GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

“ALLAH na tuba,k’udirarka tafi gaban tunanin duk me tunani! Ya Ubangajin sammai da k’assai!Ya Ubangijina na mik’a duk al’amurana gareka! Muryarshi tafara rawa alamar karyewar zuciya????ya Ubangijina bani da k’arfi bani da dabara sai abinda kazartai a kaina! Ubangiji ka iya mana! Yamaida idonshi me lafiyar ya rufe dan d’ayan kumburan daya dad’ayi yasa kanshi ya mishi wani irin nauyi kamar an d’ora mishi buhun duwatsu,a hankali yacigaba da maimaita addu’ar”Allahumma lasahla illah maaja’altahu sahlan wa’anta taj’alul hazna izaa shi’ita sahlan…

Wallahi abu kamar wasa k’aramar magana ta zama babba kwana biyu sunanan a haka kamar yadda wannan ma’aikaciyar jinyar tafad’a mutanan d’akin sai mutuwa suke yi…wari da k’udaje kam ba a magana.Doctor Bode Davis mamallakin asibitin da wasu matasa suka shigo d’akin yana nuna musu”kun gansu sune nake so a fita dasu daga waje muna so a gyara wajen…wani a cikin majinyatan yafara zaginsu”kai Bode ALLAH yak’ara tsine maka albarka,kuma in ALLAH ya yadda kaima sai sun maka abinda suka mana,ka sanni farin sani har family card nake dashi a asibitin nan amma yanzu kace bazaka dubani ka ciremin harsashin dake cinyoyi naba har sai na baka kud’i!

ALLAH yatsinema gamayyar da zaka nemi taimako a wajen wanda kuke gamayyar yak’i taimaka maka a sanda kake tsananin buk’atar haka, tirrr da irinka, wallahi nayi nadamar duk wata mu’amala data ta6a shiga tsakaninmu!Wani yakai mishi kutifo”how dare childish rat…Zai sake kai mishi kutifo Bode yace kyaleshi yaji da abinda yadameshi,in dai kanada kud’i to zamu cire maka,ko da ATM card d’inkane in dai yana aljihunka sai mu d’auka kafad’a mana pin-number mu ciro kud’in muzo mu cire maka.

Yana daga kwancen ya d’ud’d’ura musu zagi sannan yace”gwamma in mutu da in baku ATM d’ina gidan kud’i su rik’e kud’in na bar musu har abadan duniya. Kai bakinka ba zaiyi mutu ba duk da kana kwance sai yadda a kayi da kai? Eh bazai mutu ba ALLAH ya fiku, mutuwata da rayuwata ba ta hannun ko wani kafiri,a hannun ALLAH take tunda gashi nan har yanzu da raina, ai ba a san ranku muke numfashi ba,kuma na rantse da girman ALLAH sai na d’auki fansa,sai na rama abinda kukama Babana da k’anina!

ALLAH dai yabani lafiya zan tafi Maiduguri,na rantse da girman ALLAH duk wanda ya kwanta toh da safe sai dai ku d’auki gawarshi ku rubuta ku ajiye alk’awari ne wannan,idan ko mutum bai mutuba to ya daina baccin dare sai dai in zai dauwama a kwanan zaune dingirgir.Kai! Suka daka mishi tsawa”kamana shiru komu k’arasaka.Idan kun fasa k’arasani kuba jikokin Baranzan da Zamburan bane,dan kun kashe ni ai a kwai sauran matasa irina da zasu maye gurbina insha-ALLAH. Basu sake magana ba suka tafi.Suna fita yafara kuka yana numfarfashi,yana cigaba da zagin su…Wucewar wasu dak’ik’u sai ga wasu matasa guda biyu sun zo sun d’auke shi.

Julaibib yabi bayansu da kallo yana zancen zuci”kowace irin azaba zasu sake gana mishi oho!Zuciyarshi tak’ara rauni hawaye yafara zubo mishi,ba zato yaji ansa hannu ana share mishi hawayen”kayi hauk’uri ni zan taimakeku,dan banji dad’in abinda aka muku ba sai dai”I have no power da zan hana.Yakalleta da idanshi me lafiyar”ma’aikaciyar jinyace tana sanye da riga da buje farare kanta da k’arin gashi tozon rak’umi guda,yakauda kai… Tabbasss shima da yana da k’arfin da zai iya magana to da shima ya d’ud’d’ura mata zagi bayan ya mata dukan mutuwa wallahi.

Tabisu da kallo cikin tausayi”casualties ne rututu all of them ramshackle.Tayi tsaiii…cikin tunani ta yaya zata taimakesu?Sai kuma ta jijjiga kai tana murmushi yes,tayi d’as da yan yatsunta “fad’uwace tazo dai-dai da zama,sai tajuya da sauri tafita.

