Labarai

Halaye masu kyau da na koya a wajen Musulmai -Wata budurwa Kirista





Wata budurwa mabiyar addinin kirista ta bayyana wasu muhimman dabi’u da ta koya daga wajen Musulmai.

A cikin wani bidiyo da budurwar mai suna Gayobi Achawa ta saka a shafin TikTok, ta bayyana cewa ita ba Musulma bace amma tana da ‘yan’uwa Musulmai a cikin danginta.

Halayen da ta koya daga wajen musulmai

Budurwar ta bayyana cewa wadannan halayen na Musulmai da ta koya wadanda suke matukar birgeta, ta koye su ne a wajen ‘yan’uwanta da kuma wajen yin aiki tare da Musulmai.

Ga jerin su kamar haka:

1. Mata Musulmai sun nuna mana cewa ba sai mace tayi shigar banza ba kafin kyawunta ya bayyana. Mata Musulmai za su rufe jikin su amma za ka ga kyawun su yayi matukar bayyana.

2. Biyayya, Musulmai nada matukar biyayya kan addinin su. Ba musulmin da zai bari a taba darajar Al-Qur’ani, manzon Allah (SAW) da Allah (SWT). Idan abota ta hadaku, to lallai komai rintsi komai wuya za su kasance tare da kai.

3. Musulmai ba munafukai bane, Musulmai ba ruwan su da munafurci idan suka ce za suyi abu to lallai gaskiyar kenan za suyi shi.




Related Articles

Leave a Reply

Back to top button