GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tad’an sunkwui da kai cikin ladabi”Baba ina son magana da ku.Yagyad’a kai”to Sudaida… Julaibib yayi wani huci”me wannan yarinyar take nufi? K’arar shi za ta kawo wajen su Baba?Ina jinki Sudaida me yafaru?Muryar ta tafara rawa alamar zuciyarta ta karye”ni dai Dan ALLAH Bilkisu zata dawo gidan nan da zama zan had’o kayanta… Inna tace”ashsha to me yayi zafi idanu za suci wuta har haka Sudaida?Inna kusan kullum sai mun samu sa6ani da Yaya d’ansarai a kan ta,wai d’azu da safe har yana fad’a min zan kashe mishi ‘ya saboda na daketa,kuma agaban idanunta ya rufeni da fad’a kamar zai dakeni,Lillahi warasulihi Inna ace kamar Bilkisu sai abinda take so za a dinga yi a cikin gidan nan?Sannan ita ba ta laifi, ba ta kuskure kome tayi dai-dai be a wajen shi, wannnan abinda yake yi ya dace da tsarin ingantacciyar tarbiyya!?

Ni dai ta zauna a wajenku kawai.Inna ta numfasa to me yakawo dukan?Sudaida duka ai baya ba da tarbiyya sai dai yakangarar,ni ma ba na son duka.Wani haushi yamamaye ta wallahi mantawa tayi kuka takawo gidan mutuwa”ai kamar yadda Bilkisu take hantar Yaya d’ansarai to haka abun yake a wajen Inna son ta take kamar me,shi yasa ba gidan da take son zuwa kamar nan dan Inna tana biye mata ne,yanzu ma abincin daren ta daban tadafa mata.

Tasa hannu ta share hawaye”shikenan Insha-ALLAH daga yau ba ruwana da duk abinda Bilkisu za tayi ai ALLAH yagani bani da wani k’arfi ne dan haka zan kyamaci kome a zuciyata.Auna had’a idanu ya gallamata harara”ai dukan yayi yawa ne har ciwo kika ji mata to me zaisa bazanyi fad’a ba.

Baba yayi tsaiii…yana nazarin kalamansu d’aya bayan d’aya,yakad’a kai”Maimunatu wannan hukuncin na ki na adalci ne kuwa?Tsakani da ALLAH Sudaida ta fiku gaskiya;kar k’aunar yarinyar nan tarufe idanunku fa,idan an ciza to yakamata a hura…yanuna Julaibib”Malam d’ansarai da ilminka da girmanka amma kana irin wannan abun?Kiwo aka ba ka game da sha’anin Iyalinka fa,shi itace tun yana d’anye ake tank’warashi…kana nunama Bilkisu tsananin gata amma ba kwa6a to an yi ba ayiba kenan…an 6ata goma biyar bata samu ba,dan me za tayi laifi ba za a hukunta taba?Mahaifiyar tace fa idan ba a nuna mata abinda takeyi kuskure ne tun yanzu ba,to a gaba ma cigaba dayi za tayi,kuma duk fad’an da zaka ma Sudaida to na rok’eka da girman ALLAH kadaina yi a gaban Ya’yanku,hakan yana gur6ata tarbiyyarsu,dan ALLAH Malam d’ansarai idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba kaji ko?

Yanuna ta”ke kuma Sudaida ba ke za ki yanke hukunci na rad’in kan ki ba kome ya miki,tunda shine ubansu shine a hakku a kansu dan shine shugabanku ke da yaran gaba d’aya.Ubangiji ya muku albarka,sannan duk yadda ranki ya6aci kiyi hak’uri dasu kinga banji dad’in furucinki akan Bilkisu ba,ke uwace bakinki amsashshene akan ta,dan haka ki janye wad’annan kalaman na ba babu ruwanki da duk abinda za tayi,ai kece kuwa me ruwa da tsaki yaushe za ki biye ta wani d’ansarai Ya’yanki kadararki su shiga garari,duk abinda ya kumayi ki bugo waya ni dake ki fad’a min zai sha mamakin yadda zanyi wallahi ALLAH kinji na rantse ko?

Kalaman Baba sun tausashi zuciyarta”to Baba nagode ALLAH ya k’ara girma.Inna ma tajijjiga kai toh na gano kuskure na kiyi hak’uri Sudaida ALLAH yamuku albarka,ku tashi kitafi gida dare yana dad’a yi,ta lek’a d’akin-shak’atawa duk sun yi bacci Inna tace suyi tafiyarsu kawai.

