
Abubuwan rashin jin dad’in da suka faru kuma shine tun bayan yak’in Zongon-Kataf da yak’in da akayi a k’waryar cikin Kaduna na k’addamar da shari’ar musulunci wani hargitsi da kisan rayuka bai kuma faruwa a k’aramar hukumar Zangon-Kataf ba,to amma a ‘yan kwanakin nan manyan kabilun yankin Bajju da Atyap da sauran kabilu da basa sallah sun fara neman hana musulmai rawar gaban hantsi,takalan fad’a ba irin wanda ba sayi to amma bai damu hausawa ba,saboda duk fad’in doron duniya kowa ya shaida duk in da kaga musulmi kuma bahaushen mutum to ba wani abu yakai shiba face neman ilmi ta yadda zai bautama Ubangiji ba tare da jahilciba,sai kuma neman kud’i,kuma musulmi na da sauk’in halin da basa son tarzoma,wannan dalilin yasa suka d’an sararama hausawa amma ba hak’ura sukayi gaba d’aya ba,aka cigaba da zama cikin aminci da amana kamar yadda zuciyar bahaushe take a ko ina.
Tana kwance a d’akin baccinsu lullu6e da bargo tana chat da Nasmat,video call d’inshi yashigo ta d’aga da sallama,ya amsa da wani salo irin nashi yana murmushi”eyehhh… Kaga Hajiya baki da wata matsala.Tayi yar dariya”godiyar Ubangiji a kowani hali da yanayi Zaujiii…Yagyad’a kai”ina yaran?Suna gidan Inna wai a can zasu kwana,yad’auki kofin gabanshi ya kur6i abinda yake ciki yamayar ya ajiye. Me kake shane?Shayi tad’an yamutsa fuska”asha lafiya.
Zaujatiii…Yakirata.Na’am.Nayi kewarki, bakya barina inyi ayyukan dake gabana,gangar jikina ne kawai a Sudan amma tunanina da zuciyata suna gida wajenki,gashi kwanakin basa sauri,anya ba visa za kiyi ki taho ba?Tawani marairaice”ni ma nayi kewarka,Yaya d’ansarai…Esbeer kaji?Kamai da hankali akan aikin da kaje yi,ai kamar yaune zaka dawo gida katarar da zuri’a da Iyalinka cikin k’oshin lafiya Insha-ALLAH,ka yi kwanaki goma sha shidda,saura kwana hud’u kacal ai…
Zaujatiii…na rantse miki da ALLAH daga shi ba wani kece duniyata,ina k’aunarki fa.Tagyad’a kai cikin gamsuwa da kalamanshi bawai shaci fad’i bane”ni ma haka Zaujiii…Ina k’aunarka a kowani hali da yanayi, baka da abokin tarayya a irin k’auna da soyayyar da nake maka”in poor and in rich,in sickness and in health…till death due part us”yaja numfashi yafesar da iskar ta baki ta hanci”oh ya rahman…wani shauk’i da d’okin ganinta yamamaye shi…sun dad’e suna musayar kalaman k’auna sannan suka fara magana akan kud’in daya turo aka sai wasu kayan aiki na ginin makaranta.
Hantsi yadubi ludayi tashirya cikin doguwar riga kamfala,tatafi gidan Inna suna tattauna wasu al’amura daya shafesu,Abu me aikin da Julaibib ya d’auko ma Innar tashi tashigo da sallama ta ajiye farantin hannunta a gaban Sudaida tana tsokanarta “uwar biyu tashi kici kwad’on zogale na miki naga kwanaki biyu in dai kinzo abinda kike tambaya kenan, yau kuma naji baki tambaya”tamik’e zaune dakyar tana murmushi”nako gode miki Abu ba kad’an ba,sannu da aiki,tad’iba da bismillah takai bakinta, tafara taunawa cikin gyad’a kai “gaskiyar magana wannan k’uli-k’uli akwai d’ankaren dad’i da d’and’ano, tasa hannu a jaka taciro dubu biyu tabata”yaba kyauta tukwuici Abu.Abu takar6a tana godiya “madallah ALLAH yak’ara bud’i,yasaukeki lafiya… Tad’anyi murmushi kawai,sai Innace ta amsa da” amin. Abu tajuya takoma d’akin-girki tana yaba halin kirkin zuri’ar Hajiya.
Bilkisu tashigo cikin shagwa6a ta rungume Sudaida tabaya”Mama kince za ki kira min Baba mu gaisa.Tad’an harareta”kin fa dameni idan nace na fasa sai ayi yaya dani?Asma’u da shigowarta kenan ta amsa dama me hali baya fasawa”wallahi abu me sauk’ine muyi k’uli-k’ulin kubura dake.Bata kula Asma’u ba tafara kiranshi,cikin d’oki Bilkisu ta manna wayar a kunne”Baba afqadtuka(nayi kewarka) Yayi dariya ALLAH Megadona?ALLAH kuwan Baba jiya ma nayi mafarki wai ka dafa mana naman talo-talo naci nak’oshi…tanata mishi shirme yana dariya… Toh ni dai gaskiya idan bazaka dawo ba zan sa Kawu Aminu yakawoni in da kake ai yasan wajen ko Baba?Eh yasani.Ina Walida?Tatafi da Kawu Aminu siyo kindirmo a riga ni dai nace baza niba,shine wai yace idan suka dawo suma bazasu sammin ba,Baba kace Mama yau ta soya min dankalin turawa da kwai. Yagyad’a kai”to Bilkisu na har da lemun kwakwa ko?
