GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Alfurqan Science Academy.

Musulman Zonkwa sunyi murna da farin ciki da samuwar wannan makaranta,Ya’ya dayawa an ciresu daga wasu makarantu an dawo dasu nan.Julaibib ya so kwarai ya zauna da Iyalinshi dan bata jin dad’i,sai dai hakanshi bata tadda ruwa ba dan da yammacin ranar ya mata sallama yakama hanyar Gidan-Waya washe gari da sassafe zasu tafi Jos asibitin k’ashi na Bima abokin karatunsune yayi hatsari a hanyar shi takomawa garin na su na Jos yakakkarye.

Sai k’arshen mako yazo,gidan Hajiya yafara zuwa kamar yadda yasaba,su Hajiya an dad’a tsufa sai dai Alhamdulillah tsufa me amfani tayi dan bata rikice ba,tana gane kome da kowa,sun dad’e suna hairarsu kamar yadda suka saba.Bilkisu kuma tagaji da jiranshi kamar yadda Sudaida tace mata ta zauna ta jirashi ba sai ta bishi ba ai zo.Tanata k’unk’uni tana turo baki gaba,Sudaida tana shiga d’akin-girki Bilkisu tasa dogon hijab d’inta har yana jan k’asa,wai haka sabuwar malamarsu ta Alfurqan take sawa,shine tace lallai itama haka zata dinga sawa Julaibib kuwa yad’inka musu ita da Walida kala-kala,tayi sand’a tafice da sauri.

Hajiya tana ganinta tace kai wannan yarinya da gaggawa kike hannun hagu a romo”sarauniya me d’ansarai ai ban ce zan rik’e miki uba ba.Julaibib yayi yar dariya ya tuno da Sudaida itace me fad’a mata haka musamman idan tana jin haushin su.Bata kula Hajiya ba tarungumeshi tawani shagwa6e”Baba tun d’azu kazo kayi zamanka anan.Yashafa kanta “Esbeeer Megadona yanzu zamu tafi.

Takalleshi cikin farin ciki”Baba yau Mama ta barni ni na had’a maka lemun karas,kashu da citta”kaji d’and’anon kuwa?Yagirgiza kai.Wallahi sooo luciousss…yadda tayi furucin yabasu dariya. Shima yace”thank you sooo very much my dear Bilkisu. Yarik’o hannunta suka mik’e”Hajiya barinje in sha lemun nan tunda sanyin shi. Bilkisu tad’an zaro idanu tana kallan Hajiya”ALLAH na mantane amma yanzu zan kawo miki naki dama Mama bata san nafito ba.Hajiya tace”tafi can sai yanzu kika tuna dani to bana sha.Tabi Julaibib da sauri da yasa takalmanshi yafara tafiya”ALLAH kuwan sai kin sha idan ba haka ba nima bazan kuma shan dabgenkiba.

Da daddare Julaibib yatafi kai Bilkisu da Walida hutun k’arshen mako gidan Inna,Sudaida tana shan rake taji tauuu…tauuu…tauuu…!K’arar harbin bindiga har tana hango kyallinshi ta tagar da take bud’e,raken hannunta ya su6uce, tarintse idanunta cikin matsanancin tsoro duk da abin ya zame musu jiki to amma na yanzu ya firgitata wallahi, tana Istirja’i yashigo da sallama yazauna yana kallanta”lafiya kuwa?Tad’ago tana kallan shi cikin mad’aukakin mamaki”kai bakaji harbin bindigar da akayi yanzu a jere har sau uku ba?

Yaya d’ansarai anya garin nan za a samu kwanciyar hankali a cikin shi? Yamaida kai da bayanshi jikin kujerar yana murmushi”matsoraciya kawai…Ta tsare shi da idanu. Yad’an kalleta” ke ba kome fa na…Ta girgiza kai”ba kome fa kace?Haka shekaran jiya danaje gida muna magana da Baba shima yace wai ba kome,to ni abinda bangane ba,a ba kome d’in me yakawo wannan harbe-harben ba dare ba rana?Anya ba koyan harbin suke yi ba? Baza kusa yan lek’en asiri su binciko muku me ake ciki ba Yaya Julaibib? Yaciro wata takadda daga aljihun gaban rigarshi da biro yafara lissafe-lissafenshi a ciki”to me kika ga anyi?Koma me sukeyi bata shafe muba…tayi shiru tana kallan shi aranta tanata maimaita Kalmar”kome sukeyi bata shafe muba… Yagama ya bud’e Laptop d’inshi yayi yan rubuce-rubuce a ciki ya rufe sannan ya kalleta”gobe Insha-ALLAH zani Kaduna mun tura kud’in kayayyaki amma har yanzu shiru tun wancan makon muke waya da manager na wajen amma sai wani hanya-hanya yake mana toh zani inga koma meye ganin idanuna.

