
Yanzu barinje in yi alwala lokacin tafsir ya kusa,kuma yau d’in nan Insha-ALLAH nake tunanin zamu rufe sai ALLAH ya kaimu ramadan me zuwa ga masu tsawon rai.Toh Yaya Julaibib adawo lafiya, kuma dan ALLAH ana idar da sallar magriba ka dawo gida da wuri kasha ruwa,tazuba mishi dabinon ajwa a aljihu daya manta bai d’iba ba kaji Yaya d’ansarai?Yad’an dafa kafad’arta”Insha-ALLAH nagode Sudaida.Tabi bayan shi da kallo cikin yaba k’ok’arinshi da wata irin k’aunarshi da take dad’a narkewa a sararin cikin zuciyarta.
Safiyar sallah garin yayi lullumi a sanda hantsi yadubi ludayi ta yi k’ok’ari tagyara gidan da taimakon shi,ko ina yana k’amshin turaren d’aki, sassanyar iska tana kad’a fararen lubayen da ratsin ruwan hoda saboda rashin nauyin su.Tana sanye da voil-lace ruwan sararin samaniya(sky blue)doguwar riga dan d’aura zani wahala yake mata yanzu,d’an kunne,sark’a da warawaran hannayenta da zobe na zinare,suna ta d’aukar idanu saboda kyallinsu,ga jan lallanta me yarfin bak’i da tayi k’afafu da hannaye sun k’ara haskata,bata d’aura dankwalin kayan ba sai tayafa k’aramin mayafi ruwan sararin samaniya me shara-shara,gashin kanta yasha gyara daren jiya a wajen gyaran gashi da Julaibib yarakata.
Takoma d’akin-shak’atawa tazauna tana kallan shirye-shiryen wasannin sallah a tashoshi mabambanta aranta kuma tana mita”Yaya d’ansarai ya hanata tafiya gida taje tayi sallah a cikin Iyaye, yan’uwa da abokan arziki,sannan tun d’azu aka sakko daga masallacin Idi ya aiko a kar6a musu tuwon sallah shi da abokanshi kusan awa d’aya kenan,taja tsaki ai ko danko sukeci yaci ace zuwa yamzu sun gama ya shigo,a hankali tazame takwanta a doguwar kujera tacigaba da kallan amma ranta sam ba dad’i.
Taji ana sallama tare da k’wank’wasa k’ofa, taja malalacin tsaki a yadda taji dad’in kwanciyar nan data sani tabar k’ofar a bud’e koma waye tad’aga murya tace a shigo,tamik’e dakyar taje tabud’e, bakinta yak’i rufuwa saboda mamaki sai bin yaran takeyi da idanu,suma sunata tsallen murna sunzo gidan Inna Sudaida,za suci dad’i,yarik’o hannun wasu daga cikin yaran”kai kuzo kawai in maidaku wajen Iyayenku dama daga masallacin Idi natarkato miki su,ban tsaya tambayar kowa ba,yad’aure fuska ganin sunk’i motsawa”mitafi nace ko? Wasu suka mak’ale kafad’a, wasu har idanun su yaciko da kwallah.
Tarik’o hannushi”haba Yaya Aminu talek’o ta koma kenan,yagyad’a kai” eh mana tunda baza ki bamu hanya mushiga ba basai mu koma in da mukafi wayau ba?Oh dan ALLAH kayi hak’uri murna da mamakin ganinku ne yamantar dani abinda zan yi tun farko,tamatsa yaran sunata rige-rigen shiga,suka zazzauna suna tsallan murna wasu suna fad’in su sun dawo nan gidan Inna baza su wani koma Zonkwa ba.
Yaya Aminu naji dad’i wallahi,tazauna suna gaisawa tare yima juna barka da sallah ALLAH yamaimaita mana na bad’in bad’in bad’ad’a…tana tambayarshi mutan gida.Kowa lafiya k’alau Sudaida, mutuniyarki Nasmat ta bani sak’o yana mota,yakalli yaran sun baje suna cin abinci, hakanan zuciyata taraya min dama kaje wajen Sudaida, nace musu nan zanzo shine suka dinga rok’ona ALLAH annabi wai suma za suzo.Tayi yar dariya”ai kuwa nagode daka zo min dasu ALLAH yabar zumunci,dama kad’aici ya dameni.Yakalleta cikin tausayi dan cikinta ya girma”sai hak’uri kanwata,kafin mu shigo na ga Julaibib d’in mutane sun mishi yawa,na san haka kawai bazai kyaleki ke d’aya ba.
To Yaya Aminu kaci abincin mana. Yad’auki wayarshi yana duba sak’on karta kwana da aka turo mishi”ke ni dama kunu kika kawo min. Takalleshi wani iri “kai dan ALLAH wani irin kunu yau take sallah fa.Yamaida wayar aljihu”uhun ba a shan kunu ranar sallah ne kome? Yayi bismilah loma biyar yayi a tuwon sannan yad’auki cinyar kaza yad’an gutsira yamayar ya ajiye dan baya wani jin yunwa,ai kin san halina ni nama ba d’ad’ani da k’asa yayi ba, wannan sai su autan Inna kura kyaci da gashi,tad’an yamutsa fuska”to ai bashi kad’ai bane har da Yaya Musaddiq, yakama ha6a wuuu…au haka ne?Babbar magana ance da mak’asau bawa,barin kama bakina.Tayi yar dariya.
