
Takalli Musaddiq shi kuma yayi saurin kau da kai”Shin da gaske ne abinda tafad’a? Yagyad’a kai “Aishi yasa tun farko nafad’a miki Julaibib bazai aureki ba danna sanshi farin sani.Tamik’e tana sa6a jakarta akafad’a” Shikenan amma ba hakan yana nufin na hak’ura da shi bane,ku ai musulmai mata hud’u kuke iya aura,dan haka ban damu ako tanawa zanzo ba,ni dai burina in mallaki Julaibib a kowani irin hali da yanayi,zanje inyi tunanin abinda zai fishsheni.
Tana fita Safiyya tadawo.Yayi murmushi yana mik’o mata hannayenshi “Amma gaskiyar magana kin burgeni”bata mika nata hannayenba,tagalla mishi harara”Shi me gayyarma ba shiga shirginta yakeyiba sai kai,ba kamar kid’iba sai kayan ganguna? Yafuzgota da k’arfi” Haba Safiyyahhh… Kina ganin wani abu zai shiga tsakanin mune?Kasham bata gabana. Tashagwabe murya”ai ba anan takeba an danne bodari aka,ni dai kawai ko?Tad’ago tana kallanshi.Yagyad’a kai” Uhun ke me? Ni dai kawai maganin kar ayi to tun wuri kar a fara..Yayi yar dariya yana d’an jan karan hancinta”To ranki yadad’e zan kiyaye”Yakamata kuwa hakan.Sai yad’an bata marin soyayya suka k’yalk’yale da dariya.
Kwanakin Julaibib uku a Kaduna sannan yadawo ranar laraba da yammaci,wata yar Seminar sukayi da k’ungiyar”Ansaruddeen”yana rataye da bak’ar jakar matafiya,godiya yakeyi ga ALLAH daya kaishi lafiya yadawo dashi lafiya sannan yashige gidan da sallama.Inna ta amsa sallamar da murnan ganinshi “Maraba da autana “Yazauna agefen tabarmar cikin murmushi,Iyaye dad’in ganine dasu,musamman idan kayi dace da masu ilmi da sanin yakamata. Fatanshi har kullum ALLAH yabashi ikon jiyar dasu dad’in rayuwa kamar yadda suka jiyar dashi,musamman ilmin addini dana boko da tarbiyar Al’Isamiyya da suka bashi.
Yacire takalmanshi masu rufi da safa sannan yagaisheta”Inna ya zafi”?Tagyada kai “Zafi kam akwaishi,sai dai yakusa k’arewa tunda damuna nagab da sauka.Yadi6o ruwan randa yanasha yaji dad’i har ranshi saboda k’amshin saiwoyin datake zubawa aciki dan k’arama ruwan armashi wajan sha yana zancen zuci”Inna duk lokacin da bana gida ruwan randan nan naki nake fara kewa,ya ajiye kofin.To Ubangiji yabamu damuna me albarka.Inna ta amsa da Amin.Yaciro mata tsarabarta sannan yamik’e yasa takalmanshi”barinje gidan Hajiyar mu”To ka gaisheta.
Daga gidan Hajiya yawuce gidan Kawunshi,yaran gidan suna zaune a d’akin-shak’atawa suna kallo,k’ananan suka taso aguje suna murnan ganinshi”oyoyo Yaya Julaibib,oyoyo Yaya Julaibib duk suka mak’alk’aleshi dan d’ansarai indai wajan kyautane to ba daganan ba,sam abin hannunshi baya rufe mishi idanuba, suna ganin ya bud’e jaka suka fara tsalle kowa yana fad’in “Yaya Julaibib bani, a ah ni zaka ba,nima ai na iya rabo Yaya Julaibib….yace a ah bari aba babba Sagir maza kaima Khausar taraba muku, yanunata da yatsa”banda ke a ciki,rabo irin na adalci kawai za kiyi a tsakaninsu.Tayi yar dariya”To shikenan Sagir kawo ledan.”waisu Mama basa nan ne? Eh sunje gidan suna. Yajuya shikenan na dawo anjima.
A zaure sukayi kaci6is,taja baya da sauri”Sannu da zuwa”ya amsa da yauwa.Daga ina kike? “Gidansu Nasmat.Ka siyo min tsaraba?Yad’an kalleta “Haba dai, babba dake acin tsaraba?Tayi yar dariya “Yanzu dan ALLAH Yaya d’ansarai wani girmane dani?Ina abin yake wai maye yacinye jariri?Ai duk girmana ban kai Hajiya ba,daga gidansu Nasmat naje gidanta na kuma tarar da ita tana cin tuffa kuma tace tsabarar dama kai matane.
To dake da Hajiya dayane?
