
“This is my hijab…I will never remove.
Wak’ar Ahmad Bukhatir data sa a matsayin ringtone d’inta tafara tashi,abinda yasa Julaibib yazabura tare da bud’e idanunshi yana kallanta.Itama abin ya bata mamaki,tabbasss da k’afarshi ba a sagale take ba,ba abinda zai hanashi mik’ewa.
Tad’aga wayar da sallama,jikin Julaibib ya dad’a yin sanyi saboda ringtone d’in Sudaida kenan tun saninshi da ita da waya bata ta6a canja waba, haka kuma idan tana cikin nishad’i wak’ar da zaiji tanayi kenan,wanda a wasu lokutan shima ba zato sai yaji yana wak’ar,har rannan yakalleta “Zaujatiii…bakya gajiya da wannan wak’ar,ta masa”eh Yaya d’ansarai ai kalmomin cikin wak’ar ne babu na yarwa,ni duk wak’ok’in Ahmad Bukhatir ina sansu tunda ba harigido, gaskiya da gaskiyace kawai.
Yamaida idanunshi ga kallanta. Tagyad’a kai”na’am Insha-ALLAH,tayi jimmm…tana sauraron abinda ake fad’a daga d’ayan bangaren,wani d’an lallausan murmushi ya su6uce mata gefe da gefenta fuskarta suka lotsa ciki sosai(dimple)sannan tace”fi amanillah…Ilal-liqaa.Tacire wayar a kunnanta tana kallan d’an siririn farin agogon dake d’aure a hannun damarta,tayi rubutu a wayar sannan tasata a jaka.
Tamatsa kusa da gadan da yake kwance tana farin ciki da farkawarshi,cikin muryarta ta natsuwa tace mishi”sannu…ya jikin?Sai kawai idanunta suka kawo ruwa saboda tuno ranar data fara d’ora k’wayar idanunta a kanshi”yana kwance magashiyan wasu sassan jikinshi inda akwai sara da suka naman wajen yayi kore yana fitar da wani ruwa me wari,tsutsotsi yammm…sunata fitowa ta wajen, sai dai yanzu Alhamdulillahi yanata samun sauk’i,ta sauke idanunta akan k’aton d’inkin da aka mishi a kai da kafad’unshi duk sun d’auko warkewa.
Tasake kallan fuskarshi sai taji irin abinda taji a ranar farko ruguzowar wani abu kamar gini a k’ahon zuciyarta,ta kauda kai da sauri,shigowar wasu ma’aikatan jinya guda biyu sanye da kakin soja ya bata tabbacin lokacin bada magani yayi.Tad’an sara musu dan suna aikin su yadda yakamata”aikinku yana kyau”bravo.Sukayi murmushi”Thank you. Tagyad’a kai”you’re well come,tajuya tafita a d’akin tare da rufo musu k’ofar a hankali.
Makonni uku bayan nan Julaibib yayi kyan gani fiye da zato saboda yana samun kulawa ta musamman da kuma cimar abinci me inganci da gina jiki,k’afar da aka dad’a gyarawa itama yana d’anyi tattaki da ita amma da taimokon sandunan da yake dogara jikinshi(crotch)a gajiye yashigo d’akin ya had’a zufa kashirban saboda d’an tafiyar da yayi,ya yar da sandunar yana goge zufan fuskarshi,tunani barkatai sun cika k’wak’walwarshi na abubuwan da suka faru, yanajin d’acin mutuwar kamar yanzu yafaru.
Aka turo k’ofar tare da yin sallama. Yad’ago idanunshi da suka kad’a jawur ya amsa sallamar,bai kuma cewa kome ba har Alhaji Salim ya zauna yanata kallan Julaibib d’in cikin tausayi yana ayyane-ayyane a zuci,yasauke numfashi”Qadarullahi wamasha’a fa’al.
Julaibib sai hak’uri dan ALLAH mahaliccinmu ya fika sanin halin da kake ciki,idan ka dogara gareshi zai samar maka da mafita a ragowar rayuwar da zakayi ga kuma tarin lada na maida al’amura gareshi.Nagode Alhaji, kuma bani da bakin da zan gode muku sai dai Ubangiji yasaka muku da irin sakamakon shi,dama kuma ina son sanin kud’ad’en da ka kashe min a asibiti nan.Alhaji Salim yagirgiza kai”ni duk abinda na maka na yi shine dan girman zatin ALLAH a matsayinka na d’an uwana musulmi me buk’atar taimako,ba wai na yi shine idan ka warke ka biyani ba,ni a wajen ALLAH nake neman ladana.
