Uncategorized

HALIN GIRMA 1-5

“Yaki takwara ta, zo nan.” Gajin tace tana daga zaune
a in da take

 

“Me yake damun ki?”

 

“Na’am?”

 

“Fad’a min idan kina da wata matsala ne, na dade ina lura
da yanayin rashin walwalar ki, sai dai na kan dauki hakan a matsayin halitta,
amma kuma jiya sai abun yazo kaina, na dinga tunanin ko dai kina da wata damuwa
ne? Da kika kasa sanar wa wani kika barta a ranki.”

 

“Babu komai Gaji, yanayi na ne a haka amma ni babu abinda
yake damuna.”

 

“Kin tabbata.”

 

Daga mata kai tayi tana jin kamar ta saki kuka, ga dama ta samu
amma bata da ikon furta wa, toh tace mene ma wai? Hakan ba shi zai hana Mama ta
daina muzguna mata ba, Kai tsaye zata kare kanta da zarar Gajin ta tuhume ta
karshe kuma abun ya koma kanta kowa ya cigaba da mata kallon marar kirki ko
kuma wadda bata san halacci ba. Shiyasa ta zabi yin shiru kawai dan fadar ba
zata sauya komai ba, su duka sun yarda da Maman yarda irin ta ban mamaki.

 

“Ai nasan bangaren Hajara baki da wata matsala dama, na dai
zata ko damuwa ce dai irin ta rashin maman ki kusa dake, duk da bani da haufi
akan kulawar da kika samu iyakar abinda zaki samu kenan ko da ita mahaifiyar
taki ce.”

 

“Haka ne.” Tace a kasalance

 

“Yawwa ki dinga dan daurewa kina shiga cikin yan uwanki
kinji? Zaman shirun da kike babu dadi.”

 

“In sha Allah zan gyara.”

 

“Yawwa… Haka nake son ji.”

 

“Ya batun yajin aikin nan kuwa? Kun dauko karatu tiryan
tiryan yajin aiki ya tsaidaku da tuni wata maganar ake ba wannan ba.”

 

“Wallahi shiru ba labari, muna dai ta addu’a Allah ya sa a
daidaita.”

 

“K’asar nan kenan ai, dan karatun ma yanzu nema ake a hana
dan talaka yin sa.”

 

“Wallahi.”

 

” Allah yayi mana maganin abinda yafi karfin mu.”

 

” Amin ya Allah!”

 

” Shiyasa nace duk ku fidda mazaje kawai da zarar wadanchan
sun tafi kuma azo ayi naku zaman haka nan ba zai yiwu ba.”

 

Shiru tayi gabanta ya fadi, bata son taji ana maganar auren su,
gashi kuma taga alamar ba za’a dauki lokaci ba za’a ce su fidda mazaje, ya
zatayi da ranta? Da ganin suna makaranta yasa maganar ta lafa amma yanzu yajin
aikin da aka tafi da ba’a san ranar dawowa ba ya saka iyayen nasu yanke
shawarar suma su aurar dasu kawai sai karasa karatun a dakin su.

   Tashi tayi tayi ma Gajin sallama ganin lokaci
yayi, taje tayi alwala ta saka Hijab dinta ta fito, a falo ta tarar da Mama
tayi saurin tsugunnawa ta gaishe ta

 

” Mama barka da gida.”

 

” Saura idan an tashi ki tsaya shiririta a hanya ko ki
tsaya gidan Gaji karki zo kiyi abinda ya dace, jiya kam kinci darajar babanku
yana nan.”

 

“In sha Allah.” Tace sannan ta mike ta fice Maman ta
rakata da harara.

 

****Sati biyu tsakani aka fara bikin gidan nasu, duk yadda taso
gujewa wasu abubuwan amma Maryam bata barta ba, komai idan za’a yi sai ta
sakata a ciki, haka kunshi da gyaran kai tare suka je da wata kawar Maryam din.

  Alhamis suka fara bikin, a compound din gidan Anty
Mabruka sukayi bridal shower iya su da kawayen su, juma’ah akayi kamu asabar
aka daura aure hade da yini, lahadi aka kai kowacce gidan ta.

