
Yagirgiza kai”shi dai yazo wannan yanki na k’arshe har abadan duniya,amma idan Ummi tayi aure ta ga za ta cigaba da zumunci da dangin mahaifiyarta toh shi dai bazai hana taba,tunda matar Mazon ALLAH Sallallahu alaihi wa’ahlihi wasallam Safiyya tana zumunci da yan’uwanta na jinsi Yahudawa,wannan bai zama haramun ba.
Yana wannan zancen zucin Rahab tashigo”Baban Ummi.Yad’ago yakalleta ba tare daya amsa ba.Tayi k’asa da murya”Mama ta fitane? Yayad’a kai.Sai ta zauna sannan ta fad’a mishi abinda yake faruwa a asibitin da take aiki”na san zaka taimakesu, mu an hana mu musu kome da tun ranar da aka kawo su dana fara basu taimakon gaggawa.
Jikinshi ya dad’a yin sanyi”nagode Rahab da kika fad’a min wannan maganar Insha-ALLAH zan taimakesu.To kazo muje ka gansu dan kasan ya azayi kafin goben.Yagirgiza kai”bazan fita in bar Ummi da Bobby kad’ai a cikin gidan nan ba.Tayi yar dariya”kana tsoro kar ya soke ya 6arke maka ‘ya da wuk’a ne?Tad’an motsa kafad’a”na san ba abinda zai mata amma dan hankalin ka yakwanta barin kira Kuno da Yachat su tayasu zama kafin mu dawo ko? Yagyad’a kai”yauwa yanzu naji dama-dama wai kibiya a cikin idanu.Takama ha6a kuma dai? To anyi ba ayi ba kenan.
Bayan sun idar da sallar magriba Ummi take tambayarshi”Abbana d’azu naga kun fita da Aunt Rahab ina kuka jene?Yakalleta da kulawa “ceton ran wasu bayin ALLAH yan’uwan mu musulmai naje,gobe dasu zamu wuce Kaduna.Bobby yad’aga labulan d’akin “ke Ummi baza kizo muyi hirar bankwana bane ko me?
Tad’anyi murmushi”zuwa kai amma kabari muyi sallar Isha’i.Yasaki labulan yak’arasa shiga cikin d’akin yamik’a mata wata babbar waya samfurin Samsung”to ga wannan idan kun gama you shoud let me know zani Fadiyan Guga ne.Takar6i wayar ranta ba dad’i, a daren litini yashigo da manyan wayoyi sunfi hamsin,da su na’ura me kwakwalwa wai duk tsintar yayi a cikin gari da tarin kud’ad’e a cikin buhu”lallai wata shari’ar sai dai a lahira wallahi!.
Washe gari da sassafe sukayi sallama da kowa suka d’auki hanyar garin gwamma,ko a hanya basu samu wata matsala da jami’an tsaro ba dan kowa ya san abinda yafaru a Zonkwa, idan musulmai ne su jajanta tarebda addu’ar”ALLAH yasa kaffarace,idan kuma arna ne suji dad’in ganin mutanan da suke kwance cikin mawuyacin hali,da da dama da sun k’arasa su da bindiga,wanima gallama Alhajin Salim harara yayi”to wad’annan dai ai kuna 6atama kanku lokaci me wajen kaisu asibiti”repetitive strain injury ne dasu fa ko baku gani bane?Mun gani sai yaya?Alhaji Salim ya tambayeshi.Yamotsa kafad’a yana ta6e baki”they are in coma I don’t think they will survive. Alhaji Salim yaja motar ba yare da yace kome ba.
Motarsu tana tsayawa a harabar gidan sauran yaran suka fito da gudu” oyoyo Abbanmu… Oyoyo Yaya Umminmu,suka ringume juna cikin farin ciki.Hajiya Bara’atu farar mace,jaruma me k’ok’arin adalci da gaskiya a duk al’amuranta tak’arasa saukowa daga matattakalar benen,fuskarya d’auke da murmushi, Ummi tasaki k’annanta ta rungumeta “Mamanmu nayi kewarki,kullum sai na yi mafarkinki. Tarik’e hannunta suka zauna”nima haka,toh ya fargaba?Ummi takad’a kai”Mamanmu al’amarin ba kyan gani sai ma kinga wad’anda muka kai asibiti mutum a raye amma ya fara ru6ewa tsutsotsi suna fitowa a jikinshi!Takama goshinta da hannun dama kwallah sun ciko idanunta “kai! Mamanmu arna basu da imani kona sisin kwabo kuma…sallamar Alhaji Salim daya tsaya gaisawa da mak’otanshi da katseta daga abinda zata fad’a.
“Sannu da zuwa Alhaji.Ya zauna”yauwa sannu da gida ya akaji da yara?Tayi murmushi kawai wanna ta tambayi ya masu jikin?Toh godiyar Ubangiji a kowani hali da yanayi,yakad’a kai amma abin kam ba gyan gani.