Yagyad’a na sani Alhaji ban kuma man taba,kuma har abadan duniya bazan ta6a mantawa da wannan karamcin na kaba,to amma ina da kud’ad’e da yawa a asusun ajiyata ta gidan kud’i… Idanunshi suka sake kad’awa jawur bani da kowa… Idan ban baka kud’in ba to me ma zanyi dasune?Wa zan ba?Iyaye da Iyali da sauran yan’uwa ko? Toh duk sun rigamu gidan gaskiya, yakad’a kai cikin alhini da tsananin tausayin kai.
Zuri’ata tatafi abadan,babu me dawowa har a nad’e doron duniya!!!Yad’aga hannayenshi”Ya Ubangijina!Ka jikansu, ka gafarta musu!Kasasu a cikin shahidan bayinka wad’anda zasu tashi ranar alkiyama jinin jikinsu da aka zubar yana k’amshin turaren almiski.Alhaji Salim yana tayashi da amsawa da”amin amin ya rabbi.
Wucewar wasu dak’ik’u d’akin yayi shiru,Alhaji Salim yakatse shirun ta hanyar kallan Julaibib cikin natsuwa sannan yace”ai ko kai kake da abinda za kayi da kud’i.Julaibib yakalleshi kallan k’arin bayani.Alhaji Salim yajijjiga kai”abinda nake nufi ka samu damar da zakayi sadaka me gudana ga Iyaye da Iyalanka da wad’annan kud’ad’e ladan hakan yacigaba da binsu kamar suna rayene suna aikata aikin alherin da kansu ko kuwa?Julaibib yajijjiga kai yana wani lallausan murmushin da yamanta rabon da yayi hakan, labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,sai yamik’a mishi hannu sukayi musafaba “nagode,nagode kwarai da gaske da wannan tunatarwa taka Alhaji”Jazakallahu khaira-khaira jazaa’ih.
Haka rayuwar Professor Julaibib Abdullahi d’ansarai tacigaba da tafiya Alhaji Salim yana kan hanyar zuwa dubashi kullum ta ALLAH, wasu lokutan kuma har da Iyalanshi,basu ta6a k’osawa ba har zuwa lokacin da likita yaga dacewar ya sallame shi dan ya warke sai d’an abinda ba a rasaba,wanda yau da gobe kuma da bata bar kome ba zata k’arasa warkar dashi.
Alhaji Salim yad’aukeshi suka tafi gidanshi, babban gida kwarai da aka k’awatashi da filawoyin hibiscus da Queen of the night.Wannan gidanane ina fata zaka iya zama a cikinshi,kasan abin talaka sai a hankali,suka fito daga motar sannan yaba Julaibib mukullin d’aki guda d’aya daga cikin d’akuna shida da suke harabar gidan,yasa hannu biyu yakar6a yana ta godiya har Alhaji Salim yad’an dafa kafad’arshi”ba kome wannan ai…yiwa kai ne,ka shiga ka huta, yamik’a mishi hannu sukayi musafaha.Alhaji Salim ya wuce cikin gida.
Julaibib yasa mukulli yabud’e d’akin… Wani sanyi da k’amshin turaren d’aki suka daki k’ofofin hancinshi,yad’an lumshe idanunshi,rabon da yaji k’amshi me saukar da natsuwa a ilahirin gangar jiki da sararin zuciya tun Sudaidanshi tana raye, yabud’e idanu yana bin d’akin da kallo kome a kwai baya buk’atar k’arin kome sai tufafin sawa,yakwanta a gadon rigingine yayi matashin kai da hannayenshi tunani barkatai ya cika k’wak’walwarshi a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba dashi.
God’iyar liman ba gudu ba ka ye.
Alamar shiga masallaci cire takalmi.
14 Rajab 1441
8 March 2020
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na ashirin da shida.
A mando sansanin Alhazai(hajji camp)wasu yan gudun hijirar Zonkwa suka yada zango musamman wad’anda basu da takamaiman in da zasu zauna,tabbasss suna samun tallafi to amma kun san k’asar tamu kome kashin dankaline…sune sukayi sama da fad’i da mak’udan kud’ad’en sai d’an abinda ba a rasaba talakwa suka samu,zasu cinye hakkin jama’a su kuma je lahira su biya a in da ba a biyan bashi da tsurar kud’i sai aikin alherin da aka aikata a doron duniya, da tallafin gidauniyar