Takalleshi wani iri ranta ba dad’i”nifa tafiye-tafiyen nan naka ya fara shigar min hanci da k’udundune wallahi,yana hanani rawar gaban hantsi, jiya fa yakamata kazo garin nan baka zo ba,na kauda kai banyi magana ba,yau kazo sai kuma gobe kace Kaduna za ka tafi washe gari da sassafe ka koma Gidan-Waya?A k’arshen makon ma baka hutaba?Ni gaskiya ban yadda ba shi Yaya Musaddiq d’in yatafi mana.Yayi yar dariya”Zaujatiii…uwar gidata anan duniya har a aljannah;ai ko Musaddiq yaci ya huta ko da yaushe shi yake tafiya,rabona da inje Kaduna saro kaya na kusa shekara fa,ko wannan karon bashi yace inje ba nine naga dacewar hakan shima yad’an huta…Kyan rawa da makar6i,amma kisha kurumunki Sudaidan d’ansarai ai na kusa ajiye koyarwar da nakeyi in dawo kan wannan makarantar gaba d’aya, kinga tafi-tafiye ya k’are sai mu manne kamar k’arfe da mayen k’arfe kullum muna tare mutu ka raba takalmin kaza ko?Yad’age gira yana mata wani kallon k’auna.Tayi shiru ta kyaleshi,dan wannan tafiyar da zaiyi ta 6ata mata rai sosai wallahi.

Shi kuma yacigaba da maganar shi duk da bata kulashiba,ai ya san tanaji tunda ba kurma bace,ranar litini d’inma bazan bar garin nan ba har sai munje an sake miki scanning ni wannan girman cikin yana bani mamaki a watanni biyar kacal.Hummm kawai tace tazame ta takwanta dakyar.

Da safe suna karyawa yazuba mata idanu yana zancen zuci ganin ta tsame hannunta a abincin wai ta k’oshi kuma ba wani cin kirki tayiba “wannan cikin gaba d’aya ya canja mishi Sudaida,ga yawan laulayi,ga rashin samun ishashshen bacci saboda munanan mafarkai,ga wasu k’ananan k’uraje da suka fito mata a duka la66anta ba irin magungunan da bata shaba dan su warke amma abin yaci tura,tayi sanyi sosai.A hankali tajingina bayan ta da jikin kujera tana yamutsa fuska”wash ALLAH!… Zaujiii…bakaji bayana ba kamar zai 6alle.Yafara mata tausa “sannu Sudaida. Tad’an kalleshi kawai.

Aminu yashigo da sallama shima yakalleta cikin tausayi”Sudaida ko asibiti zamu tafi ne? Tad’an yi luuu…da idanunta kamar zata rufe sai kuma takalleshi”Yaya Aminu sai gobe za muje.To ALLAH yaraba lafiya,yamik’a ma Julaibib hannu sukayi musafaha sannan yazauna suka gaisa da Sudaida. Suna hirarsu da Julaibib amma suna sakota,wani abun tayi magana wani kuma ta musu shiru. Aminu yamik’a mishi katin za6enshi(voters card)ni dai wannan karan bazan yi za6e ba,tunda ko ka za6a wanda kakeso to a k’arshen wanda su suke so shine sai lashe za6en da kuri’a mafi rinjaye,magud’i kiri da muzu haka ake yinshi.Bai wani dad’e ba yamusu sallama yatafi.Shima Julaibib yayi shirin tafiya Kaduna.

Yazauna a hannun kujerar da take kwance suna kallan juna na wucewar wasu dak’ik’u, tarik’e hannunshi”ban so tafiyar nan ba har ga ALLAH, ina ji ajikina kamar ba zamu sake had’uwa ba, idanunta suka kawo ruwa.Haba Zaujatiii…me yasa kike wannan furucin? Insha-ALLAH kafin magriba ai na dawo,sharrr…hawayen suka zubo mata,yafara goge mata”kiyi hak’uri Sudaida kome ya kusa zuwa k’arshe,kullum muna tare har sai kin gaji da ganina,yazame hannushi daga cikin nata,yamik’e yana gyara kwalar farar rigarshi”zo muje kawai kiyi zamanki a gidan Inna ko gidan Kawu idan na dawo sai in tsaya in d’auke ki.Uh uh ba kome idan naji bazan iya zaman ba to sai in tafi,tawani marairaice”

Tafiyar za kayi Yaya d’ansarai? Eh Sudaida ina 6ata lokaci gwamma inyi maza in tafi tunda ba kwana zanyi ba.Yasunkuya yabata sumba,tashafa k’asumbarshi sukama juna adabo.Har yakai k’ofa takirashi”Yaya d’ansarai…yatsaya cak sannu yajuyo “na’am Zaujatiii…suka sake zubama juna idanu na wucewar wasu dak’ik’u,tasauke gwauran numfashi a sanyaye tagyad’a kai “shikenan adawo lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button