Daga baya suka jiyo muryarshi.Tad’an karyar da kai gefen dama”Kai Yaya Aminu yanzu ni banfi Hajiya ba?
Ke dalla tafi kabamu waje, irinki goma baza su kama k’afar Hajiyarmu ba bare su fita,to ke asuwa?Karankad’a miya dake. Julaibib yace”ah to kin daiji ko?Ya tambayi Aminu”akwai ragowar kunun tsamiya a d’akinka? Kaima ka san ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar bata Fulani bace.Yace yauwa to kije ki d’auka kiyi farau-farau dashi.Tajuya zata shige gida”ai ni kunu koda d’uminshi ba d’ad’ani da k’asa yayi ba bare ragowa, zanzo har gida in kar6a,sai kaba Innarmu ta ajiyemin koda na zo baka nan…
…Kome na rayuwa naci dana sha an halicceshine dan d’an Adam,shakeru aru-aru tun kafuwar doron duniya,za kuma kaci har kagaji,basa k’arewa sai dai kagama rayuwarka katafi kabarsu…
…Rabo na me rabo ko kura tagani haramiyarta.
15Rabi’a Thani 1441
12 December 2019
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI ????
Daga alk’alamin ????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na hud’u.
Monday ranar aiki ko nasara na tsoronki.Ranar litini aka koma makarantun boko a zangon karatu na farko.Sudaida da Khausar sunfi kowa farin ciki saboda shigarsu aji d’aya a k’aramar Secondary,kuma a wannan lokacin aka turo yan TP(Teaching Practice) Julaibib na d’aya daga cikin wadanda aka turo makarantar su,to kamar yadda su Sudaida ke murna haka Kasham ma tayi murna dan makarantarsu d’aya.
Dasafe yashiga gidan cikin shigarshi ta fararan kaya.Yagaishe da su Mama, sannan yakalli Sudaida da take karyawa”idan kika bari nafito daga d’akin Kawu baki gamaba to ni tafiyata zanyi.Tamik’e tsaye tana addu’ar gama cin abinci nama gama barin kira Yaya Khausar sai mujiraka a mota.Gaisawa kawai sukayi da Kawun nashi yafito suka tafi.
Kasham tana zaune a farar kujerar roba a inuwar dalbejiya kullum tana ganin irin zirga-zirgan da Sudaida takeyi idan an tashi tara(break) tsak’anin wajan saida kayyakin da wajan da Julaibib yake yawan zama,da alama ita yake aika tasiyo mishi abinda yake buk’ata. Tasauke gwauran numfashi wato dai yana magana,kalli yadda Sudaida take dariya, duk yadda akayi shi yayi furucin daya sata darawa.
Bayan an koma aji yamik’e yashiga d’akin malamai(Staff Room)sai ganinta yayi zaune a tebur d’inshi magana zamuyi tafad’a cikin murmushi.Ranshi a 6ace yama rasa abinda zai fad’a sai kawai yajuya dama alli(chalk)zai d’auka to gwamma yatafi Principal Office yad’auki wani acan.Tabiyoshi da sauri”ji mana Julaibib,ka tsaya kaji abinda zan fad’a maka,idan kuma kaki to ina biye da kai duk inda kasa kafafunka.Bai saurareta ba yayi tafiyar shi,sauri yake yi har yana tuntu6e, abin yabata dariya”To wai shi Julaibib tsoronta yakeji da bayaso ya tsaya kusa da ita ko me?Ta tuno ranar data mamayeshi ta rungumeshi a Gidan-Waya yadda ilahirin jikinshi yakama rawa.Toh ni dai bana gane ma wannan tsoron naka wallahi.
Lidiya tak’araso wajan tana mata kallan takaici nama na jan kare”ai ke dai kin gama a sara Kasham,namiji yana gudunki amma ke kina ta shige mishi sai kace shine mahad’in numfashinki?Taja dogon tsaki”to kidai yi a hankali kafin dalibai su farga,dan kin san ba dad’i zaki jiba idan suka tasaki a gaba da wak’ok’in shak’iyanci.Tagyad’a kai”zan so hakan indai zasu danganta ni da Julaibib a cikin baitocinsu.Ke Lidiya bazaki gane kome ba dan baki fad’a tarkon so ba. Ai ko na fad’a tarkon so bazanyi hauka da wawanci da rashin aji a wajan da nasan ba a maraba dani ba.tawuce tabata waje.”Iska dai na wahalar da me kayan kara.
A sanda hantsi ya dubi ludayi na ranar a sabar,yana zaune a shagonsu yana lissafin mutanan da suke bi bashi kuma su kai shiru mak’atau balaguro a lahira”kamar sun sha nonon uwarsu,d’ago kan da zaiyi caraf idanunsu yahad’u.Yafara ambatan ALLAH a zuci.