaman shi kamar yadda yace ba me sa mishi mata a cikin damuwa.
Da safe tana kwance tak’i tashi tahad’a mishi shayin shi ko ruwan wanka,shi yamusu kome,yagama shiryawa sannan ya zauna a gefen gado”Sudaida yakira sunanta.Tad’ago tana kallanshi yana sanye da babbar riga yar ciki da wando na farin yadi yana karya hular zita”har yanzu baza ki tashi daga kwanciyar k’asan nan ba?Tasauke idanunta k’asa”ni dai nafi jin dad’in nan.Yagyad’a kai”sauri nake yi damunje asibiti.Tamik’e zaune dakyar”ba sai munje asibiti ba,naji sauk’i Yaya d’ansaarai.Yagirgiza kai”za dai kiji sauk’i,tun yaushe nakai miki ruwan wanka amma har yanzu baki tashi kinje kin yiba?Yamik’a mata hannayen shi”ta so muje in cud’a ki.Tayi yar dariya”bayan ka shirya?Ai zaka 6ata adon ka,yi tafiyarka yanzu zan yi.Yad’an motsa kafad’a”uh to menene a ciki,ba sai in canja wasu kayan ba? Tamik’e tana mishi rakiya,kad’an ta taka mishi ta dawo tayi kwanciyar ta dan dama bata so tayi wankan,idan tafad’a mishi to sai ya tilasta ta yin wankan ko ta so ko tak’i.
Har yadawo tana kwance yayi tsaiii…yana kallanta yana bin d’akin da kallo,ba abinda tayi yakad’a kai cikin damuwa”wannan ba halin Zaujatiii…bane tabbasss bata da lafiya.Dakyar yatashe ta sai wani narkewa takeyi, amma tanayin wanka sai tajita garau…yana kallon tashar larabawa suna nuna yanayin al’adunsu yana cin gasashshiyar kaza me kayan lambu tashigo yabita da kallo tana sanye da material bak’i me yarfin filawoyi ruwan k’asa, d’an kunne,sarka da warawarenta na zinare sai d’aukar idanu sukeyi saboda kyallinsu,fuskarta shar da kwalliya, bakinta yana kyallin jambaki ja.
Tazauna suna kallan juna “Zaujatiii…kinyi kyau dame kike son tukwuici?Tad’ora ha6arta a kafad’arshi tayi furucin da wani salon shagwa6a “agada(plantain) yajuyo yakalleta”kin cinye wannan agadan dana siyo miki ne?Ta amsa kai tsaye”wallahi tun jiya.Yabud’e baki dan mamaki saboda ada shi yake matsa mata tasoya musu dan ba wani dad’ata da k’asa yayi ba,amma a yan kwanakin nan cin agada takeyi kamar ta samu abincin gado,d’an kullum, ranshi yadad’e me martaba tuwo miyar kuka abincin hausawa.Kai shifa bai yadda ba sai da yaje yaduba in da suke ajiyewa yaga ba kome sannan yadawo yana cemata lallai kinyi k’ok’ari,yad’auki waya yana kiran wani mak’ocin shi da yau yatafi Jos kuma anjima zai dawo dan ALLAH yasiyo mishi agada.
Yasake kallanta bayan yagama wayar amma fa na d’auka bakya jin dad’i danaga tun safe kina ta bacci har shabiyun rana.Ai na fad’a maka lafiyata k’alau kawai ni dai nafiso in kwanta in yi baccine.Ya mata nuni da kazar.Tagirgaza kai dan ko sha’awar ci batayi,tad’auko lemun peach tana sha suna hira jefi-jefi suna kallansu har suka gama shirin,sannan yamik’e zai koma makaranta “adawo lafiya.Takashe kallan tad’auki wayarta ta kunna data zuwa duniyar yanar gizo…
Da daddare kafin yadawo daga sallar Isha’i Sudaida tayi baccinta a inda ta idar da nata sallar. Yatasheta”Zaujatiii…ga agadan an kawo.Dakyar tad’an bud’e idanunta da yanayin bacci takalleshi sai ta mayar ta rufe,tayi wani juyi tana dad’a shemewa a dadduma”barshi sai da safe ni bacci nake ji,tacigaba da baccinta sai kuma tamik’e zuwa d’akin bacci.
