
Haka suka ma musulman Kamatan haka, haka,hakaaaa sai da suka tashi garuruwa goma sha uku,amma dan rashin mutumci da da rashin hankali wasu tsinannu suke iya bud’e baki suce wai musulmai yan ta’addane,kuma gwamnati tanaji tana gani ba a d’auki wani mataki a kan suba,toh gobe ma idan sukaji sha’awar hakan ai basu da fargabar kome dan sun san idan sun kashe musulmai suna jin kamar sun kashe kiyashi ne,kuma da yake bahaushen mutum shima wani k’aton sakarai ne har yasake yadda ya koma garin Zonkwa wai da sunan cin kasuwa…na rasa ina hankali da tunanin wasu daga cikin mu yake.
Sai da sukayi sallar azahar sannan suka tafi gidan Doctor Manogi,shi da Bongel suka dad’a yima juna ta’aziyya,yaba su Humaima kud’i,ran Doctor Manogi da Bongel bai musu dad’i ba saboda kud’in da yawa.Julaibib yad’anyi murmushi”kusa ranku a inuwa yanzu d’ansarai bashi da zuri’a,toh idan ban ba sauran yan’uwa abokan arzik’i na musulmai ba wa zan ba?ALLAH dai yasa tamu k’arshen tayi kyau, jikinsu yayi sanyi,suka amsa da amin.Sukayi sallama yaja motar yatafi,suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa ta6ace ma ganinsu.
Yana zaune a harabar gidan yana alwala Misbahu k’anin Ummi yakawo mishi k’aramin Identification card(ID Card) d’in shine na”Zonkwa Internally Displaced Person daya manta dashi jiya a motar.Nagode ko?Misbahu yayi murmushi sannan yajuya yana fad’in barin d’auko hulata mutafi masallacin.
Shehin malami(Professor)a Jami’ar Usman d’anfodio Sokoto(UDUS)Maimun abdulqadir ya kawo ma Julaibib ziyara,sun sha hira har sun gaji,tun safe suke tare har bayan sallar la’asar,lokacin ne yake haramar tafiya.Cheque ya rubutama Julaibib na miliyan biyar.Julaibib yagirgiza kai”Professor kar muyi haka dakai mana wannan kud’in to ai ka kwashe kud’in asusun ajiyar takene.
Yagalla mishi harara”idan ma zagina kakeyi a kaikace toh nagode,kuma ka kirani da Maimun kawai.Bazan iya ba Professor;matsayi ai ALLAH yake bayarwa kuma ya baka dan haka dole in baka,bazan k’i kiranka farfesaba.Maimun yace “uhum… Wa yaga farfesa ciki fal geron sunday.Sukayi dariya dan sun tuno lokacin.Julaibib yace ai dane,yanzu cikin farfesa cike yake da dajjaja da labanun.Ya ajiye mishi cheque d’in”ba fa zan kar6a ba,na ma gode kwarai da kayi takakkiya kazo in da nake,dan me san kane zai damu da kai har kuma yazo takanas inda kake dan yaganka kuyi zumunci duk da tazarar dake tsakanin mu.
Maimun yakalleshi cikin natsuwa “d’ansarai kar muyi haka dakai mana,wallahi da ina da lambar asusun ajiyarka da sai dai kaji alert. Julaibib kai ai abokin aminci da amana ne,har abadan duniya bazan ta6a mantawa da karamcinku kai da marigayi Musaddiq ba,duk in da zan ba da tarihin rayuwata to tabbasss sai kun fito a ciki.A lokacin da muke karatu a Gidan-Waya na baka wannan labarin yanzu ma zan sake ba ka”tun ina ciki mahaifina yakwanta dama,a haka mahaifiyata ta haifeni tacigaba da kula dani da sauran Yayyina su hud’u duk dani mu biyar,bata samu wani tallafi daga dangin mahaifinmu ko na ta dangin ba,kasancewar suma babu ta musu katutu,duk da haka munfi wasu daga cikinsu duk da mahaifinmu shima ba shi dashi,to amma ALLAH yatarfama garinmu nono gidan da muke ciki na shine ba haya muke yiba,wasu da yawa daga cikinsu kuma haya sukeyi,wasu kuma suna zaune a gidan da aka musu alfarma su zauna har zuwa lokacin da ALLAH ya yassare musu sukayi na su.