   Ranar litinin suka tashi gidan da sauran bakin da
basu riga sun tafi ba wanda yawanci dangin Gaji ne, a babban kitchen din gidan
suka hadu aka hada breakfast Masa da miyar taushe, har rana tayi sosai basu
kammala ba hakan ya sake haifar mata da wata irin gajiya bayan wadda take fama
da ita, tasan halin Mama sarai idan ta makale taki fitowa ayi aikin da ita duk
da akwai masu yi din amma dolen ta ne ta fito, duk da hakan ba karamin taimaka
mata yayi ba wajen gogewa da kalolin girke-girke mabanbanta. Sannan uwa uba
girkin mutane da yawa wanda ba kowa bane ya iya.

   Da saurin ta, ta karasa dakin su, ta kwanta a
gefen gadon saboda wani irin sanyi da take ji alamun zazzabi ne ke neman rafke
ta, rawar sanyi ta fara hakoranta suka shiga haduwa waje daya, ta saka hannu da
k’yar ta jawo bargon Zeenat din ta lulluba.

   Shigowar ta kenan ta tsaya daga kofar

 

“Kut! Lallai ma.” Tace tana karasawa ciki, ta fuzge
bargon da karfi

 

“Dan Allah zee ki kyale ni bani da lafiya.” Tace
muryar ta chan ciki. Shiru Zeenat din tayi tana kallon ta, sai kuma ta sakar
mata bargon ta juya ta fice daga dakin. Har dare zazzabin be sake ta ba, babu
kuma wanda yazo neman ta. Tayi tunanin Zeenat din zata fad’a wa Maman ne duk da
bata saka rai ba, amma jin shirun ya tabbatar mata da ta fad’a mata dan da ba
haka ba da tuni Maman ta turo neman ta akan wani aikin.

   Wajajen Tara Zeenat ta dawo dakin, ta kalle ta a
zaune saman abun sallah ta kudundune, juyawa tayi ta fita ta dawo da paracetamol
a hannun ta da ruwa ta mika mata. Karba tayi da sauri tayi mata godiya, bata
amsa ba ta sake fita sai gata ta dawo da katifar Iman din, ta shinfid’a mata
sannan ta dauko bargon ta, ta dora mata akai ta haye gadon ta kwanta ta rufe
idon ta. Sosai Iman taji dadi a ranta, ko ba komai tayi mata abinda bata taba
ba, tashi tayi da k’yar ta lallaba ta fita kitchen ta hado tea sannan ta dawo
ta sha da k’yar ta sake komawa ta kwanta ta kudundune.

   Kwanan ta uku a haka, har ta soma samun karfin
jikinta, Mama ta shigo sau daya ta bata anti-malaria shima dan tasan Abban zai
iya tambaya ne, shima da tasan zai shigo ya duba ta ne, tana jin sanda take ce
masa sun je asibiti ma kuma jikin da sauki.

  

***Karamin daki ne da yafi kama da shago, katifa ce karama irin
ta yan boarding school sai jakar kayan sa a gefe, bayan haka babu komai a dakin
sai wani dogon mudubi dake rataye jikin bangon dakin.

   Tsaye yake a gaban mudubin yana duba fuskar sa
dake cike da kasumba ko ina har baka iya ganin komai na fuskar tasa sosai,
kansa rufe yake da katuwar hular sanyi, ya nannade wuyan sa da abu, kafar sa da
hannun sa duk rufe suke cikin hular sanyi, idan ka cire fuskar sa da itama
kasumbar bata wani bari a ganta sosai, babu wani abu na jikin sa dake a bud’e.
Kayan jikin sa a wanke suke tsaf, sai dai sun tsufa sosai, har da wata yar bula
a jikin hannun rigar.

   A ko da yaushe yakan tsaya ne a daidai hanyar da
take hucewa idan ta dawo daga islamiyya, amma kuma kwana biyu ya rabu da ganin
ta, shiyasa ya yanke shawarar zuwa gida duk da yasan ba tsarar sa bace amma zai
gwada sa’ar sa.

  

 

 

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

 

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da
wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

 

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu
dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma
kasan cewa tafiyar ta dabance_*

 

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN
NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

 

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

 

*_DEEN MARSHALL👉🏾
Mamuhghee_*

 

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat
rano_*

 

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn
abdul_*

 

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss
xoxo_*

 

*_ÆŠABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

 

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU
AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

 

2👉🏾400

3👉🏾500

4👉🏾700

5👉🏾1000

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button