GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kaskon wuta me wuyar tallafa.
Na gaban wuta shi yake jin d’umunshi.

9 Rajab 1441
3 March 2020

We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim ( Ra’ibs)

Shafi na ashirin da biyar.

Cikin tsananin tashin hankali yake fad’in Musaddiq…Musaddiq kana inane!?Shiru ba amsa yacire wayar ya duba har yanzu a had’e suke,wucewar wasu dak’ik’u Julaibib yana cigaba da kiran sunan shi Musaddiq!Dakyar ya amsa.Kana inane? Musaddiq yamirgina kai cikin ciwo”bazaiyi amfanin kome ba,na san mutuwa zan yi tawa ta riga ta k’are,d’ansarai…kab… Ka6uya… K…kak… Kaw… Wai.Zuciyar Julaibib tasake tsinkewa yafara kuka”na rok’eka da girman ALLAH kafad’a min inda kake zan zo in taimake ka…kai kad’ai karage min d’an uwa na jini a doron duniya!Yacigaba da magiya har Musaddiq yabud’e baki dakyar yace”ina wajen masallaci.Wani masallacin? Wanne Musaddiq?

Yayi tambayar a gaggauce jin wayar shi tayi k’ara alamar caji saura kad’an yak’are… Musaddiq ya kasa magana sai nishin azaba yakeyi… Wanne daga cikin masallacin Muss…kafin yak’arasa fad’in sunan difff wayar takashe kanta.Yafurzar da wani huci yana kallan k’onannun k’asusuwan Sudaida sai yaji kukan cakkk…Ya tsaya,yamik’e tsaye yana mata addu’ar dacewa da rahamar Ubangiji”Zaujatiii…ya fad’i sunan yana jijjiga kai”sai ALLAH yahad’a mu a lahira… Uwargidata ta duniya da lahirahh!…

Koma wani masallaci ne Insha-ALLAH sai ya gano Musaddiq ya bashi taimakon gaggawa iyakar iyawarshi,zuciyarshi tabushe,wallahil-azim shima sai yayi kisa sai dai idan bai had’u da arne ba;koda zasu kashe shi,yana fita kuwa yaga k’aramar bindiga an kashe wani arne ta fad’i a hannunshi, yad’auka ya lalube aljihunshi yakwashe sauran harsashin yaloda a ciki sannan yafara tafiya cikin sand’a yana bin bango,daga nesa yahango gungunsu sun dumfaro inda yake,a hankali yazame yakwanta a cikin gawarwaki kamar shima mataccen ne.

Suka zo suka wuce suna surutai da yaren Bajju,a d’an abinda yake tsitssinta daga yaren ya fahimci harsashin sune yak’are zasu koma gida su k’ara sabon lodi,dan haka yad’aga bindiga yasaita su daga kwancen ALLAH ya taimakeshi ya harbe guda uku nan take suka zube a k’asa matattu,sauran suka fara gudun ceton rai suna zage-zage a cikin gawarwakin nan akwai wanda bai mutu ba, amma dan abu kazan uban mutum yabari muje muk’ara shiryawa wallahi zai gane da gero ake koko…Julaibib yasake harba bindiga yasamu wani a kai shima ya fad’i yana ihu da kururuwa,sai da yak’ara mishi harsashi biyu sannan ya tashi yabar wajen kafin su dawo,zuciyarshi tana tafarfasa da kalaman wanda ya harbe Sudaida”zan fasa k’ok’on kan matarka…bata sauran amfani a doron duniya”may her gentle soul rest in hell… Julaibib a gaban idanuna sukama Adnan da Sagir yankan rago…ank’ona su Inna a gidajansu… Sun kashe su Baba a masallaci…kalaman da suka dinga mishi amsa kuuwa a k’wak’walwarshi kenan.Sai yaji wani k’arfi yasake zuwa mishi.

Yana cikin tafiya yaci karo da gawar Abdul d’in Yaya Karima an daddatsashi abun ba kyan gani,bai tsaya ba dan tsayuwar bata da amfani tunda ya riga ya mutu,su da arnan kuma kowa k’ok’arin kashe kowa yakeyi haka yakeya cin karo da gawarwaki kisan wulak’anci!Julaibib yayi yawon bin masallatai amma baiga Musaddiq ba,a wajen masallacin Malam Murtala yaga wasu mutane guda biyu an sa musu taya sun k’one k’urmusss…ba ta yadda za ayi ka gane ko suwaye wallahi,yaciga da tafiya zuciyarshi na tafarfasa daga baya yaji an harbe shi a kafad’a ashe wasu daga cikin su sun hangoshi… Yajuya yana harbinsu shima har sai da harsashi yak’are,yatura bindigar a aljihu yakwanta yana a k’asa cikin mawuyacin hali jini yana zuba.

