
“Sudaida ga ruwan can kije kiyi wanka.Hajiya takama fad’a”kai Julaibibi bana ce kadaina kai mata ruwan wanka ba?Ruwan kawai da za ta bud’e famfo ta tara sai an mata kai haba,tanuna shi da yatsa “kazama jarumi dan a haka nasanka.Sudaida tamik’e kaji matar nan da wata magana to ko wankan ma idan takama ba shi zai min ba?Tamata dakuwa”ungo nan,zancen banza kawai dan an miki aiki shikenan kuma ke bazaki dinga motsa jikin kiba? Sudaida tawuce batayi magana.
Ita kuma Hajiya tana dad’a jaddada mishi gobe Insha-ALLAH zan koma in da nafi wayau Zonkwa.Yagyad’a kai sannan cikin girmamawa yace”ALLAH ya nuna mana goben da ran mu da lafiya…mungode kwarai Hajiya ALLAH yak’ara nisan kwana me amfani.To amin kaga ai kai ka san yakamata,ita wancan matar taka ai bata gode min, niko ba in da zan fara azumin watan ramadana sai a d’akina. Kiyi hak’uri Hajiya bari tafito ai dole kuwa tagode miki.
Suka cigaba da hirar su har Sudaida tafito,yad’ago yana kallan surarta a cikin hasken farin watan daya haskesu”kinyi kyau Zaujatiii…Hajiya tagalla musu harara musamman Julaibib daya kasa daina kallanta,takad’a kai”ba shakka ai kinji sauk’i tunda kika iya zama kiyi wannan kwalliyar abin ma bai tsaya anan ba kikabi jiki kika shafeshi da wannnan shu’umin humran me k’amshin fita a hayyaci,to ni kuwa zaman me zan kumayi?
Sudaida tayi lallausan murmushi”haba Hajiyarmu ban fa sanki da halin sa’idawa ba,yanzu har wani kwalliya nayi?Ko unguwa ai zan iya fita a haka.Eh to in dai kai kikaci(hauka)ai bazan musa ba.Suka kalli juna ita da Julaibib tamishi wani kallo ta kashe mishi ido…Yakai hannu yana shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi a hankali ya motsa la66anshi,Sudaida ta matsa kusa dashi”ni dai Yaya d’ansarai ban gane me kake fad’a da la66a ba gaskiya.Hajiya tamik’e”abin nayi ne to ALLAH ya tashemu lafiya.Sudaida tace kai Hajiyarmu yau da wuri haka zaki kwanta?Eh dan gobe sammako zanyi Julaibibi sai da safe.To Hajiya ALLAH ya tashemu lafiya.
Washe gari tun daga sallar asubahi bai shigo gidan ba sai da hantsi yadubi ludayi da kaya nk’i-nik’i,duk suka bishi da kallo har yagama shigo dasu sannnan yazauna suka gaisa.Hajiya tace”ai na zaci guduwa kayi saboda kar in tafi dama nace anjima kad’an tafiya ta zan yi ko kadawo ko baka dawo ba tunda duk wayoyinka a guda kabarsu. Mantawa dasu nayi sai da nayi nisa da tafiya sannan na tuna.Jos natafi na miki siyayyan tsaraba dana azumi.Hajiya tabi manyan ledojin da kallo tana jinjina k’ok’arinshi tare dasa mishi albarka”Ubangiji yayi albarka, yabaku masu muku madallah nagode nagode Julaibibi. Yayi murmushi”ai ba kome Hajiya, yad’an kalleta cikin natsuwa “na so kwarai da dakaina zan kaiki to amma hakan bazai yiwuba saboda yanayin aiki,yanzu ma Kafanchan zan tafi amma na ma wani direba magana k’arfe d’aya na rana zai zo kutafi,yasake bata wasu kud’ade sannnan yamik’e dan shirin tafiya Kafanchan.
Sabo turken wawa…kowa yayi fushi da bak’o ya ji kunya,da Hajiya tatafi sai taji gidan ya mata girma gashi shima Julaibib ba ya nan tagaji da nazarin da takeyi a cikin na’ura me k’wak’walwa ta rufe, tasa bayan tafin hannunta na hagu tana Isti’aza tare da rufe bakinta saboda hamman da tayi.Julaibib yashigo da sallama, yazauna a kujera a gajiye lik’is yacire riga yabar farar singlet. Sannu da zuwa Yaya d’ansarai.Ya aikin? Yafurzar da iska tabaki ta hanci”aiki ba dad’i kuma ba dama a bari.Wayyo! Neman halali da wuya,kowa ga ganshi a inuwa tabbasss ya sha rana sannu Zaujiii…nah,tad’an shafa kwantacciyar gargasarshi”ubangiji yak’aro lafiya ta gangar jiki da natsuwar zuciya,tad’ora ha6arta a kafad’arshi,tagewaye hannayenta tana mishi tausa. Yasauke numfashi yana jin gajiyar data lullu6eshi tana tafiya a hankali a hankali”Shukran jazilan Zaujatiii…Yad’an bud’e idanun shi daya rufe yakalleta “kin cinye agadan?A ah ai yanzu kad’an nake ci dan yafara fita kaina.Yayi murmushi.
