
Wayyo ALLAH! Tafad’a a galabaice tayi nishin wahala…uhhh…Hajiya marata!”sannu Sudaida yanzun nan Julaibibi zai zo mutafi asibiti.Ta cije le6enta na kasa ta yunk’ura zata mik’e zaune amma ta kasa;Hajiya ta taimaka mata,tad’ora kanta a kafad’ar Hajiya idanunta na rufewa da bud’ewa cikin azabar ciwo,cikinta na cigaba da hautsinewa ciwo na k’aruwa,da marar tayi wata irin murd’ewa sai ta k’ank’ame Hajiya tana Istirja’i da salati, tasake k’ank’ame Hajiya iya k’arfinta tayi wani nishi sai kawai taji wani ruwa me d’umi ya 6alle mata da kyar taduba sai taga jinine,cikin yan dak’ik’u zanin jikinta ya jik’e sharkaf,zata tashi jiri luuu…yayi awon gaba da ita ta zube a jikin Hajiya cikin d’aukewar numfashi.
Hajiya ta rikice tashiga jijjigata amma ko motsi ga jini na cigaba da zuba, saboda rikicewa sai tarasa me ma za ta matane?Tana cikin wannan halin Julaibib ya turo k’ofar yashigo.Cikin tsinkewar zuciya yake kallansu saboda ganin Sudaida da yayi kwance cikin jini male-male,k’wak’walwarshi bangaren tunani da adana bayanai yafara tariyo mishi shud’add’en abinda yafaru a shekarun baya lokacin da Bilkisu take kwance sam6al cikin jini fuj’atan.Dammm…yaji ruguzowar wani abu a k’ahon zuciyar shi”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un…baiyi wata-wata ba yasa hannayenshi ya cicci6eta cikin tashin hankali yayi mota da ita,Hajiya tabiyo shi.
Sun 6ata lokaci suna dubata sannan wata ma’aikaciyar jinya takirasu”kaine mijinta? Yajijjaga kai kawai.Tad’an kalli Hajiya sannan tamaida kallanta gareshi”yarinyar nan gaskiya tana mugun jin jiki kuma matsalar ta fi k’arfin mu,tunda sai an mata aiki kuma likita baya nan,to sai ku gaggauta kaita wani asibitin,irin wannnan zubar jinin idan yazo da k’arar kwana sai a rasa mutum.”ALLAH yabata lafiya yasa kaffarace.
Tajuya tayi tafiyarta.Hajiya ta kalli Sudaida bata san wanda yake kanta ba.Julaibibi mu san abinyi mana.Idanun shi sun kad’a jawur,yayi wani huci cikin tashin hankali sannan yaba motar wuta,a guje yafito daga harabar asibitin suka fad’a kwalta zuwa wani asibitin.
Dasauri suka d’auketa zuwa d’akin agaji da taimakon gaggawa suma sun 6ata lokaci sannan likita tafito suka bi bayan ta zuwa office suna tambayarta me yafaru?Yajikin na ta?Ku kwantar da hankalinku.Tadanyi rubuce-rubucenta a katin data shigo dashi tagama taturashi a aljihun Labcoat d’in ta, sannan tad’ago cikin natsuwa ta kalli Julaibib”ka gane ko,matsalar matarka sai an mata aikin gaggawa, idan ba haka ba za ta iya rasa ranta,saboda ciki tasamu amma ya zauna a bayan mahaifa.
Shi da Hajiya suka kalli juna sannan suka kalleta cikin murna da mad’aukakin mamaki.Yayi yar dariya”ciki likita?Tajijjiga kai”eh ciki.Suka shiga tasbihi ga buwayi gagara koya dan furucin likita ya zo musu a bazata.”Julaibib yayi sujudush-shukri.Likitar ta cigaba to amma an samu matsala dan cikin har ya fashe, abinda yasa take wannan serious bleeding d’in kenan (rupture ectopic pregnancy)kuma wannan aikin dole sai Gynea Doctor(likitar dake mu’amala da abinda yashafi lalurorin mata)kana…Julaibib yatari numfashinta”to ke fa?
Ni nan da dak’ik’u talatin zan shiga wani aikinne(operation) amma karku damu dan nayi waya da Doctor Kagarko itama kwararriyace yanzu haka tana kan hanya.Tabud’e dirowa tad’auki wani fallen littafi tayi rubuta sannan ta fad’a mishi adadin kud’in da zai biya,tamik’a mishi wannnan fallen littafin kaje kabiya kud’in sannnan kaje a d’auki sample d’in jininka idan yazo d’aya danata basai an siyaba. Yamik’e yaje yabiya kud’in,kuma yasa hannu sannnan yawuce aka d’auki jinin shi ana dubawa akaga yazo d’aya sai aka wuce dashi laboratory dan tantance sahihancinshi kafin ak’ara mata.
Doctor Khadija Aminu Kagarko tak’araso, matar me hankali da natsuwa ga tarin ilmi da ya ratsata,ta gaishe da Hajiya cikin girmamawa”ki mana addu’a Ubangiji yasa a dace.Hajiya tagyad’a kai”ALLAH ya amsa yar nan.Hajiya da Julaibib sunata kai-kawo bakunansu d’auke da addu’o’i tunda aka shiga da ita d’akin theatre,har akayi aikin aka gama aka fito da ita agadon marasa lafiya ana turata a hankali dan zuwa d’akin hutu,idanunta a rufe bata san in da takeba,ta d’ashe saboda rashin ishashshen jini,yasauke gwauran numfashi”Alhamdulillahi an tsallake tsirad’i d’aya na yin aikin cikin nasara,saura na farfad’owarta,ALLAH yasa tafarfad’o cikin hayyaci da lafiya.
A sanda rana tatafi zata fad’i magriba na shirin kunno kai Sudaida tad’an motsa da alama maganin da suka ba ta na anaesthetic ya fara sakinta…wucewar wasu dak’ik’u kuma tayi motsi da fatar idanunta sai kuma tad’an bud’e idanun tana bin Julaibib da Hajiya da suke rige-rigen yi mata sannu,a hankali bakinta yamotsa tana salati, sai kuma ta yunk’ura zata tashi,yarik’eta da sauri “Zaujatiii… Kiyi hak’uri kinga aiki aka miki kar a samu matsala,takoma takwanta ta damk’i hannunshi tamau tafara kuka mara sauti saboda jikinta ba k’wari”ni dai ku yafemin mutuwa zanyi furucin a hankali yake fita muryar kamar bana taba, sai kuma tafara sambatu
“Dan ban haihuba sai a dinga min cin kashi? Ni zan ba kaina haihuwa? Shima autan Inna ai ina jin haushin shi dan bai kawo min agada ba,har madidi nace yasiyo min amma yak’i…Hajiya cikina ciwo yakeyi marata… Wai…wayyoh Zaujiii…ni fa ba na san wannnan kallan na ka dan haushi yake bani…kai fa ran…da sauri yasa tafin hannun damarshi yatoshe mata baki dan kartayi kato6arar da zai sa shi jin kunyar Hajiya tunda ba a hayyacinta take ba kome ya d’arsu a zuciyarta fad’arshi za tayi.Ganin tak’i sakin hannun Julaibib dan yakira likita yasa Hajiya ta tafi kiranta”to fa tashin hankali gobarar gemu…
Magani a shaka badan yunwa ba.
Kome tsawon giginya daga k’wallo tafara.
2 Rajab 1441
25 February 2020
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in.
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na ashirin da uku.
Kwanakin su uku Doctor Khadija Aminu kagarko tabasu sallama dan Alhamdulillahi ta samu sauk’i, wata ma’aikaciyar jinya tana tsokanar Julaibib saboda yadda yadamu da Sudaida,lokacin ba da magani (medication)nayi idan basu zo ba da kanshi za shi yakira su”ALLAH dai yasa d’an daza’a haifa yamaka kara yayi kama da kai dan ba k’aramar hidima kayi ba.Yayi murmushi kawai yana shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi.Mutan Zonkwa ma d’ai-d’ai kune wad’anda basu zo dubiya ba a cikin yan’uwa da abokan arzik’i.
Doctor Kagarko takalli Sudaida cikin kulawa”ki kula da kyau kinga aikine a jikinki,banda aiki bare d’aukar abu me nauyi okey?Sudaida tagyad’a.Tarakasu har wajen mota, Sudaida tashiga tazauna sannan ta rufe musu motar, tad’an sunkuyo ta taga”Hajiya ALLAH yakiyaye hanya. Madam adinga kula da dressing d’in wajen yadda yakamata, kidawo akan lokaci kar fa kiyi sakaci.Tad’aga hannu tana musu adabo,suma godiya sosai suke mata.Doctor Khadija Aminu Kagarko ta san ya kamata.
Julaibib da Hajiya su suka cigaba da kula da ita da ayyukan gida.Watannin Hajiya hud’u tafara musu zancen tafiya.Sudaida tawani marairaice”Lillahi warasulihi Hajiya yanzu sai ki tafi kibarni?Tagalla mata harara”to da ni zan tayaki zaman auren?Taware yatsunta hud’u watannina haka a gidan nan,ai ko na yi iya abinda zan iya.Julaibib yagama abinci yazubo musu a faranti”sannu da aiki Zaujiii…Yayi murmushi kawai,yashige bayi yahad’a mata ruwan wanka