A wannan rana ta litini kwana akayi ana gumurzu tsakanin musulmai da arna,duk da musulmai masu kayan aiki k’alilan ne amma sunyi k’ok’ari da k’arfin zuciya suma sun kashe arna ba wanda yayi galaba akan wani,kare jini biri jini akayi”ragasss mutuwar kasko.Toh wayewar gari ranar talata kenan kowa ya galabaita ba sauran k’arfi ba kayan aiki,ba abinda mutum zai sa a bakin salati,irinsu Julaibib masu azumi ranar litini babu kome a cikinsu sai abinda sukayi sahur a daren lahadi, ga raunuka a jikin mutane da yake buk’atar taimakon gaggawa amma kayan agajin(first aidbox) tun dare yak’are.Su kuma wad’ancan anata dafa musu abinci da kayan sha na k’arin k’arfi suna zuwa suna cika cikinsu, bayan haka kuma wad’anda akayi gumurzun dare dasu, sai suka dinga komawa gida, wasu matasan na daban suna shiga cikin gari da sababbin kayan aiki.

(Tabbasss ni ‘yar Ibrahim Asdilat KD…ganauce, ALLAH yasa inga Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wa’ahlihi wasallam…yadda naga wannan al’amari ganin idanuna)

Kuma a wannan safiyar ta talata jirgin k’asa yashigo garin musulmai suka fara hamdala ga Ubangiji cewa an kawo musu d’auki…Tabbasss d’auki a kawo ta hanyar k’arama barno dawaki dan k’ungiyarsu (CAN) ce takawo musu k’arin makamai,to a wannan lokacin ne sukama musulmai ainihin kisan k’are dangi, suka tarwatse kome da kowa na garin…musulmai sai kabbara da addu’o’i sukeyi a duwatsu suna harbinsu… Amma ko gezau basuyi ba…sarkin yawa ai yafi sarkin k’arfi…Zakara a rataye baya caara;wasu na shiga gidaje sai sunma gida k’ark’af da kayan ciki sannan su banka mishi wuta,haka shaguna da koma inane, shagunan bakin hanya kuma sun kwakkwashe kome amma basu k’ona suba saboda wai anan zasu fara sana’o’insu.

A wannan mawuyacin halin sukayi a rangama da Julaibib yayi matuk’ar galabaita yana numfarfashi,wata Juli ce tanuna shi”yauwa ga shegen da muke ta nema tun jiya,yabisu da kallo idanunshi sun kad’a jawur,dan tsabar rainin wayo da samun waje “kuturu da gad’a a rama.Wai har da mata suna rik’e da wuk’ak’e gayama jini na wuce,wanda za su iya harbi da k’ananan bindigogi sun rik’e,wasu da kokara da gorori, Kauuu…bazato yaji an buga mishi kokara akai”dan abu kazan ubanka you’ve no respect muna tsaye kaima kana tsaye?

Kaci sa a ba bindiga a hannuna dana fasa k’ok’on kanka,Juli tamik’a mishi na hannunta”ga wannan”yature hannunta”rabu dashi ba yanzu zamu kasheshi ba sai yaci naman ubanshi me dogon gemunnan gashashshe; Now just kneel down,rise up your hands and close your eyes”haka yakai gwiwoyinshi k’asa yayi yadda yace.Wani da yayi tatil da uwar laifi yafara tambayarshi da yanayinsu irin ta mashaya”kai ne d’ansarai Lecturer a Gidan-Waya da nace kasamo ma yata gurbin karatu kace bata da credits d’in da za a d’auketa ko?

Yayi kamar baiji abinda yafad’a ba.Sai yabuga mishi gora a kafad’a”childish monger I’m I not talking to you?Zuciyarshi tak’ara bushewa wallahi shak’a d’aya zai wannan ragowar ruwan burkutun numfashinshi yad’auke har abadan duniya a doron k’asa,sai kawai yamik’e tsaye yana kallanshi cikin idanu”Yes Indeed,I’m d’an Sarai Lecturer in Kaduna State College of Education Gidan-Waya.Wani yazo gabanshi”how dare you baka da kome amma zaka nuna mana zafin kai?Ka san harda wancan tsinanniyar makarantar taka daka bud’e yasa mukayi yak’innan?Dan na san halinka sai kasa wasu daga cikinmu sun zama irinku masu sallah,dama yara nawa kasa suka zama irinku?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button