Kafin tagama abinci takawo mishi bawan ALLAH har yafara bacci sai da ta tashe shi tana mishi dariya”yau baza ayi nazarin karatu anjima ba kenan?Yayi mik’a yana salati”gaskiya yau ba nazarin karatun dazanyi,kin san tun a office nake gyangyad’i saboda baccin da kika hanani daren jiya.Takama ha6a tana yar dariya”Kai Yaya d’ansarai nice na hanaka baccin?Yagyad’a kai.Tayi yar dariya”au to shikenan ta kwana gidan sauk’i daga yau bazan kuma hanaka bacci ba shikenan ko?Yamata wannan kallan da bata so yayi bismillah yafara cin abincin data zuba mishi.Takauda kai tana k’unk’uni dan wallahi haushi kallan yake bata.
Ramadan wata me albarka,wata me alfarma.Tana kwance ta kifa fuskarta a cikin matashin,ya san ba bacci take yiba tsabar jin jikine kawai,tunda ko da da take ita kad’ai azumi wahala yake bata bare yanzu ga ciki,bataji shigowar shiba sai da yazauna a gefen gadon yadafa bayanta “Zaujatiii… Tamik’e zaune dakyar tana kallan shi bata da kuzari kona sisin kwabo.
Yakalli cikinta yayi girma yanayinta ya canja gaba d’aya,tausayinta da k’aunarta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarshi “Zaujatiii… Ki hak’ura da azumin nan mana,kinga wahala kike sha,barin had’o miki shayi kawai.Tawani marairaice “haba Yaya d’ansarai kalli agogo kagani k’arfe uku saura kwata na rana sai in karya azumi? Uh to menene ai kina da lalurane.A ah kayi hak’uri ai azumin ma ya kusa k’arewa tunda nayi ashirin to ai ko tara ko goman dasuka rage bazasu gagara ba Insha-ALLAH za k’arasa dani,nima ina kwad’ayin dacewa da daren”lailatul qadri”.Yagyad’a kai”Toh ALLAH yasa mudace da wannan dare daya bambanta da darare dubu a daraja,ALLAH yabaki nak’uda kafiifan(me sauki) Tayi murmushi”amin Yaya Julaibib.
Yarik’o hannunta tamik’e suka fito waje suna d’an tattaki har zuwa bayan gidan in da sukayi yan shuke-shuken su kamar su alaiyahu,ganyan ogu, timatir,attarugu,zogale,d’ad’d’oya(scent leave)da sauran su, dakyar ta zauna a d’an k’aramin dakalin wajen tasa hannu tana tsinkar lemar kwad’i/naman k’asa(mushroom)ya tsuguna yana tayata tare da tambayar ta”yau kuma me za kiyi dashi?
Tun safe natashi da sha’awar shan romon shi(mushroom sauce) yad’an kalleta”ni fa yau a tsarin abincin mu ba shinkafa.Toh Yaya Julaibib,ni ma ba da wani abu zan had’a ba haka kawai zanyi romonshi in sha. Suka gama tsinka sannan suka wuce d’akin-girki yakar6a yawanke ya yayyanka mata, yad’uko kaskon suya yazuba magyad’a kad’an yad’ora a wuta sannan yakalleta”to na miki me wuyan zo kibashi tsoro. Tad’an kalleshi a marairaice nagode,to amma Yaya d’ansarai…sai kuma tayi shiru”uhun menene kuma?
Tanuna mishi abinda take so yayi.Yad’auki wuk’a da albasar yana mita”ni fa a duk aikin gida ba abinda yake bani haushi irin yankan albasa,tagyad’a amma kuma kafi kowa san albasa me yawa a girki,jiyama ai miyar albasar kasani nayi dayake ba kai kake yankawa bako? Eh mana…sukayi dariya yana fara yankawa idanun shi suka fara ruwa, yarintse su”Zaujiii…Karfa kayanke”eh ai kin san zan iya yankewa amma kika sani,da sauri yayi yagama yana fad’in”kai gaskiyar bahaushe da yace albasa batai halin ruwa ba, yawanke hannayen shi da omo,yanad’e hannu riga toh aikin dai aikine an ba kuturu tallan jakai”yad’auko abin markad’e(blender)ina karas d’in dana gyara d’azu?Ai na had’a maka lemun,yana cikin fridge.Yawarware hannun rigar”yauwa Zaujatiii…Kin kyauta nagode ALLAH yamiki albarka.