GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranar wata laraba a watan Rabi’u Awwal kabilun garin suka tashi da neman rigima ba wanda yataka ko ya zubar musu suka fito suka dinga zage-zage da k’one-k’onan tayoyi nan da nan gari yafara rikicewa kowa yatashi a wajen sana’arshi sai gida hankali a tashe, basu suka daina wannan abun ba sai wajen k’arfe d’aya na dare.

Sudaida ta sauke gwauron numfashi “Zaujiii…garin nan yafara bani tsoro,sallolin yau gaba d’aya kowa a gidanshi yayi bayan ga masallatai nan, amma saboda tsoron wasu marasa sallah an rasa wanda zai fita?To wai me aka musu? Yayi murmushi “kome zai wuce Insha-ALLAH gobe za a tattauna da Agwam Bajju (Sarkin Bajju) kin san shi mutumne me san zaman lafiya na san kuma zai ja musu kunne Kwanta muyi bacci kinji”gobe asubanci zanyi zuwa Gidan-Waya, har Sudaida tayi bacci amma shi idanun shi biyu yana tunanin al’umara mabambanta, lokuta da dama shima yanaji kamar yatattara yabar garin,to amma idan ya bar garin ai anyi gudu ba a tsira bane”gudun da ba a tsira ba kuwa kwanciya ta fishi”.

Gaba d’aya zuri’arsu a garin suke Iyaye da kakanni,ai duk in da za shi dole dai sai ya dinga zuwa duba Iyaye da yan’uwa dan ya san mahaifanshi ba yadda za suyi su bishi ba,yasauke numfashi “zaman su a garin Zonkwa cikin wad’annan kabilu muk’addari ne tun daga Lauhul-mahfuz, k’addara ta riga fata,sai dai ya kamata suyi ho66asa dan suna so su fara musu cin kashi, shekaru kusan goma da suka wuce haka suka zauna cikin fargaba saboda fad’an d’aya 6arke sakamak’on k’addamar da shari’ar musulunci da akayi a Kaduna, a cewar su wai an kashe musu mutane da yawa a Kaduna dan haka suma za su d’auka fansa a kan musulman da suke zaune anan,tsawon lokaci haka suka zauna cikin tashin hankali,har dai kuma Ubangiji ya kawo k’arshen abun ba tare da sunyi kome ba…da wannan tunane-tunanen bacci yayi a won gaba dashi.

Sai dai cikin baccin na shi yayi mafarkin daya dinga na shud’ad’d’en shekaru”Kasham dai yau ma yasake gani cikin shigar Fulani kirar kalangunta ya fito rad’am kamar dai wancan lokacin amma idan tayi magana sai yaji muryar Sudaida…ya farka yanata nazarin wannan mafarki”toh me yak’un sane?…baccin da bai kuma komawa ba kenan har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahin farko…

Hausa/Fulani Community Development Association(HAFCODA)Taza6i manya daga cikin su, suka tafi fadar sarkin Bajju,ya kuma kar6esu cikin mutuntawa, sun gabatar da abinda yakawo su,nasan zaman lafiya,da hak’uri da juna,shima Agwam Bajju a zahirance dai ya nuna 6acin ranshi”dan sanin asirin ciki sai hanji,ya kuma tabbatar musu su kwantar da hankalinsu lallai zai tsawatar musu ta hanyar yin gargad’i a dukkan majami’u(churches)ga wad’annan samari yan zauna gari banza masu son tada hargitsi,idan kuma basuji ba to lallai zai buga musu sandar shi(a al’adarsu idan har agwam Bajju yace zai buga sandarshi to duk abinda mutum zaiyi to ba zaiyi nasara ba)

Wad’anda ba son zaman lafiyar suke yiba suka had’a taron su.Shugaban nasu yabisu da kallo d’aya bayan d’aya”kunji abinda yake faruwa, dama hausawa masu san zaman lafiya ne tunda duk abinda muke musu basu ta6a mai da martani ba…toh ni dai kawai bana son ganinsu a garin mune,kome sune suke dashi sama damu sannan hakan bai wadatar dasu ba kullum aure mana Ya’ya suke k’arayi,wani abin takaicin ko da wasa baza kaga wata yarsu kace kana sonta zaka aureta ta yadda da kaiba,sai tace bata yadda ba tunda baka yadda da addinin taba,kunaji suna fad’a kakar za6e me zuwa zasu za6i mutum biyu daga cikinsu su tsaya takarar Chairman to kuna gani za su yadda su sake dangalama wani na mu k’uri’arsune?Yaja dogon tsaki”infact I’m sick and tired of seeing all those masu sallah bounch of idiot,we’ve to do something,something seriously againts them.