Julaibib yasake mirgina kai bangaren dama cikin matsanancin ciwo,ga yunwa ta ci ta cinye k’irjinshi ya mishi nauyi,yana tunanin ma ya gamu da gyanbon ciki,numfashinshi yafara fita sama-sama kamar zai d’auke,a cikin zuciyarshi yake fad’in “Qadarullaahi wama sha’a fa’al…a hankali yafara jin wani abu na sukarshi kamar allura a ilahiran jikinshi me zafin gaske wucewar wasu yan dak’ik’u sai numfashin shi ya d’auke yayi doguwar suma.

Bobby!…takira sunan shi a rikice ganin wata shar6e6iyar wuk’a gayama jini na wuce daya fito yana karkad’ata sai walainiya take yi a hasken rana, yana wak’ar shi cikin nishad’i da karsashi:

Into my heart…come into my heart love Jesus…

Come in…to stay…come into my heart love Jesus…

Tajijjiga kai tana amsa mishi da”amennn.Yayi yar dariya”amennnn,fa kikace are you kidding me? Tagirgiza kai”Absolutely no…duk da zuciyarta lugude take yi karfa ya da6a mata wuk’ar a ciki”eh haka nace amennn,mu musulmai ai mun yadda da Annabi Isah Alaihissalam a matsayin d’an aike daga ALLAH,kune dai baku yadda da Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wa’ahlihi wasallam ba.Tajuya harshe zuwa yaren Bajju.

“Ashyyeaggo(Ina kwana

Yace oh basakut(yi hak’uri) ashe bamu gaisaba

“Ashyllafiya(kin tashi lafiya) yafad’i hakan a gaggauce ya nufi k’ofar gidan zai fita.

Bobby ani yake?(ina zaka)ya tsaya cak sannan yajuyo suna kallan kallo na wucewar wasu dak’ik’u,idanunshi sun kad’a jawur da 6acin rai,takauda kai,yasauke numfashi amma baice kome ba,ita kuma tacigaba da maimaita”ALLAHU-ALLAHU rabbi laa’ushrika bihi shai’a.

Kira yashigo wayarshi yad’aga”kuyi gaba zan biyoku yanzun nan.

Jikinta yak’ara yin sanyi dan ta tabbatar cikin gari zasu sake komawa dan an kawo mishi rahoto d’azu;hausawan daba a k’ona gidajen suba suna ta zuwa suna kwashe kayayyakinsu. Kwallah suka cika idanunta,ta had’a tafukan hannayenta alamar magiya

“Bobby I beg you In the name of Almighty ALLAH karka sake komawa cikin gari.Yaja dogon tsaki yana harararta”ba abinda zai hanani komawa.Yasa hannu zai cire sak’atan k’ofar gidan tasha gabanshi,muryarta tana rawa”haba Bobby wannan wani irin rashin tausayi ne?Me mutanan nan suka muku ne?Haba Bobby kuma fa kuna da yan’uwa a garuruwan da musulmai sune majority while ku kuma minority,yanzu idan sukace suma sai sun rama abinda ku kama yan uwansu na nan yaya za kaji a cikin zuciyarka?

Tacigaba da fad’a mishi kalaman da suka sa jikinshi yayi sanyi,haba Bobby nima bazan so ace an kashe ka batare da kayi laifin kome ba,addinina daban da addininka amma duk da haka you’re my cousin,kuma ina son ka,wannan soyayyarce ma tasa nake zuwa in da kuke,hawaye suka zubo mata sharrr…sharrr…Bobby ka mantane

“Kyan a ayyia ni anaatsi kpa shya?(Duk abinda ka shuka to a k’arshe shi zaka gir6e)

” Da anyi wyi yet kasham(me munine ko kyau)

Tafara kuka kasani sarai Bobby biblically ba ace kuma wani addini haka, toh abinda kukeyi kana ganin

Kaza baa chat?(ALLAH yana so)

A hankali ya girgiza kai.Tace to na rok’eka dan girman ALLAH kayi hak’uri kazauna a gida.Ya amsa kai tsaye sai dai idan tare zamu zauna muyita chatting for all day long.Eh na yadda.Yasake kallanta bayan haka za kimin pepper chicken,za kimin pepper soup,da irin wannan hamburger da kuka zi mana dashi da fruit salad yanunata da yatsa”concur?Tajijjiga kai”hundred percent”muje katayani ai wannan abu me sauk’ine k’wace goruba a hannun kuturu.

Alhaji Salim yasaki labulan ganin sun tafi d’akin-girki,yasauke gwauran numfashi cikin dukan zuciya,al’amarin ya ritsa da sune bayan ya kawo Ummi kamar yadda yasaba idan sunyi hutu a makatanta,ko kuma ranakun k’arshen makon da ya samu damar yin hakan,amma baya tafiya yabarta,tare suke yin kwanaki biyu ko uku sannan su koma,jikinshi yayi sanyi sosai, anya zai kuma zuwa Zonkwa bare har yashigo k’auyen Madauci?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button