Hajiya Bara’atu tama mijin na ta wani kallo dasu biyun suka san ma’anarshi duk da yana cikin damuwa sai da yayi dariya,sauran k’annin Ummi suka shiga tayashi darawa duk da basu san abinda yasashi dariya ba,Ummi ce kawai taga abinda yafaru tace musu “to kiyi shiru Ku fa a wasu lokutan baku da wayau,dan kawai kunga ana dariya sai kuma ku fara?Yaran suka kalleshi”kaima Abbanmu ALLAH sai kayi shiru.Toh nayi shiru ya daina dariyar,sai suma sukayi shiru.
Ummi tamik’e”Mamanmu barinje in watsa ruwa,kuma kuzo muje daga nan kowa yabani labarin abin dad’in da Mamanmu tabashi da bama nan.Suka mik’e Yehhh…wallahi munji dad’i,munje kasuwar baje koli,munje gidan dabbobin daji har munyi selfie da 6auna da giwa da d’awisu kuma hotunan suna wayar Mamanmu tace dama zata nuna muku.Suka bisu da kallo cikin so da k’auna irin ta Iyaye da babu kamarta a wajen kowa sai su d’in har suke shige d’akin Ummi,sai tasama k’ofar mukulli dan kar wani yafito”toh duk ku zauna sai na fito daga wanka zan baku tsarabar dana siyo muku ta d’auko wayarta ta kunna musu wak’ar”Adam wa Hauwa na Ihab Taufiq nan da nan suka fara bin wak’ar.
Mutane goma Alhaji Salim yad’ibo daga Zonkwa tare da d’aukar nauyin kome nasu na magani har zuwa sanda zasu samu sauk’i,sai dai a cikin watanni biyu da zuwan su”44 Nigerian Army Hospital”mutum d’ayane”Julaibib Abdullahi d’ansarai shine ya zama ZAKARAN GWAJIN DAFI.
Sai dai shima a watanni biyun nan sau d’aya rakkin-rak ya farfad’o daga dogon suman da yayi yana kuka da sambatun kiran Bilkisuna,Innarmu, Musaddiq, Zaujatiii… Walida,Sudaida,da sauran sunayen yan’uwa amma wad’annan su yafi kira ko a cikin baccin shi.
Sai kuma yau da yasake farfad’owa sai dai Alhamdulillahi wannan karan cikin hankali yadawo hayyacinshi,a hankali ya bud’e idanunshi yana bin d’akin da kallo,ya gane a gadon asibiti yake kwance, duk in da yasamu karaya an gyara,na hannayen shima sun warke sai dai k’afarce har yanzu da saura, ya maida idanunshi kan Ummi da take zaune nesa dashi tana magana a waya.
Wacece wannan?Ya tambayi kanshi yana kuma k’ok’arin tunano a in da yata6a ganinta sai dai bangaren tunani da adana bayanai na kwakwalwarshi sun bashi tabbacin bai san taba,bai kuma ta6a ganin taba sai yau d’in,abu d’aya da zai iya tunawa shine wata ma’aikaciyar jinya tace zata taimakesu bayan nan kuma k’irjinshi yafara mishi suya sai jin wani abu kamar allura yana tsikarin jikinshi daga nan kuma ya numfashin shi ya d’auke.Idanunshi suka sake kad’awa jawur,yanzu ne yake jin asalin ciwo a jikinshi ko ina yayi tsami.
Kwanakinshi hud’u kenan da dawowa daga hayyacinshi,amma ba wanda yasani saboda yana jin alamar za a shigo zai maida idanunshi ya rufe, yauma jin za a shigo da yamaida idanunshi ya rufe a haka har baccin gaske ya d’auke shi.Sai farkawa yayi yafara jin sheshshek’an kuka ana magana a hankali”kiyi hak’uri Ummi ki bar kukan nan dan banga amfaninshi ba,kar yajawo miki matsala”.
Mamanmu ni tausayi yake bani,duk wanda muka zo dasu sun mutu sai shi kad’ai yarage, sannan yanzu duk azabar da yasha an sake karya k’afar wai bata zauna a saiti ba?Takalleta cikin natsuwa”ba kina wajen akayi hoton k’afar ba? Kuma ai kinji bayajin da likitan yayi dan haka ba kome Ummi, ai gwamma ayi abinda ya dace a lokacin da yadace tunda ko an bar k’afar haka to daga baya dolen-dole dai sai an dawo an gyara”ayi agama ai yafi gobe adawo.
Da wannan yawan kukan da kike yi ai gwamma ki dinga mishi addu’a”ALLAH yatashi kafad’a, yasa kaffarace wannnan wahalhalun rayuwar da yake ciki ko?Tagyad’a kai”to amin Mamanmu. Hajiya Bara’atu tayi murmushi”barinje wajen a’isha mu gama maganar kayan danace takawo min sai in zo mu wuce gida yamma na yi.Julaibib yasake tambayar kanshi”su wad’annan su wanene?Sune dai suka kawo shi asibiti suna cigaba da kula dashi ko shakka babu,kullum addu’arshi a garesu”ALLAH yasaka musu da mafificin sakamakonshi ya sanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanshi.