GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Sudaida tafi gidan Inna Insha-ALLAH zan zo in sameku a can yayi jarumtar fad’a mata haka. Tarintse idanunta saboda a zaba wai…wash…uhhh… Bazan iya tafiya ba wallahi!Wai…ALLAH na!Tafara nishin azaba Zaujiii…nak’uda nake yi haihuwa zan yi…wai…Wayyo!Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un dan ALLAH ka yafe min Yaya Julaibib mutuwa zan yi!A ah Sudaida ba nak’uda bane cikin naki fa watanni biyar ne…wallahi shine bakaji marataba!Tayarfe hannu. Yasake d’ago kai yakalleshi basu k’araso in da yake ba dan sun san ba ta in da zai gudu,yaga abinda bai gani ba d’azu bindigogi AK47,pistol, shar6a-shar6an wuk’ak’e gayama jini na wuce,adduna,tayoyi da jarka wanda ya tabbatar fetur ne a ciki,ga nishin da Sudaida takeyi cikin tsananin ciwon daya had’u da tashin hankali,sai yaji wasu zafafan hawaye sharrr… Sun zubo mishi”yanaji yana gani amma ba shi da damar da zaije ya taimaketa…

Sudaida kiyi hak’uri kiyi addu’a ALLAH yana tare dake,bata amsaba nishin azaba kawai take yi tana kiran sunayen ALLAH wai…ALLAH ka taima… Bata k’arasa wasu suka shigo gidan.Wayyo! Yaya d’ansarai ga sunan…wani yad’auki wayar dama a k’asa take ta bud’e maganar”me d’ansarai ya isa ya hanamu yi?Zuciyar Julaibib tafara lugude…malam karka ta6a min mata yafad’a cikin k’araji.Yakyalkyale da dariya “matsoracin banza matsoracin wofi kaje ka 6uya kana magana ta waya,to idan ka isa kazo gidan na ka muyi gaba da gaba mana,I swear a gabanka zan zamu mata yankan rago kai ma mu maka,wawa kawai”filthy bastard…

“Wallahi ALLAH ya fiku…yasake kyalkyalewa da wata irin dariya”eh ALLAH ya fimu mu kuma munfiku kaga dai mune zamuci gari,kabimu a hankali dan zakara a rataye baya caara.Bazan biku ba wallahi.Yajijjiga kai”that’s very good,mun shigo gidan ka dan muyi bincike ance kuma kunada bindigogi to amma tunda kace bazaka bimuba za muyi maganin taurin kanka, kuma duk inda ka6uya a fad’in garin nan sai an binciko ka an kawo min kai gabana na maka yankan rago kamar yadda muka fara yima sauran tsinannun yan’uwanka.

Yakalli Sudaida da take durk’ushe tana matagugu dafe da ciki,yayi murmushin mugunta”sai nayi abinda naga dama da wannan banziyar matar taka, ya kyalkyale da dariya.Kalamanshi suka soke Julaibib da Sudaida suk’ar wuk’a a k’ahon zuciya. Ambaton ALLAH takeyi a galabaice dan zuwa wannan lokacin k’arfinta ya riga ya k’are,d’an cikinta ya dunk’ule waje d’aya,wucewar wasu dak’ik’u kawai sai jini ya 6alle mata,tana kwance ko motsin kirki ba tayi,idanunta sun fara canja kala kad’an kad’an bak’in ciki yake 6acewa.

Yayi jimmm…yana kallanta,yayi d’as d’as d’as da yan yatsunshi sannan yagyad’a kai bayan ya kalli sauran da suma shi d’in suke kallo”tunda kin min buk’ulun abinda nayi niyya to kema baki da sauran amfani a doron duniya,yad’aga bindiga yana gyara kunamar jiki(trigger)zan fasa k’ok’on kan matarka d’ansarai…Julaibib yafara karaji karka kasheta dan girman ALLAH kabari in zo ni ka kasheni a madadinta… Yakyalkyale da dariya wannan daga bayane sadaka da karuwa…shege d’an iska ai kowa ya tuba dan wuya ba lada”may her gentle soul rest in hell…suka had’a baki wajen amsawa da”amennn…Dai dai da har6e kanta da yayi tauuu…tauuu…sai biyu jini yayi kaca-kaca a jikin bango rai yayi halinshi,suka zuba fetur sannan suka sake harba bindiga wuuuhhh…wuta ta tashi suka fita da gudu wayar ta katse.

Julaibib yashiga cikin tashin hankali,ya tabbatar sun kashe Sudaida.Yayi Istirja’i yana kiran sunanta,ihun kiran sunan yasa wad’anda suka mishi k’awanya suka bud’e motar suna mazurai suka jawoshi “da uban wa kake magana tun d’azu a waya? Ko kana fad’ama sauran yan’uwanku masu sallah su kawo muku taimakone?To su zo d’in ba abinda zasu iya mana dan munfi k’arfinku har abadan duniya, yabisu da kallo duk fentin da sukama fuskokin su bai hanashi gane suba, wasu mak’otan shine,wasu ma akwai kud’ad’en da suke binsu bashi,bazato yaji an buga mishi bakin bindiga”you’re very stupid ka tsaremu da idanu ba tambayarka muke yiba?Yarintse idanunshi dan yaji bugun har k’wak’walwarshi,bai gama dawowa dai-dai ba suka rufeshi da duka, naushi da mangari baji ba gani.