Yabita da kallo har tashige.Shi kad’ai yayi zaman d’akin-shak’atawa yaci abinci kad’an, yaje yahad’a shayin shi da baya gajiya dasha.Yagama yan rubuce-rubucen shi har zuwa sanda bacci yafara kawoma idanun shi ziyara,yashiga d’akin ta kashe wuta,yakunna fitilar wayar shi yana hasketa” tana kwance a k’asa kuma yau tsabar jin bacci ko kayan bacci bata tsaya sawaba,yad’anyi murmushi yana cigaba da kallanta numfashi na shiga da fita cikin kwanciyar hankali,sai tamishi wani irin kyau na musamman, ya dad’a gyara mata rufa dan yasan ko ya maida ita gadon to sai ta sauko wai ita k’asa yafi mata dad’i,yakashe fitilar yakwanta yana musu azkar d’in bacci.
Abinda yaketa maimaituwa kenan,kullum bata da kuzuri,bata san yin kome sai kwanciya,yau dai abin ya isheshi,dan haka yana dawowa daga Kaduna jakarshi kawai ajiye,yatasata agaba sai tashirya sun tafi asibiti dan daren jiya kusan kwana sukayi tana mishi wash…wash…mararta tana mata ciwo amma abin mamaki baturiya da suna manga gari na wayewa sai tamik’e wai ta warke,yanzu kuma yadawo ya ganta lamooo bata da wani kuzari sai bacci-dai bacci dai bata gajiya…Yabita d’akin tanata nuk’u-nuk’unta”Zaujatiii…hijab d’in ne baki gane ba kome?Tabud’e wardrobe tad’auko.
A k’ofar gida sukayi kaci6is da motar Musaddiq tsayuwar shi kenan suka fito shi da Hajiya. Sudaida tarungume ta tana murna”oyoyo Hajiyarmu sannu da zuwa,suka koma ciki.Julaibib yayi murmushi”yau farar ranace agaremu me kyakkyawar suna.Hajiya ta ajiye kofin lemun”to ance ka gaida me gaisheka,kunzo nan kun share waje kun manta da kowa kuna sha’anin gabanku.Julaibib yasa hannu yana shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi “munata fama dai da ayyuka da d’alibai Hajiya.
Ganin Hajiya yasa Sudaida ta nemi kasalar data rufeta tarasa,tashige d’akin-girki tana k’ok’arin shirya musu abincin data cema Julaibib ita yau baza tayi wani girki ba,yad’an motsa kafad’a” duk d’aya 6arin manshanu a miya, dan shima ba kullum yake cin abinci me nauyi da daddare ba.Musaddiq dai bai tsaya cin wani abinci ba Sudaida tafito suka gaisa yamusu sallama suka fita da Julaibib.Har suka gama cin abinci bai dawo ba, takwanta suna hirarsu me dad’i da Hajiya,bacci yafara d’aukanta sama-sama, sannan taji sallamarshi yashigo musu da gashashshiyar kaza,bata tsaya ciba tamusu sai da safe taje tayi kwanciyar ta tana jinsu sunata hirarsu, ita kuma baccinta rabi-da rabi tayishi saboda ciwon maran d’aya matsa mata daren jiya to yauma daren yayi shine yace bari ya motsa.
Yadawo daga masallaci sallar asubahi yaganta tsugune a bakin famfo tana ta yunk’urin amai amma yak’i zuwa,Hajiya tana mata sannu,tarik’ota suka koma d’akin-shak’atawa takwanta a doguwar kujera jikinta a mace yake murusss”sannu ALLAH yasauwak’e”Hajiya ta zauna tana mata fifita ganin yadda tajik’e sharkaf da zufa kamar wacce tafita motsa jiki da sanyin safiya.
Yazuba mata idanu zuciyarshi ba dad’i saboda yadda take dad’a rintse idanunta tana mirgina kai gefen hagu zuwa dama tana yarfe hannuwa,tana ta6a mararta da take mata wata irin d’aurewa tamauuu…ita kad’ai tasan azabar da take ji, wucewar wasu dak’ik’u cikin ta ya dad’a yamutsewa ciwon yana k’aruwa,mararta kamar zata 6alle,Hajiya itama ta shiga cikin damuwa”Sudaida wai meke damunkine?Wai!Wash…wayyohallahnan…uhhh…washhh.. Tasake yarfe hannun hagu na dama na saman mararta,da kyar tayi furucin”Wayyoh! Hajiya marata ce take ciwo. Julaibib yajuya dan tsayuwar ba amfani, motarshi kuma ba ishashshen mai”Hajiya barin samu mai yanzu mutafi asibiti.Tagyad’a kai”to hanzarta dan naga abun yana dad’a k’amari.