GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

To suma duk mun kashe shegu saura kai…bai gama rufe baki ba Julaibib yayi kukan kura ya cafki mak’ogwaranshi,idanunshi suka firfito yafara kakari dakyar suka 6am6areshi,yafad’i gefe yana tari da maida numfashi,sai kuma ya mik’e ya dunfaro shi, yana nunashi da yatsa”yau ka gama kad’ewa har ganyanka wallahi.Julaibib da zuciyarshi tariga ta bushe baiyi wata-wata ba yakai mishi wani irin naushi da k’arfin bala’i a muk’amuk’i ahhh…yayi ihu ya tsuguna kame da wajen dan yaji naushin yadda yakamata,yana zubar da jinin bakinshi sai ga hak’ori biyu a k’asa yasake fasa ihun takaici kaciremin hak’ora?

Julaibib yajijjiga kai zai sake kai mishi wani naushin yaji an bank’areshi ta baya…yayi iya k’ok’arinshi yakwace amma ya kasa dan rik’on kura taga nama suka mishi tamauuu…Idanunshi suka k’ara kad’awa jawur gangar jiki da zuciyarshi mazari sukeyi,wata jijiya ta fito rad’am a gefen goshinshi kamar shatin bulala saboda rik’on da suka mishi me bala’in azaba.

Wanda aka fasama bakin ya goge jinin sannan yamik’e tsaye suna kallan kallo da Julaibib zuciyoyinsu na tafarfasa,har ya kar6i bindigar ya saita kirjinshi dai-dai satin zuciya sai kuma yayi wurgi da ita kaiii…yafad’a cikin k’araji”idan na kasheka one time naji haushin kaina wallahi…yakallesu kuci buhun abu kazan ubanshi yadda zaku iya,yatattaro miyan bakinshi me had’e da jini da kakin majinan da yayi yatofama Julaibib a fuska”filthy bastard.Yatasa matan agaba sukayi tafiyarsu. Aka fara ba Julaibib na jaki ba ji ba gani suna jaddada mishi”ai ko ba makami da hannuma zamu iya kasheka har lahira.

Wayyooo…ALLAH!!!!Julaibib ya daku iya dakuwa sun mishi walmukalifatu da jiki!Har ya daina numfashi,suka dinga janshi har zuwa inda wasu tarin gawarwaki suke suka jefashi,anjima zamu gasaku gashin kan saniya ba irin gashin tsire ba,suma suka juya sunata haki da numfarfashi…

Wani sanyine yafara ratsa har 6argonshi kamar wanda a ka ajiyeshi a sararin dusar k’ank’ara ba kaya ajikinshi,ko ina nashi na karkarwa har ya’yan hanji,abinda ya dawo dashi cikin hayyacinshi kenan, dakyar da sid’in goshi ya bud’e idonshi guda d’aya,dan d’ayan ya kumbura suntum fatar idon tayi bak’ink’irin alamar duka da kwanciyar gurbataccen jini,wajen wani irin wari,k’arnin jini da hamami ciwukan dake cikin gawarwakin yakeyi, k’udaje kuma sukace ga sunan yau take sallah a wajen su.Abubuwan da suka faru kafin ya suma suka dawo mishi tiryan-tiryan,wasu zafafan hawaye suka fara zuba daga idonshi me lafiya sharrr… Sharrr…

Yafara Istigfari wucewar wasu dak’ik’u kuma ya mirgina kai cikin ciwo”ALLAH kaine mahaliccina! ALLAH ka fini sanin halin k’uncin da nake ciki, kataimakeni.Yayi iyakar iyawarshi ya d’aga hannunshi ya kori mayatattun k’udajen da suka baibaye fuskarshi ga kuma hayaniyarsu amma abun yaci tura, k’afarshi d’aya a karye take hannayen shima haka,zuciyarshi tayi tsananin rauni yana buk’atar taimako, mak’ogwaranshi ya bushe k’amasss kamar ruwa bai ta6a wucewa ta wajen ba,miyau ma dakyar yake tsatstsafowa a bakinshi, yahad’iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da aka barbad’eshi da dakakken barkono d’an munci,kanshi yasara,yafara mishi wani matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu.A wannan tsananin ya hango gungunsu da jarka,suna zuwa suka bud’e fetur ne a ciki suka fara juyema gawarwakin har dashi sai da suka matsa daga wajen sannan suka harba bindinga tauuu… Nan take wuta ta kama wuuuhhh…suma suka juya sukayi tafiyarsu suna wata irin dariya ta rashin hankali da imani.