Wasu tarin matasan hausawa suka hango sun samu mafaka,abinda yasa suka bar dukan Julaibib kenan suka rufarma wad’ancan.Julaibib yamik’a hannu yajawo wayarshi data fad’i yasa a aljihu,dakyar yashiga motar yatashe ta yana gani dishi-dishi saboda jinin da yake zuba dan sun farfasa mishi jiki bana wasa ba,yana zuwa k’ofar gidansu yaci burki wani abu mara dad’i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarshi”ina Innarshi? Baba?Walida da Bilkisun shi!?Zuciyarshi tana bugawa da k’arfin gaske saboda ganin gidan ya gama k’onewa har ya rufta,ya tabbatar koma menene a gidan ya k’one bashi da sauran amfani a doron duniya.

Yafito daga motar yana jiri yana bin bango har yak’arasa gidanshi,yana cikin tafiyar ya yanke jiki yafad’i,awanni nawa yayi a kwance a wajen bai sani ba,ya farkane yaji mutane nabi takanshi cikin neman ceton rai, yarik’o k’afar wani”dan ALLAH taimakeni in tashi,yafizge k’afarshi”wannan rana ce ta kowa yayi ta kanshi,kalleni da kyau harsasai guda takwas ne a cinyoyina amma ina tafiya sai kai kana kwance babu alamar rauni me tsanani a tare da kai?Yayi gaba dan ALLAH kayita kwanciya har su zo su same ka a wajen…ai bai san da gaske zai iya tashiba sai da yaji hucin wutar da suka banka ya ta6i jikinshi.

Dakyar da sid’in goshi yak’arasa gidanshi nanma ya gama ci da wuta,wani wajen kuma da sauran hayak’i,yana shiga d’akin-shak’atawar yaji kamar an sa adda an sare mishi k’afafu saboda tashin hankalin abinda idanun shi suka gani. Wayyooo…!!! Sudaida ce ta k’one k’urmus,maik’on jikinta male-male a wajen kamar anyi 6arin mangyad’a,tabbasss da a waje yaga k’onannan gawar nan to ba zai gane Zaujatiii…ce ba! Kuka yak’wace mishi jikinshi da zuciyarshi suka d’auki rawa”yanzu irin kisan gillan da akama sauran zuri’arsu kenan!?Da sauran yan’uwanshi al’ummar Manzon ALLAH? Yahad’iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da aka barbad’eshi da dakakken barkono d’an munci wayyo! Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!!!Lahaula wala quuwata illah billahil aliyul azim!!! Idanunshi suka kad’a jawur sai yaji kome yafice mishi a rai… Zafafan hawaye suna zubo mishi sharrr…! Sharrr…!

Kira yashigo wayar daya manta da al’amarinta yacirota a aljihu Musaddiq…yad’aga da sauri yana fad’in Musaddiq sun kashe Sudaida sun k’onata ina sauran Iyayan mune? Suna ina?Kaima kana inane?Musaddiq ya amsa cikin tashin hankali “saurara kaji abinda zan fad’a maka dan tun d’azu nake gwada kiranka bata shiga sai yanzu.Sun kashe su Baba a masallaci, gidajanmu, Iyayanmu, matanmu da Ya’yanmu sun banka musu wuta kafin sufito su gudu!Musaddiq yafara kuka sai dai mu bisu da addu’a kafin wa’adinmu yacika,d’ansarai sunci k’arfinmu, sunyi galaba…!D’ansarai bamu da abinda zamu kare kanmu dan nima haka nafito daga gida hannu rabbana…dakyar furucin nashi yake fita… Musaddiq me yasame kane?Saurareni kawai Julaibib meye ma bai sameniba!?Menene ban gani ba?Yak’ara fashewa da kuka”a gaban idanuna akama Adnan da Sagir yankan rago…!!!

Kaiii ALLAH yatsinema arna…Julaibib k’afafuna a karye suke ga sara ba adadi a jikina,ga harsashin da suka harbeni yana cikin cikina…dakyar yake furucin Julaibib yadad’a manna wayar a kunnanshi dan maganar tashi k’asa take dad’a yi,kaima sunata neman ka ruwa a jallo dan haka ni shawarar da zan baka idan kasamu ma6uya to wallahi ka6uya,tunda ba abinda zaka kare kanka dashi…yafara tari da nishi duk tarin da yayi jinine yake fita ta baki ta hanci,yafara numfarfashi sama-sama, numfashin yana san d’aukewa,yafara magana a fizge d’ansarai mu yafema juna…abinda duk yake tsakaninmu na kud’ad’e da sauran al’amuran rayuwa duk mu yafema junaaa…!Rayuwata…ta…k’are ina ji ajikina bazan kuma rayuwa a doron duniya ba!Cikina kamar ana huramin wutahhh…!!! Wai…washhh,Yayi nishi me k’arfi…jini yana zubowa tabaki ta hanci.. Ju…l…lai…bib…kumaaa…ina!Yayi iya yinshi furucin yak’i fitowa yana nishi cikin tsananin ciwo…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button