Mahaifiyar mu tunda jajayen sawunta take sana’o’i mabambanta ta ajiye maganar aure a gefe ta kuma toshe kunnuwanta ga duk abinda zaije ya dawo na zamanta a haka ga k’uruciya ga rashin aure ba irin sharrin da ba a mataba,ita dai kawai burinta ta inganta rayuwarmu,a haka da taimakon ALLAH dana yan’uwa d’an abinda ba a rasaba ta gangand’a ta aurar da Yayyina matan,muka cigaba da gara rayuwar a yadda tazo ba a yadda muka so tazo mana ba,rannan dai ganin wahalar tayi yawa nace mata ni kawai zan fara bin mota in zama kwandasta idan na iya in samu mota in zama direba.Idanunta suka kawo ruwa tana kallona cikin jarumtacciyar zuciyarta me k’arama mutum juriya da hangen wata rana sai labari.
Maimun ni da mahaifinka ba irin rayuwar da muke so kayi ba kenan,kullum burinmu ace Ya’yanmu sunyi zarra wajen ilmin addini,dan haka kayi d’amara kabani goyon baya dan girman ALLAH karka watsa min k’asa a cikin idanuna,tanuna kanta da yatsanta”madamar ina numfashi a doron duniya to Insha-ALLAH sai ka zama abin kwatance sai anyi alfahari an mori tarin ilminka…
Idanun Maimun suka kad’a yanajin kamar a lokacin ta zaunar dashi tana fad’ama mishi kalaman.Julaibib mun sha wahalar rayuwa,har k’anzon abincin gidajan mak’ota take kankaro mana muzo muci.Kullum kalamanta na k’arfafa gwiwane “Maimun kayi hak’uri wata rana sai labari ba wani yanayi da yake din din din a doron duniya,a haka dakyar da sid’in goshi muka gangand’a na gama secondary,sai da nayi k’wadagon shekara uku sannan na had’a kud’in registration nafara karatu a Gidan-Waya.
Wasu lokutan inji kamar in gudu dan bak’ar wuya amma idan natuno da kalaman mahaifiyata sai inji k’warin gwiwa dan na san tanacan tanata k’ok’arin tara min wasu kud’ad’e kafin buk’atarsu ta taso,har zuwa lokacin da kuka shigo makarantar,tamu tazo d’aya kuka fahimci halin da nake ciki kuka taimakeni tun kafin in furta hakan,kuka yadda na dawo d’akinku gaba d’aya da zama inci abincinku,in sa kayan sawanku…da sauransu da sauransu,kun d’auke min abubuwa masu yawa game da karatuna, kuma kuna bani girma a matsayina na d’an Adam bakuyi duba da cewa k’asa nake da kuba.
Mun gama karatu lafiya har na samu koyarwa,d’ansarai kazo ka d’aukeni muka tafi Jami’ar Ahmadu Bello wai ka samo min gurbin karatu…Yakalli Julaibib ban ta6a ganin mutum me irin zuciyar kaba,kai ka biyamin kud’in registration.Da taimakon ALLAH dana mahaifiyata da kai nakai matsayin da nake,toh ta yaya zan manta wannan d’imbun alheran Malam d’ansarai?
Ya share hawayen da yazubo mishi sai dai shi ALLAH baya barin wani dan wani…ina matakin Senior lecturer mahaifiyata itama takwanta dama an gama cin mad’aci za a fara cin zak’in….ALLAH ya jik’anki mahaifiyata da sauran Iyayenmu kaafatan.
Yakalli Julaibib”to dan na baka d’an wannan kud’in da bai wuce kacika matorka da mai ba (full tank)kawanice bazaka kar6a ba?Julaibib yayi yar dariya”d’ansarai ko tayar keke bai dashi bare mota. Babu damuwa motar ma tananan tafe Insha-ALLAH,ka kuma fara shiri dan Umrah na bana da kai zamu tafi muyi azumin ramadana a can.Julaibib yayi godiya sosai sannan yarakoshi wajen mota,anan ma sun 6ata wasu dak’ik’u kafin sukayi musafaha yashiga motar ya zauna direban yaja motar,shi da Maimun suka d’aga hannu suna ma juna adabo.
Miliyoyin kud’ad’e Julaibib ya samu daga abokan arziki da gwammati,dan haka yasai fili babba yasake gina makarantar da tafi ta garin Zonkwa kome da kome gefen makarantar ya gina d’an madaidaicin gida.Ya ajiye aikin koyarwa na duk makarantun da yake zuwa, yadawo makarantarshi daya gina,suna cigaba da koyarwa da wasu malaman daya d’auka.
Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa bayan sun dawo daga masallaci sallar Isha’i”Julaibib na so kwarai da da matarka ta aure ka tare a gidan ka. Yad’an bud’e idanu dan mamaki”Alhaji aure kuma?Sai yagirgiza kai”zanyi zamana a haka har zuwa lokacin da nima zan daina numfashi a doron duniya.Alhaji Salim yakad’a kai dan shima ya d’an d’and’ana irin abinda Julaibib yake d’and’ana amma ba kamar na Julaibib ba.