Wayyo wai ALLAH!Wato idan kaji k’i gudu to Alqur’an sa gudune bai zo ba…shi dai Julaibib bai san ya akayi ba sai gashi ya mik’e…yana barin wajen wuta tabi takan sauran.Yana dafe da bango yana d’ingisa k’afa d’aya me lafiyar dakyar…wani irin jiri ya wulwulashi ya buga da k’asa yadunk’ule yana matagugu,numfashinshi fita ya keyi wani baya shiga, zuciyarshi na mishi suya tana bugawa da k’arfin gaske kamar zata fasa k’irjinshi ta fito!Wucewar wasu yan dak’ik’u sai gashi ya zube a k’asa wanwarrr cikin d’aukewar numfashi difff!

Bayan da k’urar ta lafa manya-manyan matasan arnan da akayi yak’in dasu irinsu Nuhun gidan Diryan,Julius,Shekari da sauransu da sauran su,sune suka dinga tasa k’eyar mata da k’ananan yara zuwa Police Station d’in garin suna musu zagin tsame nama da mugun alkaba’i,su kuma suna biye dasu wasu na kukan zuci,wasu na nasarari,wasu ba uh ba uh uh,haka suke tsallake gawarwaki abun ba kyan gani,kaga gawa ta kumbura ta fashe kayan ciki a waje,awani wajen kuma sun saki aladunsu suna danasha da gawarwakin…Kai ALLAH ka k’ara tsinema arna!Dan wata shari’ar billahil-azim sai a lahira!.

Zuwan sojoji da jiniyarsu (siren)da wasu masu kud’in suka hayo kuji fa?Daga wasu garuruwan dan su fitar da yan’uwansu tunda har lokacin basu bud’e hanya ba,haka ake ta zama a Police Station cikin mawuyacin hali,amma wasu daga cikin arnan suna ta kawoma yan uwansu masu sallah abinci da sauran kayan buk’ata.Yayin da wasu bak’in ciki kamar ya kashe su da suka ga maza da yawa na daga musulmai sun fito da ransu da lafiyarsu,sunata mamaki da takaici, to su wad’annan a ina suka 6oya ne a cikin garin da har basu gan suba? Sun manta cewa”zakaran da ALLAH ya nufa da caara toh fa ko ana muzuru ana shaho wallahi sai ya yi.

(Alhaji Umar Millionaire Doka,Wallahil-azim baza mu manta k’ok’arin da kayi na fara turo da sojoji Zonkwa ba har abadan duniya,Ubangiji yasaka maka da mafificin sakamakon shi,yasanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanka)

Wannan jiniyar tasa duk wani wanda ALLAH yasa yana da sauran numfashi a doron duniya na daga maza musulmai daya 6uya yafito,nan da nan suka fara d’aukar wad’anda suke kwance cikin mawuyacin hali zuwa asibitocin garin dan a basu taimak’on gaggawa, masu gudun hijira suka fara d’aukar hanya,wasu daga su sai kayan jikinsu dan an k’one kome nasu,wasu kuma ba a k’one ba,masu sauran yan uwa a wasu garuruwan suka shiga kiransu su taimako da mota azo a d’auke su an bud’e hanya…kai rayuwa bata da tabbasss! Idan ka san farkon ka,toh baka san k’arshenka,Ubangiji kamana gamdakatar da kyakkyawan k’arshe????abinda aka tara shekara da shekaru rana d’aya da wuni d’aya an tarwatsashi har abadan duniya sai dai a fara sabon nema daga farko!.

Julaibib yana cikin wad’anda aka kwasa magashiyan zuwa asibitin”Zonkwa Medical Center” Suna kwance a k’asa a d’akin da ake zama kafin aga likita (reception)sai dai tunda aka kawo su ba wanda yakallesu tsakanin likita da ma’aikatan jinya bare susa rai da wani taimakon gaggawa.Wata ma’aikaciyar jinya tashigo tana yarfa musu ruwan bala’i kamar su suka kawo kansu “gwamma ku bud’e kunnuwanku dakyau ku jini ba wanda zamu duba sai ya bamu kud’i,idan ba haka ba to sai dai ku dauwama a haka har ku k’arasa mutuwa,taja dogon tsaki” ku d’in nan kuna da taurin kan tsiya to amma hakan kuma ai yana dakyau tunda kunji a jikinku,sau nawa muna muku hannunka me sanda?Bama k’aunarku, bama k’aunar zamanku a garinmu kona sisin kwabo amma naci dambun kuturu kun kafe kai da fata,sai kuma tayi lallausan murmushi”ai gashi mun muku kattt…Kisan mummuk’e.

Tajuya tana cigaba da fad’an kalmomin wulak’anci da tozarci.Julaibib daya sake farfad’owa ya mirgina kai cikin tsananin ciwo da tausayin kai”banda rashin imani a ina mutum yake da wani kud’i a yadda yake d’innan da har zai basu sannan su dubashi!?Tsananin yayi tsanani a gareshi shi kad’ai yasan abinda yakeji a gangar jiki da zuciyarshi sai kuma wanda yashiga mawuyacin hali irin wanda yashiga,suna buk’atar taimako toh sai dai kuma baiga ta inda taimakon zai zoba…sai kuma yayi saurin fad’in.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button