GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

“d’angote Foundation” ta naira dubu d’ari-d’ari da aka ba mutane dashi suke jalauta rayuwar,Julaibib bai samu ko sisin kwabo ba,kuma hakan bai dame shiba,dan kud’i ba matsalar shi bane,sai dai ma yaba wasu,lokaci zuwa lokaci ya kanje Mando a gaisa da abokan arziki harma yayi ihsani ga wad’anda tasu wahalar tafi ta wasu.

Julaibib ya d’auko wayarshi yana jujjuya ta makonni biyu kenan da siyan wayar tare da yin swap d’in layinshi sai dai har yanzu ya kasa kunnata, sai yayi kamar zai kunna sai kuma ya mayar ya ajiye, yau ma har ya mayar sai ya dad’a d’auko ta yayi jimmm… Sannan ya kunna,tana gama sai tuwa kira ya dinga shigowa ba k’ak’k’autawa”Yad’aga da sallama… Kirane daga malamai abokan koyarwa da d’alibai;ya amsa waya sunfi hamsin kai a k’arshe gajiya yayi yasata a jirgi sannan yasamu damar fara karanta sakwanni na ta’aziyya kala-kala,daga nan ya bud’e wata wak’a da aka turo mishi wai Karmataka Studio Kano suka yi wak’ar ta’aziyya shi irin wak’ok’in nan basu dad’ashi da k’asa ba,yafara sauraro sai yaji har da yan’uwanshi yagama jinta har k’arshe,sannan ya kunna d’aya wak’ar sai yaji tsohuwar wakar da Rabi’u Usman Baba kano yayi tun lokacin yak’in Zangon-Kataf bai gama sauraroba,yakashe ya kunna yak’in Zonkwa

“Zonkwa Genocide”anan yake ganin abinda bai gani ba ganin idanun shi…sun maida makarantar daya kashe miliyoyin kud’i wajen ginata filin ALLAH,haka babban masallacin juma’ar garin da aketa kashe mata miliyoyin kud’i wajen zamanar dashi,sai dai basu rusashi gaba d’aya ba,sun rataye k’aton kan allade a gaban masallacin,tarin kwalaben giya kam ba a magana da alama mashaya suka mayar da wajen.

Yajijjiga kai “Manzon ALLAH sallallahu alaihi wa’ahlihi wasallam yayi gaskiya da yace babu amana tsakanin kafirai da musulmai kona sisin kwabo,duk yadda kuke dasu kuwa,taci na ciki wallahi. Sai ya tuno da wata magana da wani ALLAH Magani yata6a fad’a lokacin da yaga anata gudun hijira da ake fad’a a Kaduna”Wai musulmai suna ta tafiya to dawa za suyi yak’i?Ai sai sun dawo sun saki jiki tukuna zasu k’addamar musu… Ilai kuwa gashinan sun gani ganin idanun su.

Yacire wayar a jirgi yafara gwada wasu lambobi amma ba wacce ta shiga,zai sake kira,wani kiran yashigo,ya zubama lambobin idanu anya ban san me wannan layin ba?Har ya katse ya sake shigowa yana gab da katsewa ya d’aga da sallama aka amsa tare da tambayar”dan ALLAH d’ansarai ne me wannan layin?Ya amsa kai tsaye”eh shine.Tace cikin farin ciki ALLAHU AKBAR d’ansarai Bongel ce.Nan suka gaisa tanata mishi ta’aziyya muryarta tayi rauni”mun gwada lambar ka sau shurin masak’i bata ta6a shiga ba,Baban Humaima yaje Zonkwa amma bai samu kowa na kaba,har Mando ni dashi munje amma ba labarin kome”wayyo duniya!Lallai wata shari’ar sai dai a lahira.

Julaibib yace dan ALLAH ki turo min lambar Doctor dana Innan Matsirga,yasake famo mata wani miki,cikin kuka tace”baka san abinda yafaru a Matsirga ba d’ansarai?Duk sukayi shiru sai yaji ta katse wayar.Yatallafi kanshi da duka hannayen shi yanajin wani irin yanayi mara dad’i yana tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarshi kamar wanda zai yi zazza6i.To me yafaru a Matsirga?Tambayar daya kasa samo amsarta kenan a k’wak’walwarshi, yad’auki wayar da niyyar sake kiranta sai kuma yaga gwamma yaje ya samu Doctor Manogi ya maida wayar aljihu yasa farar hula zita yafita.

A harabar gidan suka yi kaci6is da Alhaji Salim da Ummi.Ummi tad’ago ta kalli Julaibib wallahi sosai take jin tausayinshi,takad’ai kai cikin jimami”ALLAH sarki kowa da irin tashi k’addarar rubutacciya tun daga Lauhul-mahfus.