Tajijjiga kai tana tsallan murna”zan rage maka har kadawo,yaushe zaka dawo d’in?Insha-ALLAH gadan bil-lail.Tawani fasa ihun murna Sudaida takwace wayar ta buge mata baki”ban hanaki wannan ihun murnan ba?Kawai ki cika mana dodon kunne.Inna tafara fad’a”nifa Sudaida ban san sanda kika 6aci da saurin hannu ba,tad’anja tsaki”haba ina amfanin irin wannan?Tayafito Bilkisu da hannu”zo nan muga bakin…yauwa kingani ko har ya fara kumbura.Sudaida tace”kiyi hak’uri Inna,Inna bata kulataba sai da tagama lalla6a Bilkisu ta daina kuka sannan ta kalli Sudaida”ya wuce amma a dinga kulawa… Tayi murmushi”to Inna a ranta tana fad’in “wuuu na manta ashe hantar Inna nata6a a gaban idanunta.
Dawowar shi da kwana biyu ya tasata a gaba wai dole sai ta raka shi wata seminar,sun gama abinda za suyi suka wuce kasuwa yasai kayan wuta na mak’udan kud’ad’e da za a sasu a makaranta.Sudaida tayi tsaiii…cikin tafakkurin abinda za ta sai ma Yaya Aminu wanda zai burgeshi har yayi amfani dashi,saboda abubuwa da yawa basu d’ad’ashi da k’asa ba.Zaujatiii…tunanin me kike yi haka?Takalleshi”Yaya Aminu na rasa me zan sai mishi bani shawara”yayi murmushi”turare da kayayyakin da yake ayyukanshi dasu(artistry equipment) sune kawai zai yaba ko?Yauwa Yaya Julaibib wannan shawara taka ta samu kar6uwa nagode.
Bayan sallar Isha’i taje gida tasame shi a d’akin-shak’atawa yana shan fura da nono,ya maida ludayin cikin kofin yana amsa sallamarta”Sudaida kece haka da daddaren nan,ina autan Innan?Ta zauna a k’asa tana maida numfashi kamar wacce tayi gudun famfalak’i saboda nauyin da cikin ta yayi”su Bilkisu yatafi d’aukowa a gidan Inna,ni kuma nagaji da jiranshi shine nayi tahowata.Da sauri ya d’auko ruwa ya zuba a kofi ya mik’a mata,har ta kai tsakanin la66anta da bismillah yasa hannu yakar6i kofin”yi hak’uri ina zuwa,bulkodi(glucose D) yad’auko yazuba mata babban cokalin cin abinci d’aya a cikin ruwan yajujjuya sannan yabata,ta shanye duka,suka kalli juna suna murmushi”yaya a k’aro?A ah Yaya Aminu nagode kwarai taurarona.
Yazauna”da kinyi zamanki, kina kirana a waya ai kin san bazank’i zuwa ba.Yaya Aminu ba kome ai nima ina motsa jiki ne.Ya kalli k’afafunta da suka kumbura,har ranshi yaji tausayin ta”mata suna shan wahala da ciki fa,duk mace me ciki ai kana ganin yanayin ta ka san abin ba a cewa kome”lallai biyayya ga mahaifa dolen-dole ne ga duk mai son gamawa a doron duniya lafiya”.Sannu kanwata to baza kije asibiti su baki magani ba? Tayi yar dariya ganin yadda yadamu dama haka yake nuna mata tausayi duk sanda suka had’u,tasa hannu tana murza k’afafun”wannan ba kome bane,ba shi da wani magani wasu suna yi yayin da cikin su ya tsufa wasu kuma ba sayi,duk cikina bai wani girma amma gashi na fara wancan makon ma naje an dubani kome nawa lafiya lau.
Yakad’a kai”toh Ubangiji yaraba lafiya.Amin Yaya Aminu nagode”ga wannan.Yakar6i ledan, yad’ago yana murmushin jin dad’i bayan yaga abubuwan da suke ciki “yanunata da yatsa duka na Aminu ne shi kad’ai?Tajijjga kai.Toh nagode ba kad’an ba”ALLAH yamiki albarka Sudaidan d’an Sarai. Sukayi dariya.Sun d’an ta6a hira har zuwa takwas da rabi sannan yace ta tashi yarakata gida dare ya farayi,suka jera suna tafiya a hankali suna magana har suka zo k’ofar gidan”shige gida kinji dare na dad’ayi ga hasken farin wata kar yasa miki mura.Sai da safe ko?Tagyad’a kai”ALLAH ya tashemu lafiya tabi bayanshi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta.