GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

A gidan Inna ma Bilkisu kuka tasa mishi ita bazai tafiba,ta had’a kai da bango tana sheshshek’a,dakyar shi da Inna suka dinga lalla6ata sannan tayi shiru ita da Walida suka rakoshi k’ofar gida tana k’ananan hawaye,yashiga mota ya zauna yana d’aura belt tarufo mishi motar”Baba ALLAH yatsare a dawo lafiya…Walida ta koma Gidan-Waya da gudu ita bata wani damu sosai ba.Tad’aga hannu tana mishi adabo,yaja motar yatafi,zai sha kwana ya leko tana tsaye, tad’aga murya”Baba Qad uhibbbuka… Shima yamata adabo sannan yasha kwana yana murmushi furucinta”My dear Bilkisu kenan nima ina k’aunarki.

Tafiya yake yi amma yanaji kamar yajuya wajen Iyalinshi,ranshi ba dad’i har yashiga Kaduna garin gwamna,kiran Sudaida yashigo yad’aga da karsash”Zaujatiii…gani a garin gwamna.Nayi tunanin dama yanzu ka shiga.To ya jikin? Ya tambayeta cikin kulawa.Da sauk’i yanzu bana jin wani ciwo sai dai na yau da gobe kawai irin na mace me juna biyu,yanzu ma na idar da sallah walha,na kuma maka addu’a ALLAH yatsare min kai a duk in da za ka shiga,nima na rok’i ALLAH yarabani da cikin nan lafiya,yabani nak’uda sassauk’a,sannan nace barin kira d’ansarai mijin Sudaida inji muryarshi da kalamanshi su k’aramin nishad’i.

Oh ya rahmanu rahim…nagode ma Ubangiji da yabani ke a matsayin mata,ke macen albarkace,kece uwargidata har a aljanah,yasake yin k’asa da murya yana fad’a mata wasu kalamai wanda sirrin sune,tako kyalkyale da dariya”kai Ustazu…? Shima dariyar yake yi”na rantse miki da girman ALLAH Zaujatiii…Ko baka rantse ba na yadda da kai,ba abinda yake fitowa daga bakin ka game da soyayyarmu sai gaskiya”ALLAH yamaka albarka Abu Bilqisss…sai ka dawo d’in.Ya amsa da to sannan sukayi sallama ya zubama tashi wayar daya cire a kunne idanu,yayi lallausan murmushi yana shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi”Ummu Bilqisss…ya fesar da iska ta baki ta hanci,sannan yasa wayar a aljihu.

Duk yadda yaso ya koma gida a ranar hakanshi bata tadda ruwa ba, sai dai sun gama kome da Manager,ashe daga can Lagos aka samu matsala amma kome ya dai-daita.Washe gari kuma wayewar gari litini yana shirin barin garin gwamma gari yarikice anata k’one-k’onen tayoyi da kisan rayuka na babu dalili,cikin damuwa Sudaida takirashi”ka riga ka taso ne?A ah.Sukayi shiru na wucewar wasu dak’ik’u”to ALLAH ya sauwak’e wai meye musabbabin wannan fad’an?Sudaida ai kin san idan guguwar siyasa tafara kad’awa sai dai Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”

Tagyad’a kai”hakane,muma nan d’in sai a hankali,wallahi mutane dayawa suna ta kwashe muhimman abubuwansu suna tafiya wai sai angama za6e kome ya dai-daita sannan zasu dawo,Abu me aikin Inna ma yanzu tazo tamin sallama zata tafi k’auyansu, hankalin jama’a da dama yak’i kwanciya tunda sukaji Kaduna ba lafiya,yanzu mu kuma sai yadda hali tayi kenan?Ta tambayeshi.Eh Sudaida amma nan in da nake ba a kome sai dai ansa matakan tsarone ba shiga ba fita, amma Manager yayi waya da babban d’an shi sojane yanzu zai zo yafitar dani tunda dama rigimar a cikin garine.Ta amsa a sanyaye”to ALLAH yasa.

Tana zaune cikin tsananin tsoro da damuwa na rashin mafita Aminu yashigo”ke Sudaida ki d’auki abinda zaki iya d’auka me mahimmanci yanzu zamu bar garin barinje in dawo…ta tari numfashinshi “har dasu Baba?Yakoma ya zauna tun safe nake magiya da rok’onsu su shirya mubar garin”gudun hijira wajibi ne idan kaga ba dama ka tsere…inji Garba Super,sunk’i toh ni dai gaskiyar magana tafiya zanyi dan wuya ko da magani ba dad’i, sunce basu hana duk me tafiya tafiya ba su dai sunanan,barinje ATM ki zama cikin shiri kafin in dawo. A sanyaye ta gyad’a kai sannan tasake kiran Julaibib sai dai tak’i shiga tabi d’akin-shak’atawar da kallo”to me zata d’auka?