Alhaji zani Zari’a ne.Yau d’in nan? Yagyad’a kai”Insha-ALLAH yanzun nan.To ALLAH yatsare,bai damu da sanin abimda zaije yi a Zaria ba. Yakalli Ummi shiga d’akin-shak’atawa ki d’auko min mukullin mota yana nan a hannun doguwar kujera, taje tad’auko Alhaji Salim yakar6a sannan ya mik’a ma Julaibib,sai ya girgiza kai Alhaji kabarshi kawai zan tafi tasha.Yasaka mishi mukullin a aljihun gaban farar rigarshi”motar haya ai lalurace Julaibib,kai kanka za ka fi jin dad’in tafiya a wannan.

Suka yi tafiyarsu suka bar Julaibib, yayi tsayuwar a kawu yafurzar da wani huci, can cikin zuciyarshi yana jinjina halin karamci irin na Alhaji Salim,kullum abincin nan sau uku a rana,idan ma anyi wani abu bayan abinci na ta6akalashe to shima haka za a ciko mishi kwano,shi ko da me zai saka musu bayan addu’ar da yake musu kullum,wani irin tagomashi zai musu?Lallai yaba kyauta tukwuici ko??? Yajijjiga kai”toh shima zai musu abinda baza su manta dashi ba har abadan duniya.

Da wannan tunanin yashiga mota yad’aura belt sannan yatasheta bakinshi na ambaton ALLAH,yana tafiya yana tunanin al’amuran rayuwa me hawa da sauka,me cike da sark’ak’iya,me d’acin da ya zarta na mad’aci a wasu lokutan,me zak’in daya zarta na zuma a wasu lokutan”Dawaamulhal minal mahal (no condition is permanent) ba wani yanayi da yake din din din abadan a doron duniya sai buwayi gagara goyo Ubangijinmu me kowa da kome.

Ya isa Teaching Hospital ya ajiye motar a inda ake ajiye motoci sannnan ya nufi office d’in Doctor Manogi amma yatarar a rufe,wani Likita yafad’a mishi yana Emergency yazauna ya jirashi idan ba sauri yake yiba…Yaciro wayarshi yashiga yanar gizo a kafar sadarwa ta Facebook,sai dai yasha mamaki kwarai da gaske da yaga tarin arnan Zonkwa da suka turo mishi da rok’on gayyata dan su zama abokai,wasu yan gaggawa hannun hagu a romo har sun tura mishi da sak’o ta messenger sai dai bai karanta ko guda d’aya ba ya gogesu yana tsaki”suna da wayau amma in da hankali yake to su basuje wajen ba,basu mayi tunaninshi ba.Masu lambarshi suma sunata mishi magana ta Whatsapp amma bai bi takan suba.

Doctor Garga Ibrahim Manogi yacire farin gilas d’in da yarufe idanunshi yana nuna Julaibib “wa nake gani haka?Sai lokacin Julaibib yad’ago kai yaga Doctor Manogi da yayi wasu yan dak’ik’u kawai yana kallanshi,yamik’e tsaye suka rungume juna “ALLAH me iko Ustazu dama kana raye? Suka saki juna yabud’e musu office suka shiga,nan fa hira ta 6arke na abubuwan da suka faru har Doctor Manogi yabashi labarin abinda yafaru a Matsirga nan d’in ma kisan wulak’anci sukama musulmai wad’anda kwanansu yake gaba sun sha dakyar,sun tasa shanunsu gaba d’aya sun tafi dasu k’auyan kansu,su dai abinda yake hannnun musulmai yana tsone musu idanu,yana hanasu rawar gaban hantsi,sai dai na gaba ya dad’e dayin gaba,kuturwar uwa tilas zama dake,su cinye dukiyar su dawo gidan jiya cin busar doya da magwaro a matsayin abinci,irinsu Innan Bilkisu da sauran yan’uwansu Bongel sun musu yankan rago;a cikinsu Bello ne kawai yasha dakyar,mun dad’e muna fama da k’wak’walwarshi kafin ta dai-daita saboda irin halin firgicin daya shiga.

Amma yanzu Alhamdulillahi ya warke garas,na samo mishi gurbin karatu a Jami’ar Madina yana can,amma ko jiya da mukayi waya wallahi sai da ya tambayeni har yanzu ba a ga wani daya dangance kaba ko mutum d’aya?Julaibib yad’anyi murmushi “Bello kenan,yakar6i lambar wayar shi,sai ya koma gida zai kirashi.Doctor Manogi yakalleshi”ka san ALLAH kawai zagewa za muyi kamar yadda musulman Kafanchan sukayi,duk wanda yasan yana cikin irin wad’annan mutanen to shima yazama cikin shirin ko ta kwana da makaman kare kai”tunda ba kwanciya akafi kare ba,sai dai a fishi da abun rufa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button