
Sak’onshi yashigo wayarta”Zaujatiii… Kar kiyi bacci fa…ina lalla6atane.Takashe wayar tayi kwanciyarta”kai ka sani.Sai da baccin Bilkisu yayi ni sa sannan yabita…yakunna fitilar wayarshi yana haske mata fuska,tasa hannu takare fuskarta sannan ta bud’e idanu”Zaujatiii baki ga sak’ona bane? Na gani. Tafad’a a taik’aice…Sudaida ta kin fahimce ni amma kika share ni kina ji Bilkisu ta tasani agaba.Tadad’a gyara rufa”uh ai duk a cikin lokacin tane, yaushe ko za a bar ranta ya6aci sarauniya me d’ansarai.Yad’an daki bayanta yana matsa mata hannu a hankali”yau haka kike jin fad’ar sunan nawa d’ansarai gatsau ba ko sakayawa?Tayi shiru kamar ba da ita yake magana ba.
Yagewayeta”to gani na zo a bani bashi na… Duk da ranta a 6ace yake amma bata hanashi abinda yake so ba…shima ya fahimci haka shi yasa yake jinta wata ta musamman a sararin zuciyarshi, Sudaida ba dama ne wallahi,ta gama lak’antar shi,a cikin ruwan sanyi take hukunta shi sai yazo yana bata hak’uri da bakin shi dan a zauna lafiya…Yawani narke kamar k’aramin yaro”Zaujatiii… Ina k’aunarki fa I can’t do without you.Batace kome ba tacigaba da bashi wasu sak’onni sai shima ya biyema yarima su sha kid’a…
A safiyar asabar yara sun sami hutun makaranta Sudaida tamatsa sai sun tafi Zonkwa dan watanninsu biyu basu je,tagama shirinta tsafff sannan tashiga d’akin…baki bud’e take kallansu da mad’aukakin mamaki baccinsu sukeyi hankali kwance ya lull6esu da bargo,tun d’azu fa tahad’a ruwan wanka za ta musu yace tabari zai musu taje tahad’a musu abinda za suci suna gamawa sai tafiya amma shine bayan fitarta suka koma su kayi kwanciyarsu,wato sune masu idanun jin bacci ko? Tayaye bargon tana tashinsu ya bud’e idanu,ta6ata fuska “haba dan ALLAH Yaya d’ansarai kai bakiyi wankan ba,su baka musu ba?
Yaziro k’afafunshi k’asa”kin san akwai sanyi ban san sanda baccin yasake awon gaba dani ba barinje in yi…tunda yashiga wanka ta san ko ya fito bazai musu ba, dan haka tatashi Walida taje tamata sai da tagama shiryata sannan ta tashi Bilkisu tamata tad’auko shadda getzner ruwan makuba yasha aiki da zare ruwan zinare da wasu k’ananan duwatsu masu d’aukar idanu saboda kyallinsu riga da buje da d’an kwali,tana ganin kayan tawani shagwa6e fuska wai ita baza ta sa kaya irin na Walida ba wanda Baba yasiyo mata dayaje Umrah doguwar rigar larabawa shi za tasa.
Sudaida ta dafa kafad’arta da sigar rarrashi”kisa wannan kinga anko fa za kiyi ke da k’anwarki, yanzu zan miki wannan kwalliyar sai kuyi Selfie da waya ta.Walida tayi tsallan murna”Yehhh…ni ma na iya tsayuwa da shan baki a selfie,Bilkisu ta ta6e baki ita yar gata haihuwar samu sai kawai tafashe da kuka tana bubbuga k’afa ita fa dole rigar larabawan nan za a d’auko mata.Sudaida ta tsare ta da idanu”idan ban d’auko ba fa?Kawai sai ta kwanta a k’asa tana burgima tana k’ara fashewa da kuka dan ta san Julaibib zai shigo…Haushi yakama Sudaida tagyad’a kai “lallai mugun gata asara,rashin shi kwata-kwata illah…
Tanunata da yatsa”ke Bilkisu ki rufe min baki.Bilkisu tacigaba da ihu da burgima tana kiran Julaibib”Baba kazo ka d’auko min doguwar rigar larabawan daka siyo min,Mama wai bazan sa ba. Sudaida ta kifa mata mari ba za a d’auko ba… Taduba yar k’aramar dorinar ta take musu barazana da ita tarasa kawai sai ta jawo wayar caja tanad’e ta a hannu”baza kiyi shirun ba ko?Ga mamakinta kawai sai tagyad’a mata kai alamar eh.Ai batayi wata-wata ba shaud’a mata iya k’arfinta caraf a kan idanunshi.