Julaibib yashigo aka cigaba da hirar dashi, ranar wunin farin ciki sukayi,sai bayan sallar la’asar Aminu ya kwashi yaran dayazo dasu cikin mota,Sudaida takawo musu cin-cin,nama da goron sallarsu,kowa ta bashi a hannunshi,sunata murna da rige-rigen fad’in” Inna Sudaida nagode,ALLAH amfana. Takalli Aminu”na rasa me zan baka rabin raina. Julaibib yadafa kafad’arta”juye mishi ragowar kunun safen nan yatafi yayi farau-farau dashi.Tagalla mishi harara,yad’an d’age gira yana mata wannan rikitaccen kallan na shi”eyehhh…ni kike harara?Kinga Sudaida Aminu yakirata,tabishi da kallo daina hararshi haka,yad’auko sak’on Nasmat data rufeshi da wrapping sheet me zanen zuciya da rafar kud’i yan naira ashirin guda d’aya”nawa goron sallar.Julaibib yasa hannu biyu yakar6a”toh Yaya Aminu mungode ALLAH yak’ara bud’i,ALLAH yabarka da Siddiqa tazama tauraruwarka har gaban abada.Yadda yayi furucin yasa sukayi dariya.
Sudaida tarufe musu motar itama tana godiya,Julaibib yasunkuyo”toh kagaishe mana da Hajiyarmu kace mata munanan zuwa mata yawon sallah ta ajiyemin dambun nama,tasa amin kilishi me tsomen aya,yanzu ma zan kirata in fad’a mata. Yad’aura belt yana dariya”toh kura duk kai kad’ai? Yaran sunata tsalle daga cikin motar suna d’aga hannu sunama su Julaibib adabo,a hankali yaja motar suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa tasha kwana ta6acema ganinsu.
K’arfe hud’u na yammacin asabar motar Julaibib ta tsaya a k’ofar gidan Hajiya.A d’akin-shak’atawa suka sameta tana waya,tagama tasauke wayar a kunnanta tana murmushi”lale marhabun,yau ina da manyan baki. Takalli Sudaida cikin tausayi dan ta kasa zama a kujera, zama tayi ak’asa tana matsa k’afafunta da suka fara kumbura alamar ciki ya tsufa wash…tafad’a tana yamutsa fuska”sannu Sudaida ALLAH yaraba lafiya.
Kai Julaibibi Sudaida tadawo kenan sai ta haihu ko?A ah jibi zamu koma ni bazan tafi in bartaba. Hajiya tagyad’a kai”madallah,to idan haihuwar tazo sai kuyi yaya?Hala ka ta6a kar6an haihuwa ne? Yashafa kwantaccen bak’in gashin kanshi”wannan karan dai zanyi,Hajiya bar wannan maganar kinji,ai haihuwar ma da saura,yad’an kalleta kuma ni gaskiyar magana”I can’t do without Zaujatiii… Besides me.
Bashakka Julaibibi zama da mad’aukin kanwa…ni dai na sanka me kawaici amma wannan matar taka me suffar takand’a ta fara koya maka rashin ta’ido ko?To kaji dakyau baza tabikaba,to me zata maka da wannan tsohon cikin?Sudaida tayi murmushi tana zancen zuci”lallaima Hajiya ni ce na koya ma Julaibib d’in rashin ta’ido?Yaya d’ansarai wallahi gwani na gwanaye ne bar ganinshi haka Ustazu-Ustazu baya san magana hummm… Takyalkyale da dariya tuno abinda yagama fad’a mata daren jiya data keta wani sha mishi k’amshi dan ta karance tsabbb…da abinda yake so.
Tad’an turo baki gaba”Hajiya ai gwamma in zauna a suffar takand’a da dai in zama tashi da nishi…bakiji kirarin muba?Bena bakya tsufa sai dai kiyi girgiza ki sake sabon gashi,kuma waya jazamin wannnan k’aramin jikin idan ba ke ba?Takalli Julaibib”Yaya d’ansarai…Kasha kuruminka k’afata k’afarka ai tare ta gammu.
Yauwa Zaujatiii…tabashi hannu suka tafa, tad’an yafito shi zo kaji,yamatsa kusa da ita tasaita bakinta a kunnanshi tana rad’a mishi wata magana, suka kalli juna,yad’age gira yana nunata da yatsa cikin yar dariya”da gaske Zaujatiii…? Ta amsa kai tsaye”na rantse maka da girman ALLAH.Hajiya takama ha6a ba shakka”wato ana nuna miki ma’aiki kina rintse idanu,da wannan tsohon cikin kike wannan iya shegen k’auri da kare? Tawatsa hannu”to ai shikenan jiki magayi baki kuma mafad’i.Yamik’e barinje shago wajen su Baba”ke sai na dawo zamu tafi gidan Kawu ko? Toh adawo lafiya.