Suna zuwa gida taje tayi wanka tayi kwanciyarta shi kuma yatafi d’akin-girki zai dafa shayin na shi na fama taja tsaki sai kaje kayita sha…takwanta cikin tunanin tsohuwar soyayyar su..ita dai ta san da son Julaibib ta girma kuma ba tajin da wani abu dazai rage k’aunarshi a sararin zuciyarta,to amma wannan yawan sa6anin da saka fara samu ita tata k’arfin k’aunar ta zuciyarshi ce ta koma kan Bilkisu da kuma kud’in da yakeji yayi?Ko kuma giyar Ilmi da dukiyace tafara bugar dashi…!?

Tad’auki wayarta takira”Umma kiyi hak’uri na kiraki da daddaren nan wata magana nake so muyi.Ba kome me yafaru ne?Hawaye suka zubo mata”Umma ni da Yaya d’ansarai ne…sai kawai tafara kuka,Umma bata hanata kukan taba sai da taci ta k’oshi tabari dan kan ta…Umma tasauke numfashi “Sudaida kiyi hak’uri ni bazan shiga tsakanin ki da d’ansarai ba ai kunfi kusa,kuma ai ba a ta6a zaman tare ace wani bazai sa6a ma wani ba…fuskantar matsalolin aure irin wannan ai dole ne dan haka ki k’ara hak’uri kuma ki yawaita addu’a kome yayi farko yana da k’arshe…kuma in dai akan Bilkisu ne to fa dole sai kin kawar da kai…ba kome za ki nuna ya dame ki ba…ki dai kiyi k’ok’ari ki jata ajiki kinga ai tafi shak’uwa dashi ko? Eh Umma…to ko ni nan a yanzu nagano wasu kura-kurai danayi game da tarbiyyarku to amma har kwanan gobe ina godema ALLAH ina godema Mama wacce ba dan ita ba da kuma kun samu tasgaro dan haka ki natsu ki san abinda kike yi game da sha’anin tarbiyyarsu…

Haba Sudaidan d’ansarai kika juya shi yayi wasu abubuwan da bai so ba sai kuma wannan za ki fara raki? Ki bi dashi ta siyasar rayuwa ko bai daina wasu abubuwan ba to amma ai za ki samu sauk’in wasu,Umma tad’anyi murmushi”taurin kan Bilkisu da kafiya kema fa haka da kike k’arama kinyishi,shi yasa bana miki da wasa…ita kuma sai abun yahad’u mata da gata…

Julaibib yashigo lokacin suna sallama da Umma.Yakar6e wayar”k’arata kika sake kaiwa,me kika fad’a mata?Abinda kunnuwanka sukaji.Yayi murmushi”ALLAH ko?Tajijiga kai”bawai…yashiga rarrashi”kiyi hak’uri Sudaidan d’ansarai ni ma na gane kuskure na,bai kamata ace Bilkisu ce zata shiga tsakanin muba,ai tare tazo ta ganmu,lallai ke macen albarka ce dakika jajirce dan ganin na dawo kan hanya nagode Zaujatiii…ALLAH yamiki albarka ya saukeki lafiya.Sai taji zuciyarta ta yi wasai”ta marairaice Zaujiii..to idan banyi hak’uri ba me zanyi bayan mun zama k’arfe da mayen k’arfe,mutu karaba takalmin kaza…?Hummm fushin masoya hutuhhh…

Rawa da k’afa d’aya sai gwani.
Da ba ‘yan koyo da gwanaye sun k’are…

5 Rajab 1441
28 February 2020

We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION

{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na ashirin da hud’u.

Gobe zan tafi Sudan fa…takalleshi wani iri” haba dan ALLAH shine baka fad’amin ba sai da daddaren nan?Yagyad’a kai”ai dan ma mun shiryane da sai na tafi zan turo miki sak’o ni nawuce sai ALLAH yamin dawowa. Tad’an harareshi”gaskiya banji dad’i ba,ba fa abinda na shirya maka.Uh bakome kibani abinda yasauwak’a,kin san ni bana raina kad’an”da hanau ai gwamma mannau. Tare suka shirya kayan tafiyar.Washe gari jirginsu yad’aga.

A wad’annan shekaru goma sha ukun Julaibib Abdullahi d’an Sarai ya taka matakai da yawa a bangaren ilmi har ya zama shehin malami ferfesa gangaran(Professor)Yasai k’aton fili yana gina had’ad’d’iyar makaranta ta zamani bangare biyu bangaren addini da bangaren boko,aiki tuk’uru ake yi k’asa tanata cin kud’i,makarantace tun daga matakin prenursery,nursery,primary da secondary,abubuwa k’alilan suka rage mishi a bud’e makarantar,yana kuma da buri nan gaba yad’ora makarantar zuwa Jami’a me zaman kanta, yana kuma fatan makarantar tacigaba har bayan rayuwarsu,Ya’yansu su cigaba har jikoki…ta shahara har zuwa sauran k’ananan hukumomi da jahar Kaduna da d’aukacin sauran jahohin dake tarayyar Nigeria.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button