Wani daga cikinsu me rangwamen kafircin yace”da munyi hak’uri kawai ai mun riga mun zama d’aya,ga Ya’yanmu a cikinsu idan munyi yak’i mun kashe mazaje to yaya zamuyi da tarin mata da Ya’yansu?Nifa Ya’yana guda uku ne masu sallah.Cikin fushi shugaban nasu ya daka mishi tsawa”enough of this stupidity,so bloody what da Ya’yanka uku ne a cikinsu? Ko akwai ‘yata a cikinsu na rantse muku zan iya kasheta, ba sune shegu masu kwad’ayin abin hannun hausawa ba? To da irin suma zan fara kisa,so dubu nawa suna wulak’antasu? Yanuna mishi k’ofa yana mazurai”now get out! Kai baka cikinmu.

Yasake bin sauran da kallo,suma shi suke kallo suna jijjiga kai alamar gamsuwa da matakin daya d’auka,fuskokin nan babu rahama da tausayi kona sisin kwabo,idanuwa jawur saboda shan burkutu da hayakin maro.”nayi dai-dai?Suka had’a baki wajen amsawa”kayi dai-dai.Yakyalkyale da wata irin gur6atacciyar dariya da bata da dadin ji saboda giya da hayaki sun gama lalata hunhunshi”that’s very good of you… Suka rufe k’ofa suna cigaba da k’usk’us d’insu na yadda zasu canja salon takunsu akan hausawa, d’akin ya kaure da dariyarsu dan sun gamsu d’ari bisa d’ari da matakin da suka d’auka…

Hankulan jama’a ya kwanta an cigaba da harkoki kamar yadda aka saba,sai dai kuma watanni kad’an a hankali abubuwa suka fara rinca6ewa za a koma yar gidan jiya,aka sake komawa cikin zaman d’ar-d’ar,basu da wani kwanciyar hankali, harbin bindigogi daga daji haka yake shigowa cikin gari ba dare ba rana alamar suna koyan harbi amma abun duka ba sanda da yake kuma dama bahaushen me ban haushinne na tanko me kan bashi,hakan bai d’ad’asu da k’asa ba,su dai neman halalinsu kawai. Mtswww ALLAH yakyauta.

Gidan shiru saboda yaran yanzu a gidan Inna suke kwana a duk ranakun k’arshen mako,Julaibib ya d’auko musu abinci,tamik’e zaune dakyar suka faraci da bismillah yana kuma mata bayanin aikin kafa ma’adanar littafai(bookshelves)da aka fara a d’akin nazari da bincike na makarantar (library)Tayi lallausan murmushi”Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira,gaskiya naji dad’i wallahi.Amin Zaujatiii…

Cikin firgici ta farka daga bacci a sulusin daren,wasu irin munanan mafarkai takeyi duk dare,har fargaba duk lokacin da rana tatafi zata fad’i magriba ta kunno kai,saboda da zarar ta kwanta baccin dare zata fara wannan mafarkan masu tashin hankali da sanya damuwa a zuciya.Julaibib yana zaune yana cike wasu bayanai a na’ura me kwakwalwa yaji motsinta,yajuya yana kallanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta kama kanta da duka hannayenta cikin maimaita Istirja’i,rigar shimin dake jikinta ta jik’e sharkaf da zufa”Sudaida lafiya?Zafi kikeji haka?

Yamik’e barin kunna miki mukayyib. Takalleshi a rikice”Yaya d’ansarai ba zafi nake jiba,jikinta yakama rawa”kasan abinda nake gani kuwa?Wai…yatari numfashinta ta hanyar sa tafin hannun damarshi ya rufe mata baki sannan yakalleta cikin kulawa”ba wai bana so inji abinda zaki fad’a bane a ah ina miki kwad’ayin samun lada saboda bin umarnin Manzon ALLAH dan yayi hani da bayyana mummunan mafarki,duk abinda kike gani to ki nemi tsarin ALLAH akan abinda kike ganin,kiyi tofi a gefen hagunki sau uku”a’uzu billahi minashshaid’anir rajim “sai ki juya daga gefen da kika kwanta zuwa d’aya gefen.Wannan shine abinda yadace.Ta rungumeshi tana sauke numfashi”nagode da wannan tunatarwan.

Ranar wata Litini aka bud’e makarantar Julaibib a zangon karatu na farko me suna…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button