Bilkisu tagigice dan taji dukan yadda yakamata tak’ara fashewa da kuka kamar zata shid’e, ya d’auketa ya zubama wajen data shaud’a mata idanu,cajar ta fito rad’am da kwanciyar jini a wajen toh jikin hutu ko ina lukwui-lukwui da tsoka ga kuma farar fata,yakalleta fuskar shi ba wal-wala”Sudaida baki da hankali kasheta kike so kiyi? Dan tace ga kayan da take so sai yazama laifin da har sai kin mata wannan dukan?An siyo kayan dan ayi meye dasu?Ya rufeta da fad’a kamar zai daketa,Sudaida tayi shiru tana zancen zuci”wai ita ce za ta kashe mishi ‘ya saboda ta daketa sau d’aya.
Tashi ki d’auko mata rigar.Takalleshi cikin idanu”na rantse da girman ALLAH ba zan d’auko ba!Yashare ma Bilkisu hawaye”to fad’a min in da take in d’auko…Cikin fushi tace”wannan rigar haramiyar ta har abadan duniya wallahi.Shima cikin fushi yajuya rungume da Bilkisu”kar ki d’auko ki dafa kici…
Sharrr…sharrr wasu hawaye masu d’umi suka zubo mata akan Bilkisu suke wannan ja-in-jar da Yaya d’ansarai?Ranta in yayi dubu ya 6aci wai shi wani irin so yake ma wannna yarinyar da har zai ga laifin ta amma yakasa tsawatar mata?Wannan makauniyar soyayyace wacce daga k’arshe baza ta haifar da d’a me idanu ba wai Zaujiii…Shine yake mata wannan hayagagar…za ta kashe mishi ‘ya… Tadafa rigar taci tunda baza ta bata ba…taci kukan ta ta k’oshi tayi shiru tunani barkatai ya cika k’wak’walwarta…yawa-yawan Ya’yan da suke samun matsala a rayuwar su to hakan yana samo asaline daga irin mugun gatan da ake nuna musu tun zamanin k’uruciya.
Sai da hantsi yadubi ludayi sannan Walida tashigo d’akin cikin wata shiga ta daban riga da wando da k’aramin hijab yan kanti…ran Sudaida ya kuma 6aci wato fitan da yayi sababbin kaya yayafi ya siyo musu kenan? Walida takalleta”kingani Baba ya siyo mana wasu kayan?Tagyad’a kai”na gani Walida. Mama kuma na ce mishi ALLAH amfana… Tad’an shafa kanta”yauwa Innarmu ALLAH yamiki albarka haka ake so duk wanda yabaki abu kisa hannu biyu ki kar6a kuma kiyi godiya…tayi yar dariya”wanda yagode sai ALLAH yak’ara mishi haka kika fad’a min ko? Eh Innarmu ashe baki manta ba.To nagode da kike rik’e duk abinda nake fad’a miki. Tad’anyi jimmm…sannan ta kalli Sudaida”Mama ita Yaya Bilkisu fa da Baba yakawo sai tace wai basu da wani kyau sai da yahad’a mata lemun tuffa da karas sannan ta yadda tasa…wai ita dai na Umrah nan take so,shine yace sai ya koma wata Umrah,damu zai tafi muje can muza6a irin wanda muke so da kanmu…
Walida… Suka jiyo muryar shi daga d’akin-shak’atawa yana kiranta,sai ta d’an bud’e idanu “Mama…Baba ne yace wai kizo mutafi na manta… Tafita da gudu tana amsa kiran na shi.Takoma tayi kwanciyarta”da bata hak’ura ba baza suyi tafiyar ba kenan kome?Tayi k’wafa”wallahi abu d’aya zai sa tabisu dan tafad’a ma su Baba abinda yake yi, da ba in da za taje,gwamma ayi ma tufkar hanci,ai gabama da gabanta aljani ya taka wuta,ita baza ta iya cigaba da ganin kayan takaicin nan ba nama na jan kare.
Ko kallanta bai yiba,to itama a cikin fushi take dan haka ba wanda yakula wani har suka isa Zonkwa. Inna taji dad’in ganinsu sai ina za a saka ina za a aje takeyi da jikokinta haka suka yi wunin farin ciki.Bayan sallar magriba Sagir k’aninta daya yazama matashin saurayi takira yaraka ta wajen gyaran gashi har Julaibib yadawo basu dawo ba shima yazauna ana ta hira,Bilkisu Megadon Zinare an samu abinda ake so dafadukar cus-cus me nama da kayan lambu take ci,ga Baba ya kawo mata yoghurt tana taci tana sha cikin jin dad’i da kwanciyar hankali.
Sai wajen takwas da rabi suka shigo Sagir yasake gaishe dasu Baba sannan yamusu sai da safe,ita kuma taje tayi sallar Isha’i ta zubo abinci tanaci;yad’an saci kallanta tayi kyau sosai amma ko nahiyar da yake bata kallaba har tagama ci takai farantin d’akin-girki sannan ta dawo ta zauna tad’an kalli yaran”kutafi d’akin-shak’atawa ku kalli wannan shirin na Balarabe da bai iya gaza gurasa ba…Suka mik’e da Sauri”ehhh kuwan Mama…