To suma da suka ankare mutanan garin suna tafiya sai suka tare hanyoyi ba shiga ba fita dan suna da wani k’uduri a zukatansu amma a zahirance fad’i suke ba kome ba kome,dole Aminu ya hak’ura.Bayan sallar la’asar wata motar roka shak’e da abinci da mutane hanya tabiyo dasu ta garin suma da gani ba tambaya yan gudun hijirane ko da wani gari suka fito? ALLAH masani.

Direban a rikice yake sunata tsayar dashi amma yak’i tsaya”wanda maciji ya sare shi idan yaga tsumma sai gudu…Kawai yayi k’undunbala zai bi takansu sai suka tarwatse daga tsakiyar titin ya wuce cikin tashin hankali suka rufa mishi baya, saboda rikicewa sai sitiyarin yakwace mishi,take ta daki sabon masallacin mak’era da ake kan aikin ginawa, kowa yayi ta kanshi dan sun kusa cin musu,suka fantsama cikin gari gidajen mutane a kid’ime,su kuma ganin wannan ya dad’a tayar ma da mutane hankali musamman mata.Sudaida tashiga d’akin-girki ta sauke abincin data d’aura dan bata da kwanciyar hankalin da zata iya k’arasawa dama tun karin safe bata kuma sa kome a bakin taba.

Takira Julaibib amma yana ganin kiran yak’i d’agawa a k’arshema yasa wayar a yanayin shiru (silent)saboda d’azu ta sake kiranshi akan kar yadawo, yabari ko zuwa gobe ne dan suma garin ya fara rikicewa, sai yace mata bazai iya ba yau d’in zai dawo yana ma hanya ta kwantar da hankalinta ba kome fa,kuma ta dafata mishi shayi,tayi abinci me kyau yana azumi kome dare bazai yi bud’a baki da kome ba bayan dabino sai abincinta ko da bai shigo kafin magriba ba,bai jira amsawar taba yakatse kiran ya kira Musaddiq yana tambayar shi”wai meke faruwane Sudaida ta dameni kar in dawo?

Yayi tsaki”kai rabu da ita,da da wata babbar matsala ai dana fad’a maka,sun d’anyi zage-zagen sune d’azu ko dak’ik’u talatin ba suyiba suka koma k’auyukan su,in dai wannan hatsaniyar ne yau suka fara?Ka san halin mata basa raina abin tsoro,watama cinnaka za kaga tanama ihu da kururuwa a zo a kashe mata kar ya cijeta.Uh uh Musaddiq sharri dai ba kyau…to suwaye suke ta guduwa?Julaibib yasake tambayarshi.Masu guduwa dama yan ciranine amma ni dai a ganin idanuna banga wani zaunanna gari daya tafi ko mutum d’ayaba.To ALLAH yakyauta.Musaddiq ya amsa”Amin d’ansarai ka iso lafiya.Da wannan dalilin yasa yak’i sake d’aga wayarta.

Sai da yashigo cikin gari sannan ya d’auki wayarshi zai tsokani Sudaida,sai dai missed call d’ari da yagani yasa zuciyarshi bugawa da k’arfin gaske kira daga kowa na zuri’arsu lambar Inna yafara kira amma tak’i shiga,fargaba ta kamashi lallai ba lafiya…

A bakin hanya kuma sunyi kaca-kaca da kayan dake cikin rokan sannan suka banka mata wuta.Me neman kuka ne aka jefe shi da kashin a waki,wai saboda yak’i tsayawa suka fara k’ona shagunan bakin hanya…ALLAH Sarki shagon Ashiru Chindo suka fara k’onawa…Mtswww bahaushe me ban haushi na tanko me kan bashi…wai sai a wannan lokacin suka san eh lallai wad’annan mutanan da gaske sukeyi,suka fara neman mafita a sanda lokaci yariga yak’ure musu, dan ba a fafe gora ranar tafiya…kumamar tsanyar da wuri take tila…Dana sani mara amfani…suka cigaba da k’ona tayoyi suna watsa borkonon tsohuwa(tear gas)wallahi abu kamar wasa k’aramar magana ta zama babba,garin yayi bak’ink’irin ga har6e-har6en bindigogi ta ko ina.

Yana cikin wannan hali kiran Sudaida yashigo yad’aga da sauri,cikin rawar jiki data murya tafara magana”Yaya d’an Sarai na rok’eka da girman ALLAH karka k’araso garin nan…me yafaru ne?Yak’i a keyi ka koma dan wallahi sun fara kashe mazaje suna k’ona gidajeee…tak’arasa maganar cikin sarewa saboda harbin bindiga shima yaji hakan jin kunnuwan shi.Kina ji? Ta amsa da eh ina…in…inaji…yana d’ago kai yaga gungunsu sun mishi k’awanya…zufa tasake karyo mishi Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un yafad’a,a wayar kuma yana jiyo hayaniya da surutai barkatai… Wasu suna ihu wasu suna kabbara,anan kuma suna jiran fitowar shi”gaba kura baya siyaki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button